Ranar Mata ta Duniya: Abu bakwai da suka kamata ku sani game da wannan rana

Me yiwuwa ku taba gani a shafukan sada zumunta ana magana a kan Ranar Mata ta Duniya, ko kuma ku ji a wurin abokai suna magana a kai.
Amma shin me wannan rana ta kunsa? Yaushe ne? Shin biki ne ko kuma zanga-zanga? Akwai makamanciyarta Ranar Maza ta Duniya? Kana wadanne bukukuwa ake gudanarwa cikin wannan shekarar?
Fiye da karni guda da ya wuce, mutane da dama na bikin tunawa da zagayowar 8 ga watan Maris musamman saboda mata.
Ku karanta wannan makala don gano dalilan da suka sa:
1. Ta yaya aka fara?

Asalin hoton, Corbis / Hulton Deutsch
Ranar Mata da Duniya, ko IWD a takaicce ta Turanci, ta fara ne daga kungiyar kwadago don a san da ita a cikin ranakun shekara-shekara da Majalisar Dinkin Duniya ta ware.
An kuma dasa tushenta ne a shekarar 1908, lokacin da mata 15,000 suka yi tattaki a birnin New York na Amurka suna neman gajeren lokutan aiki, da biyan albashi mai kyau da kuma 'yancin kada kuri'a.
Shekara daya bayan nan ne, Jam'iyar Socialist ta Amurka ta fara ayyana Ranar Mata ta Duniya.
Wata mai fafutikar kare hakkin mata Clara Zetkin ce ta fara bullo da batun ranar.
Ta kuma kawo shawarar ce a shekarar 1910 a wani babban taron kasa da kasa kan mata ma'aikata a birnin Copenhagen. Mata 100 ne suka halarci taron daga kasashe 17, kuma suka amince da shawararta gabaki dayansu.
An fara bikin ranar ne a shekarar 1911, a kasashen Austria, da Denmark, da Jamus, da kuma Switzerland. An kuma yi bikin zagayowar shekara 100 a shekarar 2011, don haka a cikin wannan shekarar a takaice za mu yi bikin cika shekaru 111 da zagayowar Ranar Mata ta Duniya.
An gudanar da komai a hukumance a shekarar 1975 lokacin da Majalisar Dinkin Duniya ta fara gudanar da bikin ranar.
Take na farko da Majalisar Dinkin Duniyar ta fara amfani da shi a shekarar 1966 shi ne "Bikin Murnar Abubuwan da Suka Gabata, Tsara Abubuwa Na Gaba".
Ranar Mata ta Duniya ta kasance ranar bukukuwan duba cigaban da mata suka samu a cikin al'umma, a siyasa da kuma tattalin arziki, a yayin da tushen siyasar ranar na nufin ana gudanar da yaje-yajen aiki, da zanga-zanga don fadakarwa game da cigaba da nuna rashin daidaito.
2. Me yasa ake tunawa a 8 ga watan Maris?

Asalin hoton, Getty Images
Shawarar Clara kan Ranar Mata ta Duniya ba ta da wata tsayayyiyar rana. Ba a yanke shawara ba har sai lokacin yajin aikin yayin yaki a shekarar 1917 - kana kwanaki cikin yajin aikin ne aka tilasta wa Tsar yin murabus, kana gwamnatin lardi ta bai wa mata 'yancin kada kuri'a.
Ranar da matan suka fara zanga-zangar a Kalandar Julian, wacce lokacin ake amfani da ita a kasar Rasha - Lahadi 23 ga watan Fabrairu.
Wannan rana a Kalandar Gregoria, ranar 8 Maris - kuma shi ya sa ake bukukuwan a wannan rana a yau.
3. Me ya sa mutane ke saka kaya launin algashi?

Asalin hoton, Getty Images
Algashi, da kore, da kuma fari, launuka ne na Ranar Mata ta Duniya, kamar yadda shafin intanet na ranar ya nuna.
"Launin algashi na nuna alamar adalci da mutuntaka. Kore na nuna alamar fata. Fari na nuna alamar tsarkakewa.
Launukan sun samo asali ne daga kungiyar mata ta Women's Social and Political Union (WSPU) a Birtaniya a shekarar 1908," in ji su.
4. Shin akwai Ranar Maza ta Duniya?
Kwarai kuwa akwai, ranar 19 ga watan Nuwamba.
Amma an gudanar da bikin ne kawai a cikin shekarar 1990, sai dai Majalisar Dinkin Duniya ba ta san da ita ba.
Mutane na bikin ranar ne a kasashe fiye da 80 a fadin duniya da suka hada da Birtaniya.
Ranar na bikin tunawa da "abubuwan karuwa masu nagarta da maza suka bayar da gudumawa a kai ga duniya, da iyalansu, a kuma al'umma", kamar yadda masu shirya bikin suka bayyana.
Kuma ana amfani da ranar wajen fadakarwa kan jin dadi da abin koyin da mazan suka zo da shi da kuma inganta dangantakar jinsi. Taken shekarar 2021 shi ne "Dangantaka mai kyau tsakanin mata da maza."
5. Ta yaya ake gudanar da bikin Ranar Mata ta Duniya, shin akwai sauran wasu bukukuwan a cikin wannan shekarar?

