Yunwa na sake kassara milyoyin al'umma a Yemen - MDD

y

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Shirin samar da abinci na Majalisar Dinkin Duniya ya yi gargadi da sanar da cewa dole ya zabtare milyoyin tallafin da ya ke bai wa al'ummar Yemen saboda karancin kuɗaɗen tallafi.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce dole ta fi bada fifiko ga mutanen da ke cikin matsananciyar yunwa a yanzu ganin kuɗaɗen agaji ba sa shigo musu da kyau.

Shirin ya ce kuɗaɗen da suke samu na tallafi sun yi kasa sosai a wannan shekara saboda matsalolin da suka karu a duniya, kamar annobar korona da sauyin yanayi.

Shugabar shirin shiyar ƙasashen gabas ta tsakiya da Afirka, Corinne Fleischer, ta shaidawa BBC cewa ana cikin yanayi kuma dole su sake jadada bukatar neman tallafi mai kwaɓi.

"Muna bukatar karin kuɗi sosai, muna bukatar agaji mai kwaɓi. Muna bukatar dala miliyan 806 kari cikin nan da wata shida domin ciyar da mutane miliyan 13.

Don hakan mun keɓe kuɗaɗe ga mutane miliyan biyar da ke cikin tsananin yunwa a yanzu. Sannan mutum miliyan 8 da suka yi saura mun ware musu rabin abin da za su bukata.

Hakan na nufin, muna karɓan abinci daga mutanen da ke cikin yunwa muna bai wa wadanda ke cikin matsanancin yanayi saboda yunwa ta cinyesu."

Ms Fleischer da ke cewa mutane na faɗi tashin ganin sun ciyar da 'ya'yansu, ta kuma shaida yada wata uwa ta shafe kwanaki ba ta ci abinci ba saboda kawai 'ya'yanta su samu abin kai wa baki.

"Ta shaida mana cewa kwanansu biyu ba su abinci ba, su na bai wa yaransu abinci ne. Wasu na cewa dole yanzu su koma cin zallan biredi da shayi. Hakan ba zai wadatar ba samun abinci mai gina jiki ba."

Hukumar WFO dai ta ce kudaden da take samu daga masu bada tallafin bai kai kashi 1 cikin 5 na dala biliyan biyu da ake bukata don ayyukan agaji a kasar Yemen.

Wanann dai ba shi ne karon farko da shirin samar da abinci na Majalisar Dinkin Duniya ke aike da irin wannan gargadi ba.

Ko a kwanaki baya sai da majalisar ta yi kira da a gaggauta taimakawa miliyoyin al'ummar Yemen wadanda ke fuskantar barazanar yunwa.

Yaƙi tsakanin dakarun Saudiya da ke goyon bayan gwamnatin ƙasar da kuma 'yan tawayen Houthi wadanda ke da alaka da Iran ya dai-dai ta ƙasar.