Lafiya Zinariya: Nau'o'in ciwon amosanin kashi da alamominsu
Ku latsa hoton da ke ƙasa don sauraron shirin:
Ciwon amosanin kashi wanda ake kira Arthritis da turancin Ingilishi, ciwo ne da yawaita a tsakanin al'umma, mata da maza da yara na fama da shi.
Wasu daga cikin abubuwan da ke janyo shi sun hada da yawan shekaru da aikin da ake yawan tsayuwa da kiba da shan giya da miyagun kwayoyi.
Mutane masu wasannin karfi a lokacin kuruciyarsu kan gamu da wannan ciwo idan sun fara manyanta.
Ciwo ne da ke janyo zafi ko radadi da kumburi a gabobi. In ji hukumar lafiya ta Burtaniya wato NHS.
Inda ta yi kiyasin cewa a kasar, fiye da mutane miliyan goma ne ke fama da wannan ciwon da kuma dangoginsa.
Hukumar wadda ta lissafa nau'oin amosanin kashi fiye da goma tare da takaitaccen bayanai kan kowannensu, ta ce biyu daga cikinsu su ne suka fi damun al'umma.
In da ta kara da cewa a Burtaniya kusan mutane miliyan tara ne ke fama da nau'in amosanin kashi da ake kira Ostro atritis a turance.
Yayin da kuma wasu kimanin dubu 400 ke fama da nau'i na biyun wato rumatoin arthritis.
Kimanin yara da matasa dubu 15 ne kuma ke fama da wasu nau'ukan cutar a kasar.