Asalin hoton, Getty Images
Ranar Mata ta Duniya ranar hutu ce a kasashe da dama da suka hada da Rasha, inda ake kara ninka yawan sayar da furanni a kwanaki uku zuwa hudu na ranar aiki kafin ranar 8 ga watan Maris.
A kasar China, ana bai wa mata da dama hutun rabin rana a ranar 8 ga watan Maris, kamar yadda Majalisar Kasa ta bayar da shawara.
A kasar Italiya, an bikin Ranar Mata ta Duniya ko kuma la Festa della Donna, ta hanyar bayar da kyaututtukan furannin mimosa blossoms. Babu tabbaci game da takamaimen wannan al'ada amma an yi amanna ta samo asali ne daga birnin Rome bayan Yakin Duniya na Biyu.
A Amurka, watan Maris watan tarihin mata ne. Sanarwar da fadar shugaban kasa ke fitarwa a ko wace shekara na mutunta cigaban matan Amurka.
Wannan shekarar, bukukuwan za su cigaba da bambanta saboda annobar korona, kana ana sa ran gudanar da bukukuwan a fadin duniya.
6. Mene ne taken bikin ranar matan na bana?

Asalin hoton, Getty Images
Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da taken na shekarar 2022 a matsayin "Daidaiton jinsi a yau, don dorewar nan gaba."
Bukukuwan za su duba matsayin mata kan sauyin yanayi.
Amma akwai sauran taken a fadin duniya.
Shafin intanet na Ranar Mata ta Duniya - wanda ya ce an tsara shi ne don "samar da wani dandali don taimakawa wajen kawo sauyi mai amfani ga mata" - ya zabi take mai maudu'in #BreakTheBias kana yana yin kira ga mutane su rika tunanin "duniya wacce babu son kai, babu nuna wariyar jinsi, ko bambanci."
7. Me ya sa muke bukatarta?

Asalin hoton, Getty Images
Mun ga gagarumin koma-baya a cikin fafutikar neman 'yancin mata a cikin shekara daya da ta wuce.
Dawowar kungiyar Taliban kan mulki a watan Agusta ya sauya rayuwar matan Afghanistan - an haramta wa 'yan mata samun ilimin sakandare, kana an soke ma'aikatar harkokin mata a kasar, har ila yau an fada wa mata kada su koma wuraren aikinsu.
A Birtaniya, kisan Sarah Everard da wani jam'in dan sanda ya yi, ya haifar da muhawarori game da kariya da tsaron lafiyar mata.
Har ila yau annobar korona na cigaba da yin mummunan tasiri a kan 'yancin mata.

Asalin hoton, Getty Images
Kamar yadda rahoton gibi tsakanin jinsi na duniya na shekarar 2021 na taron tattalin arziki na duniya ya bayyana, lokacin da ake bukata na cike gibin a fadin duniya ya karu.
Wani binciken da Sashen Al'amuran Mata na Majalisar Dinkin Duniya ya yi kan kasashe 13, ya nuna cewa kusan 1 a cikin 2 wato kashi 45 bisa dari na mata sun bayar da rahoton cewa sun fuskanci cin zarafi a lokacin barkewar annobar korona.
Wannan ya hada da cin zarafin ba a fili na, da na furta kalamai da kuma hana samun damar ababen more rayuwa da aka fi bayar da rahoto a kai.
Duk da damuwar da ake da ita kan cutar korona, an gudanar da gangamin ranar matan a fadin duniya a shekarar 2021.

Asalin hoton, Getty Images
A kasar Mexico, kungiyoyin mata sun mayar da shingen waya da aka kafa don kare fadar gwamnatin kasar, zuwa wurin tunawa da wadanda harin nuna wariya ga mata ya shafa.
A halin da ake ciki, mata a kasar Poland sun gudanar da zanga-zanga a fadin kasar bayan bullo da dokar haramta zubar da ciki a watan Janairun shekarar 2021.
Ko da yake a shekaru kadan da suka gabata, an samu cigaba - musamman a bangaren shugabancin mata.
Kamala Harris ta zama bakar fata mace ta farko kana Ba'Amurkiya yar asalin yankin Asiya ta farko da ta zama mataimakiyar shugaban kasa a shekarar 2021.
A cikin shekarar ne kuma, kasar Tanzania ta rantsar da shugabar kasa mace ta farko Samia Suluhu Hassan, yayin da a kasashen Estonia, da Sweden, da Samoa da kuma Tunisia suka samu firaministoci mata a karon farko cikin tarihi.
A watan Janairun shekarar 2022, aka rantsar da Xiomara Castro a kasar Honduras a matsayin shugabar kasa mace ta farko.
A shekarar 2021, kasar New Zealand ta amince da biyan kudin hutun zaman alhini ga mata da mazajensu wadanda suka yi bari ko haihuwar jaririn da babu rai. A yayin da a shekarar 2020, kasar Sudan da haramta yi wa mata kaciya.
Kana wa zai manta da tasirin maudu'in nan na tattaunawar #MeToo da ke magana a kan fuskantar cin zarafi da lalata?
Shekarar da ta gabata an shaida cigaba game da batun zubar da ciki a kasashe da dama.
A cikin watan Fabrairu, kasar Colombia ta janye dokar hana zubar da cikin da ya kai kimanin makonni 24.
A Amurka, yanzu haka an iyakance 'yancin zubar da ciki a wasu jihohin, inda a jihar Texas haramcin ya fara daga juna biyun da ya kai kimanin mako shida.











