Juyin mulkin da ake yi a Afirka ba zai hana dimokuradiyya aiki ba

People celebrate in the streets with members of Guinea's armed forces after the arrest of Guinea's president, Alpha Conde, in a coup d'etat in Conakry, September 5, 2021.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Mutane na taya sojoji murnar ƙwace mulki a Guinea a shekarar da ta wuce
An wallafa

Bayan juyin mulki da aka fuskanta a ƙasashen Afirka biyar cikin shekarar da ta gabata, wasu na ganin ba lallai ne dimokuraɗiyya ta yi aiki ba a nahiyar. Sai dai Leonard Mbulle-Nziege da Nic Cheeseman na ganin - duk da matsalolin da ake samu - dimokuraɗiyyar ce mafita a Afirka.

An fuskanci juyin mulki iri-iri a Afirka da ke barazanar mayar da ita baya zuwa shekarun 1980. Burkina Faso, Chad, Guinea, Sudan, Mali duk sun tsinci kan su a hannun sojoji, inda suka maye gurbin gwamnatocin dimokuraɗiyya.

Lamarin ya kusa ƙazancewa saboda samun rahoton yunƙurin juyin mulkin da bai yi nasara ba a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, sai kuma kwana huɗu bayan haka, Guinea-Bissau.

Duk sanda aka samu yanayi irin wannan, masu cewa dimokuraɗiyya ba za ta yi aiki a Afirka ba - ba za ta iya yin aiki ba - na ƙara ɗaukaka murya. A gefe guda, mutane sun yi murna da kifar da gwamnatin farar hula a wasu ƙasashe.

Duk da cewa abu ne mai wuya a ƙi fassara abubuwan da ke faruwa a matsayin gazawar dimokuraɗiyya, amma hakan kuskure ne. Ko da a ƙasashen da aka yi juyin mulkin, akasarin 'yan ƙasar sun fi son su zauna a ƙarƙashin dimokuraɗiyya fiye da mulkin kama-karya.

Bugu da ƙari, duk da damuwa da ake nunawa kan yadda siyasar jam'iyyu masu yawa ke fama, a taƙadiri na tsakatsaki dimokuraɗiyya ta fi haɓaka tattalin arziki da kuma inganta harkokin jama'a, kamar yadda wani bincike na Jami'ar Cornell da ke Amurka ya nuna.

Idan aka kwatanta, gwamnatin soja na da tarihin take haƙƙin ɗan Adam da kuma daƙile ci gaban tattalin arziki.

A Mali supporter cheers before the Africa Cup of Nations (CAN) 2021 round of 16 football match between Mali and Equatorial Guinea at Limbe Omnisport Stadium in Limbe on January 26, 2022.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wasu magoya bayan tawagar ƙwallon ƙafa ta Mali sun dinga ɗaga hoton shugaban gwamnatin soja ta ƙasar, Assimi Goita, yayin wasannin gasar Kofin Ƙasashen Afirka da aka yi a Kamaru

A wani ƙaulin kuma, Afirka na ci gaba da cin ribar dimokuraɗiyya - matsalar na farawa ne yayin da wani shugaba a mulkin dimokuraɗiyya ya fara amfani da wasu dabaru na kama-karya don ya ci gaba da zama a kan mulki ko da al'ummarsa ba sa so.

Wannan lokaci ne mai haɗri sosai. A wasu ƙasashe kamar Guinea da Mali, shugabanninsu ba su rasa farin jini ba saboda sun gina dimokuraɗiyyar da ta dace da lamurran Afirka ba. A madadin haka, shugabannin sun rasa goyon bayan jama'a ne saboda wasu lamurra sun sha kan su - a Mali da Burkina Faso misali - maganar hare-haren masu iƙirarin jihadi ce.

Hakan zai bayyana a fili ne idan muka duba abin da ke faruwa ba wai yadda muke ji a kafafen yaɗa labarai ba, cewa mene ne dalilin da ya sa mutane ke murna da juyin mulkin baya-bayan.

A Guinea, tsohon Shugaba Alpha Condé ya sauya dokokin tsarin mulki a 2020 don ya samu damar yin wa'adi na uku. Hakan bai yi wa jama'a daɗi ba, musamman ma idan aka duba cewa daga zaɓen raba-gardama har na shugaban ƙasar da ya lashe daga baya ba sahihai ba ne.

