Telegram ya zama dandalin yaɗa hotunan tsiraicin mata ba da izininsu ba

Collage of classical nudes alongside Telegram logos over an orange background. Devil emojis coming out of phone.

Asalin hoton, Klawe Rzeczy

An wallafa

Wani binciken BBC ya gano cewa ana yada hotunan tsiraicin mata masu tarin yawa a manahajar sada zumunta na Telegram don cin zarafinsu, da ci da ceto da kunyatar da su.

GARGADI: MAKALAR NA KUNSHE DA ABUBUWAN MASU ALAKA DA JIMA'I

Cikin 'yan dakikoki bayan da Sara ta gano cewa an yada hoton tsiraicinta a Telegram, rayuwarta ta sauya.

An kuma kara da shafukanta na Instagram da Facebook da kuma lambar wayarta.

Ba tare da ɓata lokaci ba kuma wasu mutune da ba ta san ko su wanene ba suka tuntubeta suna neman karin wasu hotunan.

"Sun saka ni jin kamar ni karuwa ce saboda [sun yi amanna] ni ce na yada hotunan tsiraici na, Hakan na nufin ba ni da wata daraja a matsayina na mace," ta ce.

Faɗa mana labarinku: Kuna iya aiko mana da labarin yadda kuka taɓa samun kanku a takaicin yaɗa hotunan tsiraicinku da aka yi ba tare da saninku ba. Amma za mu ɓoye sunanku.

Photograph of Sara
Bayanan hoto, Sara ta daina fita bainar jama'a bayan da aka yaɗa hotunan tsiraicinta

Sara, ba sunanta na gaskiya ba, ta yada hoton da ta dauka ita da wani, amma sai ga shi ya fita a cikin shafin kungiyar Telegram mai mabiya 18,000, akasari daga unguwarsu a Havana, kasar Cuba.

Yanzu tana fargabar me yiwuwa wasu baki a kan titi sun ga tsiraicinta. "Na ji bana son fita waje, ba na son duk wata mu'amala da kawayena. A gaskiyar magana na sha wahala sosai."

Ba ita kadai ba ce. Bayan watannin da muka shafe muna bincike game da manahajar ta Telegram, mun gano wasu rukunai masu yawa da kafofi da ke yada dubban hotunan da aka dauka a asirce, aka kuma yada a akalla kasashe 20.

Nigar ta nemi mafaka a wani wuri mai nisan dubban mil daga kasar Cuba.

Photograph of Nigar
Bayanan hoto, An tilasta Nigar tserewa daga kasar

'Yar kasar Azerbaijan ce, amma an tilasata mata barin kasarta ta asali. A shekarar 2021, an aike wa da danginta wani bidiyonta tana jima'i da mijinta, kana aka yada a Telegram.

"Mahaifiyata ta fara kuka sannan ta fada min: 'Akwai wani bidiyo, an turo min ne,'' ta ce. "Na shiga bacin rai matuka, matukar bacin rai."

An yada bidiyon a rukunin jama'a na shafin mai mambobi 40,000. A cikin bidiyon, an rufe fuskar mijin Nigar, amma ita kuwa an nuna fuskarta sosai.

Ta yi manna tsohon mijinta ne ya dauki bidiyon a asirce don yi wa danuwanta ci da ceto, wani sanannen dan fafutika mai sukar lamirin shugaban kasar Azerbaijan.

Ta ce an fad awa mahaifiyarta cewa za a saki bidiyon a cikin Telgram muddin danuwan nata bai daina fafutikar da yake yi ba.

"Su kan rika yi maka kallon kamar ka yi abin kunya. Wa ya damu ko kana da aure?" in ji Nigar.

Nigar ta ce ta tuntubi tsohon mijinta game da bidiyon amma ya musanta dauka.

Mun yi kokarin ji daga gare shi amma ya ki ya bayyana komai.

Har yanzu Nigar na kokarin mantawa da komai ta cigaba da rayuwarta: "Na kasa mantawa. Na kan je wurin ƙwararru a fannin kwantar da hankali a ko wane mako," ta ce.

"Sun ce har yanzu babu wata alama ta cigaba. Sun tambaye ni ki zan iya mantawa, n ace musu a'a.

An mika koke kan duka hotunan Nigar da Sara ga Telegram, amma kuma dandalin bai yi wani abu a kai ba. Halin da suka shiga na daban ne.

BBC na bin diddigin kafofin Telegram 18 da rukunai 24 a kasashen da suka hada da has been Russia da Brazil, da Kenya da kuma Malaysia. Yawan adadin wadande ke amfani da dandalin ya kai miliyan biyu.

Screenshot from inside a Telegram channel says "Secret Archives 18" and "Only young girls"

Ana yada bayanai kamar adireshin gidaje da lambobin wayar iyaye tare da horuna da bidiyon tsiraicin.

