Wally Funk: Ƴar shekara 82 da ta cika burinta na zuwa ƙololuwar sararin samaniya

Asalin hoton, Reuters
Mace da kamar maza a fannin tuƙa jiragen sama Mary Wallace "Wally" Funk ta kafa tarihi a bangaren harkokin sararin samaniya, inda ta kasance mace mafi tsufa da ta zama 'yar sama jannati tana da shekera 82.
A ranar Talata 20 ga watan Yulin 2021 ne ta tafi ƙololuwar sararin samaniya tare da attajirin duniya Jeff Bezos, da ɗan uwansa da kuma Oliver Daemen mai shekara 18.
Ita dai Funk, wacce ta yi horo a matsayin mai tukin jirgin sama na ganin yin bulaguro zuwa sararin samaniya a jirgin Blue Origin na Bezos, wani sakamakon ayyukan da ta yi ne a rayuwarta - kana wani abu da ta shafe shekara 60 tana nema.
Mace ta farko da ta fara
"Lokacin da na fara tashi sama, na yi matukar son in gan ni a sararin samaniya,'' Funk ta shaida wa BBC shekaru biyu da suka gabata, game da burinta mara gushewa na tashi zuwa sama.

Asalin hoton, Getty Images
Ta kasance a ko da yaushe mai fara kafa tarihi - mai shekara 82 ɗin, ta riga ta kafa tarihi a sau da dama.
Funk ta kasance mace ta farko da ta zama mai bincike game da kariya a fannin tashin jiragen sama a Hukumar Kiyaye Hadurran Ababan Hawa ta Kasa (NTSB).
Kana mace ta farko da ta zama babbar jami'ar Hukumar Kula da Zirga-zirgar Jiragen Sama ta Tarayya (FAA) a Amurka.
Ta samu adadin sa'o'i 19,600 na tashi a matsayinta na mai tuƙin jirgin sama - kana ta horar da wasu mutum 3,000 tuƙin jirgin sama.
Kafin ta sake samun wani ci gaban, tawagar mutum hudun ta yi wani horo na kwanaki biyu gabanin tashinsu zuwa ƙololuwar sararin samaniyar ranar Talata.

Asalin hoton, Getty Images
Ba zai zama wani sabon abu ba ga Funk. A lokacin da ake kan gudanar da binciken sararin samaniya a shekarar 1960, mai shekaru 20 a lokacin, Funk ta yi horo matuka.
Ta kuma da yi gwaje-gwajen lafiya da na kuzari tare da sauran mata 12 - da aka fi sani da Mercury 13. Sun yi horo iri daya da na maza 'yan sama jannati a wancan lokacin.
"Kowane gwaji na da ban mamaki da sha'awa. Sun ɗaure ni a jikin wata kujera suka yi min allurar ruwan sanyi a kan ma'aunin 10C a kunne daya.
Za ka iya hayyacinka - ba za ka iya jurewa ba. Daga nan za su fitar da kai daga cikin dakin, kana bayan sa'a daya za su sake yi maka a daya kunnen.,'' ta tuna a tattaunawarta da BBC.
Dole sai ta sha ruwa mai ƙunshe da sinadari kana aka ajiye ta a cikin wani tanki da ba za ka iya jin komai ba, a nan ne ta aka bayar da rahoton cewa ta kafa tarihi ne nuna juriya.
Akasarin wadannan gwaje-gwajen masu tsanani ne don tabbatar da cewa za su iya jurewa yanayin sabon muhalli na sararin samaniya.
"Akwai kimanin maza 125, a cikin su bakwai ne suka iya jurewa. Cikin mata 25 kuma, 13 ne kacal suka kai labari,'' ta shaida wa BBC.
Ta bayyana abin da ya ƙarfafa mata gwuiwa har ta yi wadannan gwaje-gwajen da ake bukata yayin da take magana da mai yi mata tambayoyi daga Hukumar Bincike Sararin Samaniya ta Amurka NASA a shekarar 1999.
"Na gamu da matsaloli masu dangantaka da wasu daga cikin gwaje-gwajen. Na dauke shi a matsayin matakina na kai wa ga nasara.
"Zai sa in kai ga matakin kai wa kusa da sararin samaniya, kuma nan ne na keda burin zuwa.''