Haka nan, Mista Conde ya dinga komawa ɗan kama-karya a watanni kafin juyin mulkin, yana kullewa tare da muzguna wa 'yan adawar siyasa da masu sukar gwamnati.

Shi ma Shugaban Mali Ibrahim Boubacar Keïta an zarge shi da yin maguɗi a zaɓen 2020 na 'yan majalisa. A ci gaba da ƙaruwar rashin tsaro da kuma cin hanci, hakan ya sa ya rasa goyon bayan jama'a.

A ƙasashen biyu, shugabannin sun rasa farin jini saboda sun kauce wa tsarin dimokuraɗiyya, ba wai 'yan ƙasa ne suka gaji da tsarin ba.

Shakka babu, wasu sun 'yan ƙasashen sun yi murna da juyin mulkin da aka yi wa Mista Conder da Keita, amma kuma sabin binciken da cibiyar Afrobarometer ta yi ya nuna cewa kashi 76 cikin 100 na 'yan Guinea da kashi 70 na 'yan Mali ba su goyi bayan sojojin ba.

Shi dai wannna bincike ya gano cewa kashi 77 na 'yan Guinea na goyon bayan dimokuraɗiyya, yayin da kashi 70 na 'yan Burkina Faso da kuma 62 na 'yan Mali ke goyon bayan tsarin. Kuma wata alama ce da ke nun acewa 'yan ƙasashen na goyon bayan juyin mulkin ne saboda a share fagen wata sabuwar gwamnati, ba wai don suna son zama a ƙarƙashin mulkin soja ba.

People continue protests demanding the restoration of civilian rule in Khartoum, Sudan on January 30, 2022.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Har yanzu masu zanga-zanga a Sudan na ci gaba da saka rayuwarsu cikin haɗari don kawo ƙarshen mulkin soja

A Sudan misali, dubban 'yan ƙasa sun hau kan tituna da zimmar nuna ƙin jinin gwamnatin sojan da ta ƙwace mulki a 2021 inda suka daƙile yunƙurin kafa sabuwar gwamnati bayan hamɓarar da gwamnatin Omar al-Bashir da ya shafe kusan shekara 30 kan mulki a 2019. Duk da cewa an kashe kusan mutum 79 tare da jikkata ɗaruruwansu, har yanzu 'yan Sudan ba su daina hawa kan tituna ba.

Ƙarin dalilin da ke nuna cewa har yanzu tsarin dimokuradiyya ne ya fi dacewa a Afirka - hatta a ƙasashen da ba a yin ta - shi ne irin gazawar mulkin soja.

A general view of Volkswagen's Electric Golf cars at the charging station at the Kigali Convention Centre, in Kigali on November 2, 2021.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Ƙasar Rwanda na bayyana kanta a matsayin ƙasar kimiyya da fasaha amma babu damar suka gwamnati

Duk da haka Rwanda ta fita daban a nata salon. Gaba ɗaya dai, rashin yin abubuwa a bayyane da shugannin kama-karya ke aikatawa ya jawo cin hanci da kuma rashin ci gaban tattalin arziki.

Saboda haka, a iya cewa dimokuraɗiyya a Afirka ta cimma nasarori a ɓangaren tattalin arziki da kuma yin ayyuka mafiya kyau wajen aiwatar da tsarin kyautata wa al'umma. Haka nan, da wuya su aikata cin zarafin ɗan Adam.

Wannan ta sa sojoji ke cewa suna ƙwace mulkin ne saboda su dawo da doka da oda da kuma tseratar da dimokuradiyya daga kanta da kanta.

Abu ne mawuyaci gwamnatocin soja su fitar da mutane daga ƙangin da suke ciki saboda kowane juyin mulki yana mayar da ƙasa baya ne a ɓangaren dimokuraɗiyya sannan kuma tauye 'yancin mutane na zaɓar wanda suke muradi.

Saboda akwai buƙatar gina cibiyoyin dimokuraɗiyya masu ƙarfi idan ana so a kawo ƙarshen matsalar tsaro da tashin hankali, waɗanda 'yan siyasa ba za su iya yi musu tasiri ba, ba wai cibiyoyin kama-karya ba waɗanda za su kawar da 'yan ƙasa gefe ba kuma su yi wancakali da muradansu.

Leonard Mbulle-Nziegemai bincike ne a Africa Risk Consulting (ARC, shi kuma Nic Cheeseman farfesa ne na dimokuraɗiyya a Jami'ar Birmingham da ke Birtaniya.

line