Rabi'atu Sufyan: Tarihin fitacciyar Malamar addinin Musulunci da ta rasu

Rabi'atu Sufyan

Asalin hoton, OTHER

Bayanan hoto, Rabi'atu Sufyan ta yi fice wajen gudanar da wa'azi musamman ga mata a lungu da sakon Jihar ta Kaduna, da ma wasu sassan Najeriya
An wallafa

Jama'a masu dimbin yawa a Najeriya sun yi ta alhinin rasuwar fitacciyar malamar addinin Musuluncin nan Malama Rabi'atu Sufyan wadda Allah ya yi wa rasuwa ranar Asabar.

Bayanai sun nuna cewa Malamar ta rasu ne ita da wasu abokan aikinta na da'awa sakamakon hatsarin mota a yankin Samunaka na Jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya, yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa Musabakar Karatun Al-kur'ani mai girma a Jihar Adamawa da ke arewa maso Gabashin kasar.

Malamar ta yi fice wajen gudanar da wa'azi musamman ga mata a lungu da sakon Jihar ta Kaduna, da ma wasu sassan Najeriya.

Tuni dai aka yi jana'izarta a Kaduna.

A sakonsa na ta'aziyya da ya wallafa a shafin Facebook, Abu Aysha, ya bayyana marigayiyar a matsayin "uwar marayu, mai kamar maza wajen da'awa da taimaka wa al'umma."

Malama Rabi'atu da wasu mutane

Asalin hoton, Facebook/Abu Aysha

Shi ma Jamilu Idris ya ce "na santa tun muna aikin agaji a JNI (Jama'atu Nasril Islam) tun shekarar 1990 har zuwa rasuwarta" sannan ya yi addu'ar Allah ya jikansu baki daya.

Jamilu Idris

Asalin hoton, Facebokk/Jamilu Idris

Wace ce Malama Rabi'atu Sufyan?

Wani ɗan jarida mai suna Adamu Garba da ya yi aiki sosai da malama kan harkokin da'awa ya shaida wa BBC cewa an haifi Malama Rabi'atu Sufyan kimanin shkeara 62 da suka gabata, kuma su uku ne a wajen mahaifiyarsu.

Tana da yaya Alhaji Yusuf wanda shi ma ya rasu, sai kuma ƙaninta Malam Sulaiman.

Ta rasu ta bar mahaifiyarta da ƙanin nata Malam Sulaiman.

Malama Rabi'atu Sufyan ƴar asalin ƙaramar hukumar Kura ce ta jihar Kano, kuma ta fara karatunta ne daga makarantar allo a can, daga bisani ta koma wajen kawunta a Lagos, "amma ba ta daɗe sosai ba sai ta koma Kaduna."

IMWON

Asalin hoton, IMWON

Bayan ta koma Kaduna ne sai ta koma ƙarin karatu inda ta shiga wata makarantar Islamiyya a Kawo New Extension.

Daga can ta wuce Salmatu Institute da ke Unguwar Mu'azu a Kaduna don zurfafa ilimi.

Daga baya kuma ta koyar a makarantar Salmatu Institute ɗin da wata makaranta a Riga-Chikun da ma wasu makarantun da dama.

Bayan wasu shekarau ta koma Jami'ar Ahmadu Bello Zaria inda ta yi digiri a fannin Larabci.

Kafin rasuwarta Malama Rabi'atu ma'aikaciya ce a gwamnatin jihar Kaduna a matsayin mai kula da makarantun firamare.

An fara sanin Malama Rabi'atu ne a lokacin da ta zama mamba ta ƙungiyar Da'awa ta mata ta Fomwan. Sannan ta zama mataimakiyar shugabar ƙungiyar Women In Da'awah.

Daga baya ta ƙiriƙiri tata ƙungiyar mai suna Initiative for Muslim Women in Nigeria IMWAN, kuma ita ce shugabar ƙungiyar ta ƙasa.

Malama ta yi aiki a matsayin jami'ar bayar da agajin gaggawa ta Jama'atu, ta yi mamba ta ƙungiyar MSS, sannan Sarkin Musulmi ya naɗa ta shugabar Gidauniyar Nana Asma'u ta ƙasa.

"Wani abin sha'awa shi ne malama ta rayu a kan neman ilimi da bayar da shi, kuma a kan wannan hanya Allah Ya karbi rayuwarta," in ji Adamu Garba.

A lokacin gwamnatin Shugaban kasa Umaru Musa Yar'adua an gayyace ta gudanar da wadansu ayyuka da musamman da suka shafi mahajjata.

Malama tana yawan gabatar da shirye-shirye a gidajen rediyo da talabijin, daga cikin waɗanda suka fi fice har da wanda take yi a gidan talabijin ɗin Farin Wata mai taken "Mace Ta Gari".