Rashin jin dadi sau da dama
Amma burin Funk na zama mace 'yar sama jannati ta farko ya gamu da cikas - a karon farko.
Lokacin da hukumar NASA ta yanke shawarar cewa matuka jirgin saman da suka yi gwajin tukin jiragen yaki masu tsananin gudu da kuma wadanda ke da takardar shaidar kamalla karatun digiri a fannin injiniya ne kawai za a dauka a bulaguron sararin samaniya.

Asalin hoton, Wally Funk via Blue Origin
A wannan lokacin ba a bari mata su zama matuka jiragen gwaji nayaki.
Duk da wariyar da ake nuna wa mata a fili - wani abu da aka gudanar da bincike a akai a zaman sauraron bahasi na gwamnai - Funk ba ta yanke ƙauna ba.
"Na sha rubuta wa hukumar NASA, amma sau hudu ana kin amincewa da bukatu na a lokuta daban-daban saboda ba yi karatun digiri a fannin injiniya ba, wanda ba zai taba yiwuwa ba,'' ta bayyana a hirar da aka yi da ita a shekarar 1999.
Amma kuma, yunƙurinta bai tafi haka nan ba.
''Na cika da farin ciki a lokacin da Sally Ride ta zama Ba Amurkiya ta farko da ta je sararin samaniya a shekarar 1983.
"Ta kira ni kana ta gode min kan yin wadannan gwaje-gwaje, saboda su ba su yi gwaje-gwajen da irin wahalwalun da muka yi ba,'' ta shaida wa BBC..
Hangen samun nasara
Funk ta ce ba ta ji dadin cewa ta kasa samun nasara daga hukumar NASA ba, amma kuma ba ta baƙin ciki. Ta ci gaba da jajircewa kan burin da take da shi.
A karshen shekarar 1900, ta sanar da aniyarta ta zama mai yawon bude ido ta farko zuwa sararin samaniya a Amurka. Bulaguron da aka yi niyyar yi a shekarar 2005 da bai faru ba.

Asalin hoton, Getty Images
A shekarar 2010, ta biya kimanin dala 200,000 na tikitin jirgin Virgin Galactic na kamfanin Richard Branson, wanda ya fara jigilar fasinjansa na farko a cikin wannan watan.
Funk ba ta cikin wannan jirgo, amma yanzu za ta yi tafiya a matsayinta na ''babbar bakuwa'' ta Bezos.
Kamar jirgin Virgin Galactic, jirgin rokar Blue Origin zai dauki fasinjoji zuwa sararin samaniya, wanda ke nufin fasinjojin za u tashi sama kama sa dawo kasa.
Ba za su zagaya saman duniya ba kamar yadda aka saba a jirgin 'yan sama jannati.
Bayan tashi sama daga wurin da akekaddamar da tashin a kusa da Van Horn, na jihar Texas, sabon jirgin rokar samfurin Shepard 4 dauke da fasinjojin zai kai nisan gudun kilomita 3, kan ko wace sa'a
Za a kai su zuwa nisan kilomita 100 zuwa saman duniyar Earth, zai kuma ba su samar yawo a sama - da jin rashin nauyi - har na tsawon mintuna hudu.
Jirgin zai kima sauko kasar duniyar Earth ta hanyar amfani a balam-balam din tashi, a tafiyar da ake sa ran za ta dau tsawom mintuna goma.

Asalin hoton, Blue Origin
Bayan rasa samun damar da ta yi a sau da yawa, da alamu daga karshe Funk za ta zama 'yar sama jannati.
Ana iya ganin Jeff Bezos na bayyana wa Funk tsare-tasren tashi saman a ani faifen bidiyo da ya yada, kana ya tambaye ta abinda za ta fada bayan ta sauka.
''Zan bayyana cewa,' Masoyi wannan shi ne abu mafi kyau da ya faru da ni,'' Funk ta bayar da amsa.
''Da wuya in jira. Ko kai wanene babu wani abu. Za ka iya yi muddin ka sa a ran ka kana son yi. Ina son yin abubuwan da babu wanda ya taba yi.'' ta ce.