Mun ga yadda jagororin rukunan dandallin ke tambayar mambobinsu su rika aiko da hotunan tsofaffin matansu ko 'yanmatansu, da abokan aiki ko na karatu ta cikin dandalin don a rika yada wa ba tare da an bayyana sunan wanda ya turo ba.

Yanzu Telegram y ace yana da masu bibiyarsa fiye da miliyan dari biyar a fadin duniya - wanda ya zarta na shafin Twitter - wanda yadda shafin ke ikirarin mutunta sirrin jama'a ya janyo hankali tare da kara yawan masu amfani da shi.

Crowd of pro-democracy protesters waving red and white flags in Belarus

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, An yi amfani da Telegram wajen kitsa zanga-zanga a Belarus

A watan Janairun shekarar 2021 ne miliyoyin mutane suka koma yin amfani da dandalin sada zaumuntar na Telegram daga manahajar WhatsApp, wacce ta sauya ka'idojin sirrin ta.

Dandalin ya kuma janyo hankulan masuamfani da shi da ke neman gurbin da babu ka'idoji da yawa, da suka hada da wadanda aka haramta wa amfani da wasu dandanlin.

"Kamar yadda Telegram da mamallakinta suka bayyana, ba sa son su rika tantance masu amfani da shafinsu," in ji Natalia Krapiva, ta kungiyar kare 'yancin masu amfani da shaufkan sada zumunta ta Access Now.

Amma kuma bincikenmu ya nuna cewa wannan halayya da rikon sakainar kashi wajen sa ido ya sa Telegram zama wata matattar da kuma tudun-mun-tsira ga wadanda ke son su rika kwarmata tare da yada hotuna da bidiyon tsiraicin.

Telegram ba shi da wata takamaimiyar manufa ko ka'idoji na shawo kan matsalar yada hotuna da bidiyon tsiraici, amma ka'idojin tafiyar da dandalin ya sa masu amfani da shi suka amince "kada a yada abubuwan da suka shafi batsa a dandalin da jama'a za su iya kallo na Telegram da sauransu".

Screenshot of Telegram's in-app reporting tool for reporting content that breaks their terms of service.

Yana kuma da wata manahajar kao rahoto a duka rukunan sirri da na sarari, da kuma kafofi inda masu bibiya za su iya kai rahoton yada batsa.

Don gwada yadda Telegeram ke kafa ka'idoji da manufofinta, mun gano tare da kai rahoton hotuna 100 a matsayin na batsa ta cikin manahajar kai rahoton da ke cikin dandalin.

Bayan wata guda, ba a iya bude 96 daga ciki ba. Mun kasa gano sauran hudun, saboda suna cikin rukunan da ba za mu iya shiga ciki ba.

Bayan da kamfanin ya cire Telegram daga shagon manahajojinsa na intanet na wucin gadi saboda faya-fayen bidiyo irin wadanda muka aike, Telegram ya dauki karin matakai kan hotunan cin zarafin kananan yara.

Members of the far-right group Proud Boys attend a rally in Portland, Oregon, U.S. September 26, 2020

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Members of far-right groups moved to Telegram

Dandalin ya kuma hada kai da hukumar lura da aikata manyan laifuka da Kungiyar Tarayyar Turai EU a shekarar 2019 don kawar da abubuwa da dama na kungiyar IS da suka mamaye shafin.

"Mun san cewa Telegram zai iya cirewa, kuma yana shan cire abubuwa a suka danganci ayyukan ta'addanci ko wasu abubuwa da suka shafi tsatsauran ra'ayin siyasa,'' in ji Dakta Aliaksandr Herasimenka, mai bincike a Cibiyar Intanet ta Oxford.

Amma kuma da alamu cire hotunan tsiraici bai zama muhimmin abu ba.

Telegram ya ki ya amince mu yi hira da shi, amma a wata sanarwa ya shaida mana cewa bai cika tsananta sa ido kan abubuwan da jama'a ke yi ba, kana yana duba rahoton mabiyansa game da abubuwan da suka saba ka'idojin da ayyukansa.

Photograph of Joanna
Bayanan hoto, Joanna reported images that were shared without consent in Telegram

Telegram din bai tabbatar da ko an amince da yada hotunan tsiraicin mutane ba tare da saninsa ba a dandalin, ko kuma akan cire su ba.

Abin da za a jira a gani shi ne ko tsawon wane lokaci ne kamfanin zai inganta aikin sa ido kan ka'idojin a yayin da yake shiga sabuwar gogayyar kasuwannni tare da fara samun kudin shiga.

Ga matan da aka zubar wa da kima kana suke cikin kuncin rayuwa saboda yada hotunan tsiraicinsu a Telegram, ba za a samu isasshen sauyi a nan kusa ba.

Investigation by the BBC World Service Disinformation team.