Afghanistan: Mutanen da ke kwana a kan titi saboda bala'in yaƙin Afghanistan

Girl seen walking away from the camera
    • Marubuci, Daga Yogita Limaye da Ashitha Nagesh
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Kabul da London
  • An wallafa

Lokacin da suka isa can, mutane da dama na kwana a kan tituna da manyan ɗakunan ajiyar kayayyaki da aka yi watsi da su.

Suna ta fama da wahalhalu na samun abinci, da matsuguni, da sauran abubuwan amfanin yau da kullum kamar magunguna da kayayyakin kiwon lafiya.

Amma sun san ba su da wani cikakken zaɓi - sai dai na zama cikin halin matsi a birnin Kabul ko kuma na yiwuwar hallaka a cikin gidajensu a garuruwansu da suka baro.

Yanzu haka, dubbai sun tattaru a wasu sansanonin da suka kakkafa a wani sarari mai cike da ciyayi a wajen birnin.

Asadullah, wani mai shekara 35 da ke sayar da kayayyaki a bakin hanya a lardin Kunduz ya zo babban birnin ne tare da matarsa da 'ya'yansa mata ƙanana biyu a cikin farkon wannan makon, bayan da mayaƙan Taliban suka banka wa gidansa wuta.

"Ina kasuwanci a bakin titi ne, ina sayar da abinci da kayan ƙamshi…amma a lokacin da mayakan Taliban suka shigo kai hari ne muka dawo birnin Kabul," ya shaida wa BBC.

"Yanzu ba mu da kudin sayen burodi, ko samun magani ga 'ya'yana."

A yayin da fada da tashe-tashen hankula ke kara rincabewa a Afghanistan, kana mayakan Taliban na kara karbe ikon sabbin yunkuna a arewacin kasar, dubban mutane na cigaba da tserewa daga gudajensu don neman mafaka a Kabul babban birnin kasar.

Asadullah
Bayanan hoto, Asadullah yana sayar da kayayyaki ne a bakin titi a yankin Kunduz
Asadullah's two daughters
Bayanan hoto, Ƴaƴan Asadullah mata biyu kenan da ke kwana a kan titi a Kabul

Asadullah da iyalansa na kwana a bakin titi.

"Duka gidanmu da kayayyakinmu sun ƙone, shi ya sa muka taho Kabul muna addu'a Allah ya taimake mu.

"Rokoki da bama-bamai sun fada gidanmu…an yi mummunan artabu a cikin kwanaki bakwai da suka gabata, ba mu da burodin da za mu ci kuma duka shaguna da gidajen burodi a rufe suke.''

Wata mata wacce bata bayyana sunanta ba, ta shaida wa BBC cewa ta tsere daga gidanta a arewacin birnin Pul-e-Khumri tare da mijinta da 'yayanta. Ta ce mijinta ya samu rauni a yakin.

"Mun kasance cikin zaman jin dadi da walwala, amma saboda fashewar bama-bamai mun rasa gidajenmu shi ne muka zo nan,'' ta ce. ''Mun bar gidajenmu daga mu sai kayan jikinmu kana babu kudi.''

Unnamed woman who spoke with the BBC
Bayanan hoto, Wannan matar ta ce iyalanta a baya na cikin jin daɗi a Pul-e-Khumri,

Kungiyoyin bayar da agaji sun yi ta gargadin karuwar 'yan gudun hijira a Afghanistan tun bayan da dakarun da Amurka ke marawa wa baya suka fara ficewa daga kasar a farkon wannan shekarar, bayan safe shekaru 20 suna gudanar da aikin soji.

An fara aikin sojin a shekarar 2001 bayan harin sha day aga watan Satumbar 9/11 a Amurka. Yanzu akasarin dakarun kasashen waje sun janye.

Tun bayan nan ne, arangama tsakanin mayakan Taliban da dakarun gwamnati da kara ta'azzara. Kungiyar Taliban ta karɓe ikon akalla takwas daga cikin manyan larduna 34 na kasar, kuma suna barazanar karbe karin wasu.

Jaridar Washington Post ta wallafa bayanan wasu jami'an gwamnatin Amurka da ba ta bayana sunayensu ba na cewa shi kan sa birnin Kabul ka iya fadawa hannun Taliban a cikin kwanaki 90 masu zuwa, a yadda binciken rundunar sojin Amurka ya nuna.

Tashin hankalin ya haddasa karuwar mutanen da ke tserewa gidajensu zuwa babban birnin kasar.

A cikin watan Yuli Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa karin wasu mutane kusan 270,000 sun rasa matsugunansu a kasar bayan da dakarun suka fara janyewa - an kuma ƙiyasta cewa wannan adadi ya karu a cikin kwanaki kadan da suka gabata.

Yayin da hakan ke faruwa, fararen hula fiye da 1,000 ne aka hallaka kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana.

Crowds of displaced people in Kabul
Bayanan hoto, Dubban mutane na samun mafaka a wani sansani a Kabul

Kungiyoyi masu zaman kansu sun ce rashin matsugunan ya yi mummunan tasiri musamman kan mata da kananan yara.

"Muna samun rahotannin karuwar a bangaren bukatu na kiwon lafiya, da cin zarafin jinsi, da cin zarafi ta hanyar lalata da fataucin mutane,'' Jared Rowell, darakta a hukumar lura da Yan Gudun Hijira ta kasar Denmark (DRC) a Afghanistan ya shaida wa BBC.

"Auren wuri zai kasance wata babbar matsala saboda ana sayar da kananan 'yanmata don samun kudi wa iyalansu. Irin wadannan abubuwa, da a koda yaushe ke zama matsala za su kara muni.''

Kamar su abinci, da mastuguni da kayayakin kiwon lafiya, Mista Rowell y ace wadanda suka rasa matsugunan a Kabul na tsanannin bukatar kudi.

"Yana da matukar muhimmanci mutane sus amu kudi a hannu,'' ya ce.

"Hakan nan nufin hukumomi irin su DRC za su rarraba musu kudin da zai bai 'yancin cin gashin kan su wajen sayen abubuwan da suke bukata.

"Kudi na da na shi muhimmancin a daidai wannan lokacin, musamman ma da yake za su koma cikin babban birnin irin Kabul mai fama da tsadar kayan abinci.''

Shi kuwa Asadullah, babban fatansa yanzu shi ne watarana iyalansa su sake komawa rayuwarsu irin ta baya a garin su Kunduz.

"Muna son komawa mu cigaba da rayuwarmu a can,'' ya ce. ''Muna fatan watarana za a samu zaman lafiya a Afghanistan, kana kasarmu za ta samu 'yanci."