Elisa Loncón: Matar da ta samu ɗaukakar rubuta tsarin mulkin ƙasa bayan fama da talauci

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Daga Eva Ontiveros
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
- An wallafa
A shekarun 1970 lokacin da Elisa Loncón ke tasowa, sai ta yi tafiyar mil 8 kafin ta isa makaranta. Iyayenta 'yan asalin yankin Mapuche ne na kasar Chile, wadanda ke rayuwa cikin bakin talauci a wani kauye da ke kudancin yankin Araucanía.
Babu wanda ya ke taimakon kai ta makaranta, yawancin lokuta da kafa take takawa ta hanya mai cike da datti.
Mahaifiyarta aikatau ta ke yi a gidan masu kudi, sannan ta na kaunar wakoki. Mahaifin ta kuma kafinta ne, kuma shi ya koyawa kan shi yadda zai yi rubutu da karatu lokacin da ya ke da shekara 17.
Rayuwa ga wadannan iyali na cike da wahala da fadi tashi, dakyar iyayensu ke samawa Loncón da 'yan uwanta shida abincin da za su ci. Ko can a makaranta ma bakar wuya ta ke sha, saboda yadda ake cin zarafinta saboda tsatson da ta fito. Sai dai duk da hakan, ba ta karaya ba.
"Na fito daga iyalai masu saukin rayuwa, kamar sauran kabilar Mapuche muna shan bakar wuya," kamar yadda ta fada a kwanakin baya lokacin tattaunawa da jaridar El País ta kasar Sifaniya.
"Kabilar Mapuche 'yan asalin kasar Chile su na da yawan gaske, da kuma harshen da suke amfani da shi, su na da addini da tallafawa wajen bunkasar tattalin arzikin kasar.
"Sai dai kash, ba su da wani tabbacin 'yancin akan dukkan harkokin da suka shafi kasar. "Mu na mutuntawa da daraja kan mu, cikin abin da muka sa ni daga tarihinmu da al'adu".
Sannu a hankali ta bar kauyen da ake kira Lefweluan, inda yawancin dangin ta suke, ta kuma kallama karatu a matsayin malamar makaranta mai koyar da harshen Ingilishi.
Ta ci gaba da karatu har ta kai matakin digirin digirgir a jami'ar Leiden, da ke kasar Netherlands,ta kara yin wani digirin digirgir a fannin Adabi a jami'ar Pontifical Catholic da ke Chile, kafin daga bisani ta zama cikakkiyar Farfesa a jami'ar Santiago.
Baya ga aikin da ta ke na fannin ilimi, Loncón ta shiga yakin kwatarwa kabilar Mapuche 'yanci.
Ta yi suna matuka cikin masu fafutukar kare hakkin jama'arta, a farkon shekarar nan ne aka zabeta 'yar majalisa cikin kujeru 17 da aka warewa kabilu irin na ta a fannin duba kundin tsarin mulki, kuma su za su rubuta sabon kundin tsarin mulkin kasar Chile da ke fama da rarrabuwar kawuna.

Asalin hoton, EPA
Lamari ne mai cike da tarihi, saboda har kawo yanzu tsirarun kabilu ba su da katabus a sha'anin tafiyar da kasa, kuma Chile ba kasa ce da ba ta tafiya da sauran kananan kabilu.
'Yan asalin kasar mazauna daji ba a sanya su cikin kundin tsarin mulkin da ake amfani da shi a kasar ba, tun zamanin mulkin mulaka'un shugaba Augusto Pinochet, da ya yi mulki daga shekarar 1973 zuwa 1990.
A kokarin kawo sauyi, a wannan watan an zabe ta cikin mambobi 155 da za su shiga taron da za a yi da ya hada kabilun da aka maida saniyar ware, wanda shi ne karon farko da aka taba yi a tarihin Chile.
Cikin annashuwa da farin ciki, ta dunkule hanunta tare da daga shi sama, cikin dandazon masu tayata murna ta ce:
"Ina jinjinawa al'umar Chile, daga arewaci Patagonia, daga gabar ruwa zuwa tsaunuka, har tsuburai, da dukkan wadanda suke kallonmu a halin." Bayan nan sai ta daga tutar kabilar Mapuche.
Ta ci gaba da cewa "Ina mika sakon godiya ga wadanda suka bani goyon baya daga sassa daban-daban, ina son shaida musu yarda da amincewar da suka yi da ni, da kokarin tabbatar da mafarkin kabilar Mapuche, kuma ku ka zabi mace ta farko da ta fito daga wannan yankin, wannan abu ne da zai sauya tarihin kasarmu."

Su wanene kabilar Mapuche?
- Kafin zuwa Sifaniyawa a karni na 16, kabilar Mapuche sun mamaye kudancin kasar Chile
- Sun yi fice a fannin dawa, kuma sun yi kokarin tsayawa da kafarsu lokacin mamayar karni na 19, amma daga bisani aka ci karfinsu, tare da maida su sanaiyar ware a wani dan kebantaccen yanki
- An saida wa manyan kamfanoni gonakinsu
- Kusan kashi 12 cikin 100 na al'ummar Chile na kiran kansu 'yan asalim Mapuche.

Babban taron da za a yi na sauya fasalin kundin tsarin mulkin, wanda ya kunshi mabobi maza da tsirarun mata kuma shi ne irinsa na farko a duniya, an cika shi da mutanen da ba su fito daga gwamnati ba.
Wannan ya sanya ake da kyakkyawan fatan, za a samu nasarar sauyin da aka dade ana korafin ya kamata ayi tun shekarar 2019, lokacin da kasar ta fuskanci mummunar zanga-zanga.
Cikin bukatun da kabilar Mapuche da sauran kabilu tara na kasar suka mika shi ne samar musu da jiha, wanda hakan zai sanya aji muryarsu da karba musu 'yanci, da amincewa da al'adunsu da kuma harsunansu.
Ita kan ta Loncón, ta sha rubuta littattafai da ke koyar da harshen Mapuche wato mapudungun.
Har wa yau, al'ummomin na son a karbo musu gonakin da aka kwace musu tun zamanin iyaye da kakanni, wanda hakan ke janyo rashin jituwa tsakaninsu da sauran kabilu.
Loncón ta shaidawa jaridar La Tercera ta kasar cewa: "Za mu amince ayi sasanci, don haka su daina tsoron mu.
Ta yi kalaman ne gabannin gabannin zabarta, ta kara da cewa " Ana yi wa al'ummar Mapuche rashin adalci, wannan kira ne na ba su 'yancinsu, a kuma karbe mu a yadda muke a yi mu'amala da mu cikin gaskiya da adalci."

Asalin hoton, Getty Images










