Zaɓen Amurka 2020 kawo yanzu ya laƙume dala biliyan 14

Trump supporters in Madison, Wisconsin, on November 7, 2020

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Magoya bayan Mista Trump a jihar Wisconsin yayin da suke dakon sakamakon zabe
An wallafa

Zaben shekarar 2020 ya kafa tarihi bayan da alkaluman kudaden da aka kashe suka bayyana yadda ya sha gaban dukkan zabukan da aka taba yi a tarihin Amurka, wanda kawo yanzu zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dattawa da na wakilai sun lakume kimanin dala biliyan 14.

Adadin na bana ya nunka kudaden da aka kashe yayin yakin neman zaben da aka yi shekara hudu da ta gabata.

Wata cibiya mai suna Center for Responsive Politics da ke sa ido kan yadda ake gudanar da siyasa a kasar ce ta bayyana haka a wani rahoton da ta fitar.

Ko shakka babu, babban dalilin kashe wadannan makudan kudaden shi ne zaben shugaban kasa - wanda ba abin mamaki ba ne ganin yadda aka samar da kudade ga yakin neman zaben Joe Biden domin ya sami damar kayar da Donald Trump.

Takarar da Mista Biden yayi da Shugaba Trump da kudaden da suka kashe yayin yakin neman zabensu zai zarce dala biliyan 6.6. Wannan ya zarce adadin dukkan abin da aka kashe a dukkan yakin neman zaben na 'yan majalisa da na shugaban kasa a 2016.

Biden and Trump with White House in between them

Daga ina kudaden suka fito?

Yawancin kudaden da aka kashe a yakin neman zabe ba daga aljihun 'yan takarar suka fito ba.

Akwai masu bayar da gudunmawa manya da kanana da suka rika taimaka wa 'yan takara da kudade.

Akwai kuma wasu attajirai masu sha'awar kafa gwamnatin da za ta zame musu inuwa idan ta lashe zabe da suka mika wa 'yan takarar daruruwan miliyoyin dalar Amurka.

Shin me ake yi da kudaden?

Abu na farko da ke lakume kudade yayin da ake yakin neman zabe shi ne tallace-tallacen talabijin: A bana kawai an kashe dala biliyan 1.8 na tallace-tallacen 'yan takarar shugaban kasa, kamar yadda kamfanin Advertising Analytics mai kula da yadda ake talla a kafofin yada labarai ya wallafa cikin wani rahotonsa.

Ofishin yakin neman zaben Mista Biden kawai ya tara dala miliyan 938 zuwa 14 ga watan Oktoba, kuma idan aka hada dukkan kudaden da jam'iyyun siyasa ke ba 'yan takarar biyu, za a taras an kashe kusan dala biliyan biyu a tallata 'yan takarar mukamin shugaban kasa kawai.

Zabukan shiga majalisar Amurka

Ba a zaben shugaban kasa kawai ake facaka da dala ba, domin yayin yakin neman zaben shiga majalisar Amurka a bana, 'yan takarar mukaman majalisar wakilai da na dattawa sun kashe daruruwan miliyoyin daloli.

A North Carolina kawai 'yan takarar mukamin sanata biyu - Thom Tillis na jam'iyyar Republican da Cal Cunningham na jam'iyyar Democrat sun kashe dala miliyan 272.

Wannan daya ne cikin yakin neman zabe hudu da suka kashe fiye da dala miliyan 200 - inda sauran na jihohin North Carolina da Iowa da South Caroina da kuma Arizona.

'Yan takara daga jam'iyyar Democrat sun kashe jimillar dala biliyan 5.5 a bana, su kuwa 'yan Republican sun kashe dala bliliyan 3.8.

Ban da masu karamin karfi da su ka bayar da gudunmawar kashi 22 cikin 100 na dukkan kudadn da aka tara, akwai manyan attajirai kamar Sheldon Adelson mai gidajen caca da matarsa Miriam Adelson da ke kan gaba wajen tarwa 'yan Republican kudade, wanda a bana sun mika mu su dala miliyan 183.

Graphic showing Capitol and White House with price tag

A bangaren 'yan Democrat ma akwai attajirai kamar Mike Bloomberg wanda shi daya tilo ya ba 'yan takara daban-daban dala miliyan 107.

Akwai kuma wasu masu zurfin aljihun kamar shugabannin kamfanonin fasahar sadarwa na zamani da ke Silicon Valley, wato wurin da kamfanoni kamar Facebook da Google ke tafiyar da harkokinsu.

Su ma sun taka rawa wajen samar da makudan kudaden ga ofisoshin yakin neman zaben manyan jam'iyyun Amurka biyu.

Akwai Karla Jurvetson wadda attajirar likita ce kuma tsohuwar matar wani mai zuba jari a harkokin fasahar sadarwa da ta bayar da dala miliyan 24, wanda yawancin kudaden ta ba Sanata Elizabeth Warren ce wadda 'yar takarar mukamin shugaban kasa ce a bana.

Akwai kuma Dustin Moskovitz, daya daga cikin wadanda suka kafa Facebook. Shi ma ya mika dala miliyan 24 ga wata kungiya mai suna Future Forward mai adawa da manufofi da siyasar Shugab Trump, kuma sun fitar da tallace-tallace masu yawa domin illata shugaban na Amurka.

President-elect Joe Biden attends a virtual meeting with frontline healthcare workers in Wilmington, Delaware on November 18, 2020

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Ranar 20 ga watan Janairu za a rantsar da Joe Biden a matsayin shugaban Amurka na 46

Inda aka dosa daga nan

Amma inda 'yan takarar suka fi samun kudade masu tsoka da gwami shi ne daga kasuwar hada-hadar hannayen jari wadanda aka fi saninsu kasuwar da sunan Wall Street.

Daga Wall Street kawai 'yan takara daga jam'iyyu daban-daban sun tara fiye da dala miliya 255, wanda mafi yawan kudin - dala miliyan 161.7 'yan jam'iyyar Democrat ne suka amfana da su.

Su kuma 'yan jam'iyyar Republican sun samo dala miliyan 94.5 domin gudanar da yakin neman zabe a wannan zaben na 2020.

Dala biliyan 14 da kawo yanzu kamfanin Advertising Analytics ya bayyana shi ne yawan kudin da aka kashe a dukkan yakin neman zaben na bana, ko kusa ba zai zama adadin karshe ba.

Akwai wasu zabukan cike gurbin 'yan majalisar dattawa biyu a jihar Georgia da kawo yanzu jam'iyyun siyasa ke ta kai komo a kai. Ana hasashen za su kashe daruruwan miliyoyin dalar Amurka - saboda duk wanda ya lashe wadannan kujerun biyu, shi ne zai yi iko da majalisar wakilan kasar na shekara hudu mai zuwa.

Akwai kuma kidayar kuri'un da har yanzu ake yi, musamman a jihar Michigan da Pennsylvania, inda ofishin yakin neman zaben Mista Trump ke kashe miliyoyin daloli domin a sake kirga kuri'un da ake takaddama a kansu, baya ga miliyoyin alolin da lauyoyin da ke shigar da kara da masu yi wa shugaban na Amurka hidima a jihohin da yake kalubalantar kayen da ya sha.