NDLEA ta ƙwace miyagun ƙwayoyi da darajarsu ta kai naira biliyan 5 a Rivers

Asalin hoton, NDLEA/x
Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Najeirya (NDLEA) ta ce ta ƙwace miyagun ƙwayoyi da darajarsu ta kai kusan Naira biliyan 5 a tashar jiragen ruwan Onne da ke jihar Rivers.
Kwamandan NDLEA a tashar, Omerio Odo, ne ya bayyana hakan yayin bikin ranar yaƙi da ta’ammali da miyagun ƙwayoyi ta duniya a 2026.
Ya ce kayayyakin da aka kama sun haɗa da kwantena guda bakwai ɗauke da sama da kwayoyi miliyan 3.5 na opioids da kuma kwalabe miliyan 1.2 na codeine, tare da kayan da nauyinsu suka kai ton 206.
Ya ƙara da cewa an samu wannan nasara ne ta hanyar tattara bayanan sirri, ƙara tsauraran matakan sa ido da kuma haɗin gwiwa da sauran hukumomin tsaro da masu ruwa da tsaki a harkokin jiragen ruwa.
Odo ya bayyana cewa kayayyakin da aka kama kaya ne da za su shafi rayuwar mutane da iyalai da kuma al’umma baki ɗaya. Ya kuma yi gargaɗin cewa duk da muhimmancin tashar Onne wajen kasuwanci, masu safarar miyagun ƙwayoyi na ƙoƙarin amfani da hanyoyin ruwa wajen shigo da haramtattun kaya cikin ƙasar.
Kwamandan ya tabbatar da cewa NDLEA za ta ci gaba da ƙara ƙaimin matakai ba ƙaƙƙautawa wajen daƙile fataucin miyagun ƙwayoyi, tare da jaddada buƙatar haɗin kai daga gwamnati, al’umma da hukumomi.
Ya kuma bukaci masu harkokin dakon kaya da su riƙa bincika kayayyaki sosai tare da bayar da rahoton duk wani abu da ake zargi.













