Hotunan taurari masu ban sha'awa da wani dalibi ya dauka

Starlight skyline photo

Asalin hoton, Bryan Shaw

Bayanan hoto, Bryan Shaw ya ce rashin haske a yankinsa ne ya taimaka masa ɗaukar irin wannan hoton kan Dunure Castle gaɓar Ayrshire
An wallafa

Wani ɗalibi ɗan ƙasar Scotland ya ƙaddamar da hotunan sararin samaniya da ya ɗauka ta hanyar amfani da na'urar hangen nesa a bayan lambunsa.

Bryan Shaw, dalibi a Jami'ar West of Scotland, ya shafe sa'o'i da yawa yana kallon taurari da tattara hotuna da bidiyo don wani shiri na ƙarshen shekara.

Bryan Shaw holding a telescope

Asalin hoton, Bryan Shaw

Bayanan hoto, Mr Shaw ya ce ya gano ta hanyar amfani da na'urorin hangen nesa da dama lokacin da yake nazarin yadda zai ɗauki hotunan taurari.

Dalibin da ke ajin karatu na hudu ya sami nasarar ɗaukar cikakkun hotuna na gungun taurari da waɗanda ke da haske a shekaru da yawa, kamar Pleiades, Andromeda da Orion Nebula.

Whirlpool Galaxy

Asalin hoton, Bryan Shaw

Bayanan hoto, Taurarin da Mr Shaw ya dauka da na'urar hangen nesa ta telescope

Mr Shaw - wanda ya fara ɗaukar hotunan sararin samaniya a bara - yakan sadaukar da darensa kan burinsa, na ɗaukar hotunan taurari a wajen gidansa da ke c New Cumnock, gabashin Ayrshire.

Rosette Nebula

Asalin hoton, Bryan Shaw

Bayanan hoto, Gungun taurarin Rosette Nebula na da tazarar nisan shekara 5,000 daga duniya

Ya ce: "Yana cin lokaci, amma ina matuƙar so wannan. Ina shirin samun babbar na'urar hangen nesa domin faɗaɗa ilimi na, kuma don na iya ɗaukar wasu abubuwan da ba zan iya ɗauka ba a yanzu."

Ina son na ɗauki hotunan na duniyoyi da wata - abin da nake tsarawa kenan.

"Babban burina shi ne na ɗauki taurarin nebula."

Red-giant branch stars

Asalin hoton, Bryan Shaw

Bayanan hoto, Taurari

Dr Sheona Urquhart, malamin kimiya a Open University, ya shaida wa BBC cewa hotunan da aka ɗauka "abubuwa ne da ke nuna yanayin duniyarmu."

"Abin da nake tunani ya fi ban sha'awa shi ne yadda ya ba sai ka je kasa da kasa ba, ka samu hotuna masu ban sha'awa - daga gida za ka iya samun abin da kake so," in ji shi.

The Moon

Asalin hoton, Bryan Shaw

Bayanan hoto, Mr Shaw ya ce abin aka fara a matsayin aikin Jami'a yanzu ya zama wani burinsa

Dukkanin hotuna haƙƙin mallakar Bryan Shaw ne.