Abin da ya sa 'yaki da zuciya' ba shi da fa'ida

Grumpy cat

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Daga David Robson
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Future
  • An wallafa

Ka yi tunanin cewa ba ka dade da gamuwa da wani yanayi maras dadi ba - misali wani abokinka ya manta da zagayowar ranar haihuwarka, ko an ki daukar ka wani aiki da ka nema, ko kuma ka farka daga barci sai kwatsam ka tuna cewa za ka koma bakin aiki a ranar bayan wani dogon hutun da ka yi.

Shin yaya irin wadannan abubuwan ke sosa maka rai?

Kana iya gaya wa kanka cewa ba abin damuwa a kai ba ne. Kana kuma iya kauce wa yin tunani kan labarin maras dadi, kuma idan ka tuna da shi sai ka rika tambayar kanka dalilin da ya sa ba ka da juriya sosai.

Ana iya bayyana wannan halayyar ta dora wa kai laifi a matsayin ta "kunyata zuciya": wato gazawa ce ga mutumin da bai iya yakar damuwa ba.

Kallon bangaren da ke karfafa zuciya ga kowane irin lamari na iya zama tamkar karfin gwuiwa, ko ma a ce jarumta.

Sai dai idan aka kafe a kan wannan hanyar, mutum na iya dora wa kansa laifi idan wasu batutuwan da ke bukatar ya nuna fushi ko murna idan lamuran yau da kullum sun auku.

Saboda nuna damuwa kan abubuwa na rashi ko na fushi ko na damuwa abu ne da kowa ke son kauce musu, wani bincike na cewa rungumarsu na da fa'ida a rayuwarmu.

Amma ba ina magana ne kan rungumar matsananciyar damuwa irin wadda ke damun wasunmu ba, irin wanda ke kai mutum asibiti domin likitoci su ba shi kula ta musamman.

Ina magana ne kan damuwa mai zuwa ta wuce ta wucin gadi, na wasu sa'o'i zuwa 'yan kwanaki.

Irin wadannan ba su da hatsari ga zamantakewarmu ta lokaci mai tsawo, saboda haka babu laifi idan mun rika bijire musu.

A woman holding an umbrella looks out at the rain

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Akwai batutuwan damuwa da ke wucewa kamar gajimare - sai dai babu fa'aida a rika kauce mu su

Kamar yadda wata masanar falsafa dan kasar Italiya Ilaria Gaspari ta ce cikin littafinta na baya-bayan nan mai suna Vita Segreta Delle Emozioni (Boyayyen Sirrin Halaye), kokarin da ake yi na danne yadda muke ji na iya kara yawan "kunya" da "tsoro" ga yadda dama muke ji.

Ta ce sakamakon haka na haifar da wata damuwar da ta fi wadda muke son kaucewa tun da farko.

"Na dade kafin in fahimci cewa bin zuciya bai kasance rashin natsuwa ko kwarkwarcewa ba, sai dai alama ce ta zama mai rai, mai rungumar zahirin abubuwan da ke faruwa a duniya."

Gaspari na magana ne kan abin da ya faru gare ta kai tsaye, amma wani jerin bincike na kimiyya ya tabbatar cewa "kunyata zuciya" na iya cutar da lafiyarmu.

Rungumar mai kyau da mummuna

Na fara mayar da hankali ne kan tasirin "kunyata zuciya" yayin da nake binciken rubuta littafina The Expectation Effect (Tasirin Sanya Rai). Akwai tarin shaidar da ke nuna yadda za mu iya samar wa kanmu lamurran da za su cika ma na burinmu.

Na yi tunanin ko lamarin ya shafi tunaninmu. A maimakon sauya yadda muke kallon batutuwa, muna iya sauya tunaninmu game da batutuwan - kuma wannan matakin na iya inganta kiwon lafiyarmu na lokaci mai tsawo.

A misali, koma baya ba abin jin dadi ba - amma kana iya gane cewa yana taimaka ma na koyon darussa daga kurakuren da muka tafka.

Makamashi mai haifar da bunkasa

Tuni kuma na gano dumbin shaidun da ke nuna yadda runumar hali maras dadi da mutum ya sami kansa a ciki na iya taimaka ma sa a rayuwarsa nan gaba.

A dubi batun damuwa a misali. Muna iya tsammanin damuwa na iya lalata yadda muke gane amfaninta da yadda za ta iya yin tasiri a garemu.

Muna iya kallon yadda muke ji a matsayin wata hanyar samun karfin gwuiwa.

Da alama dan fim din nan Robert Pattinson na amfani da wannan tsarin wajen magance tsoro da yake fuskanta yayin da yake taka rawa a wurin daukar fim. A dogon zango yana iya rage fadawa ciin matsananciyar gajiya da sarewa.

A jogger holds his head in his hands as he sits on a step and looks to the floor

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ba lallai ne shiga wani hali maras dadi ya cutar da mu ba

Akwai kuma wani zaton da ya shafifushi. Muna iya yarda cewa rashin samun yadda muke so na rage ikon da mue da shi kan batutuwa, amma muna iya kallon yanayin a matsayin mai ba mu karfin gwuiwar da zai sa mu bukaci a ba mu abin da ke mallakinmu ne.

Har yanzu masana kimiyya na binciko hanyoyin da yanayi ke yi tasiri ga ingancin lafiyarmu, kamar yadda wani bincike na Max Planck ya samar - sai dai tarin bayanan da aka wallafa na tabbatar da alakar da ke tare da yanayi da kuma kiwon lafiyar dan Adam.

Siffofi daban-daban

Shigowar wannan sabuwar shekarar na iya ba mu kyakkyawan damar ajiye wannan ilimin gane alakar hai da ake ciki da lafiyarmu.

Ga wadanda ke yankin arewacin duniya, yankin yafi sanyi da zama jikakke, kuma komawa bakin aiki na iya zama maras dadi bayan bukukuwan karshen shekara.

Wasunmu na iya samun kanmu cikin damuwar shiga sabuwar shekara mai cike da sarkakiya yayin da muke fatan samun bunkasar rayuwa - wadanda ka iya haifar da yanayin rashin jin dadi da damuwa.

A wasu lokutan kuma za mu iya samun kanmu cikin damuwar da babu alamar mafita daga gareta - kuma tilas mu bukaci dukan tamakon da ya dace domin ficewa daga halin da muka sami kanmu.

Sai dai a zahiri, halayen da muke samun kanmu a ciki ba iri biyu ne ba kawai, wato mai dadi da maras dadi, ko mai kyau da maras kyau, amma suna bayyana ne ga siffofi daban-daban - kuma mayar da hankali kan duka wadannan nau'ikan halin da muke ciki zai taimaka ma na iya takun da ya dace a rayuwarmu.

*David Robinson marubuci ne kan ilimin kimiyya wanda mazaunin birnin Landan na kasar Birtaniya ne.

An wallafa sabon littafinsa mai suna The Expectation Effect: How Your Mindset Can Transform Your Life a Birtaniya ranar 6 ga watan Janairu, za a kuma wallafa shi a Amurka ranar 15 ga watan Fabrairu. Ana iya bin sa a Twitter a @d_a_robson.

An fara wallafa wannan makalar ce a shafin BBC Future.