Wannan layi ne

Nasarorinta

Malama Rabi'atu

Asalin hoton, IMWON

Women with Substance Initiative ta ba ta lambar yabo a Abuja, haka ma kwamishinan ƴan sanda na jihar Kaduna ya ba ta lambar yabo kan wayar wa da matasa kai.

Adamu Garba ya ce: "Sarkin Zuru ma ya ba ta lambar yabo sakamakon Musuluntar da mutum 150 a wani ƙauye a ƙaramar hukumar Zuru lokacin da ta je Da'awa.

"Sannan akwai wani ƙauye ma a jihar Neja da ta samu nasarar muusuluntar da mutum a ƙalla 400 a garin, har ta jagoranci gina masallaci.

"Malama ta rayu a kan taimakon marayu da gina makarantu da masallatai. Ta kan shiga ƙauyukan da ba a taɓa tunani ba don yin da'awa," in ji shi.

Ya ce malama ta goya yara da yawa da take kula da su da karatunsu, duk da cewa ita ba ta taɓa haihuwa ba.

Cikin ayyukanta har da zuwa gidajen yari don yin wa'azi da kuma kai ziyara gidajen marayu.

Wannan layi ne

Tunawa da Malama Rabi'atu Sufyan

IMWON

Asalin hoton, IMWON

Bayanan hoto, An shaidi malama da yawon kyauta ga marasa ƙarfi

Wata ƴar jarida da ta yi aiki sosai tare da Malama Rabi'atu Sufyan, mai suna Rukayya Ayuba, mawallafiyar Mujallar Kallabi, ta ce: "A yau gaba daya tunanina da juyayin da na tsinci kaina a ciki shi ne game da rasuwa Malama Rabi'atu.

"Abin mamaki shi ne yadda hirar yar uwarta da ta taɓa ba ni shekaru kimanin 15 da suka gabata ya rinka dawo min musamman ma labarin rayuwarta a lokacin da take tasowa.

"Hakika ba zan manta da wannan labari ba musamman ganin yadda ya yi daidai da yadda ake daƙushe karatun 'ya'ya mata a yankin da ta fito daga ciki wato arewacin Najeriya.

Kafin Rabi'atu Sufyan ta shiga makarantar boko ta ce min ta sha gwagwarmaya da dama. Tun daga cin zarafi a cikin gida zuwa shiga halin ko-in-kula daga al'umma da ke kewaye da ita.

"Ta gaya min cewa mijin mahaifiyarta ne ya fara sa ta a makarantar koyon sana' a. Ya so ya tallafi rayuwarta ƙwarai da gaske amma sai fulako ya hana mahaifiyarta ta iya zama tare da ita.

"Ina tuna wannan duk kusan lokacin da na ga hoton ta a kafafen yada labarai, fuskar nan cike da tsagen Fulani (musamman ma zanen kalangu da 'yar baka).

"Sai a raina na ce lallai Malama muna alfahari da samun bafulatanar asali mai dimbin ilimi da kokarin yada shi lungu-lungu da sako-sako ba tare da gajiyawa ba.

Wannan yana tuna min da rayuwar Nana Asma'u bint Fodio da rayuwar hidimar yaɗa ilimin addinin Musulunci na 'yan taru. A duk lokacin da na ci karo da hotunanta tana ziyartar ƙauyuka da bayar da tallafi ga al' ummar Musulmi.

Wannan layi ne

Wani abu game da Rabi'atu

IMWON

Asalin hoton, IMWON

Rukayya Ayuba ta ƙara da cewa: "Wata rana da ba zan manta da ita ba ita ce ranar da na hadu da Malama Rabi'atu a gidan mai ana yi mata garanbawul na motarta saboda za ta yi tafiya.

"A nan muka zauna a wajen garejin gidan man a kan benci muna dan tattaunawa game da tarihin rayuwarta. Na tambaye ta ko wannan zuwan da take yi sabis din mota ba matsala?

"Sai ta ce min babu, saboda hidimar addini take yi. Har ma ta ƙara min da cewar akwai 'yan ƙananan gyare-gyare na mota ma da da kanta take yi saboda gudun ɓacin rana.

"A cikin shekarar da na hadu da Malama Rabi'atu tana matakin karatunta na digiri na biyu ne. Wanda sannu a hankali ta cimma bayan komawarta makarantar Islamiyya da boko da girmanta.

"Ta yi min bayani cewar ta ga amfani ilimi kwarai da gaske domin ta dandana rashinsa a farkon rayuwarta. Don haka ne ba ta yi masa riƙon sakainar-kashi ba."

Wannan layi ne