Zaɓen Amurka na 2020: Yadda takarar Kamala Harris ta fito da ƙalubalen da mata 'yan siyasa ke fuskanta

Kamala Harris

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Babu yadda za a kauce wa tattauna batutuwan da suka shafi mata a zaben Amurka na bana, ganin cewa Sanata Kamala Harris ta kafa tarihin zama 'yar takarar maiamakin shugaban kasar - abin tambaya kawai shi ne, shin akwai bambanci kan yadda ya kamata a tunkari batun mata a wannan lokaci?

Bari mu duba yadda tsayar da ita takara ya fito da batutuwan da mata suka kwashe shekara da shekaru suna fuskanta a siyasa - da kuma yadda abubuwa ke sauyawa - tare da mai sharhi Debbie Walsh, darakta a Cibiyar Nazari kan mata Amurkawa da Siyasa a Jami'ar Rutgers.

Yadda ake kauce wa yin fushi

Dole matana da suka tsunduma cikin harkokin siyasa su bambance tsakanin tsayawa tsayin daka da kuma nuna fushi. Bincike ya nuna cewa irin dabi'ar da mata ke nunawa za ta iya sa wa a rika kallonsu a matsayin kamun kai yayin da a lokaci guda za a kalli maza a matsayin masu nuna kwarin gwiwa.

Bugu da kari, matana da suka fito daga tsirarun kabilu suna fuskantar wariyar launin fata. Kuma a Amurka, an dade ana amfani da kalaman "bakar mace mai yawan fushi" . Wadannan kalamai, wadanda aka soma amfani da su a karni na 19, suna nuna bakar mace a matsayin maras hankali, wacce ba ta da halyya irin ta mata.

Kamar yadda Ms Walsh ta bayyana: "Ana zargin mata da kasancewa marasa karfi sosai wajen zama shugaba ko mataimakin shugaban Amurka, a lokaci guda kuma, ta yaya za ka nuna karfinka ba tare da nuna kanka a matsayin mai cike da fushi ba ?"

Tana ganin Ms Harris ta yi daidai kan abin da ta yi lokacin muhawarar 'yan takarar mataimakin shugaban kasa, amma ta kara da cewa akwai wasu lokuta da ta yi baya-baya - ko da yake yadda ta rika mayar da martani cikin da'a ba tare da ta rika katse abokin hamayyarta ba ya yi "matukar kyawu" kuma ta yi abin da ya yi wa mata dadi musamman wadanda ake rainawa.

Za ta iya jagoranci?

Wasu masu sharhi sun bayyana cewa mata sun taka rawar gani fiye da maza a wajen yakin neman zaɓe, ko da yake masu zaɓe babu ruwansu da jinsi dan takara. Galibi ba a tantama kan ƙwarewar namiji amma dole ne mace ta nuna cewa za ta iya abin da take son yi.

Kuri'ar jin ra'ayin jama'a da Economist/YouGov suka gudanar a watan Agusta ta nuna cewa mataimakin shugaban kasa mai-ci ya dan yi tazara kan Ms Harris. Kashi daya bisa hudu na Amurkawa sun ce ba su da wani ra'ayi takamaimai kan Ms Harris, yayin da kashi 14 suka ce ba da ra'ayi kan Mr Pence.

Bayan muhawarar da suka yi, akasarin masu kaɗa ƙuri'a na ganin cewa Harris ce ta yi nasara. Sai dai da aka tambaye su kan ko wane ne ya kamata ya zama shugaban kasa, ƙuri'ar ta sha bamban.

Kuri'ar jin ra'ayin jama'a da YouGov ta yi ta nuna cewa akasarin Amurkawa - kashi 56 - na ganin Mr Pence zai fi dacewa ya zama shugaban kasa idan Mr Trump ba zai iya shugabanci ba, yayin da kashi 50 ne ke ganin hakan a kan Ms Harris. A tsakanin masu kada kuri'a da ke da zaman kansu, kashi 53 sun bayyana kwarin gwiwa kan kwarewar Mr Pence, yayin da kashi 44 suka nuna hakan a kan Ms Harris.

Wannan layi ne

Sunan da ake kira na da shi a gida

Lokacin da ta amince da tsayar da ita a matsayin 'yar takarar mataimakiyar shugaban Amurka a jam'iyyar Democrat, Ms Harris ta ce mukamin mataimakin shugaban kasa babban abu ne amma mukamin "matar mahaifi" ya fi muhimmanci.

A yayin da ake gabatar da ita ga Amurkawa, sau da dama Ms Harris tana bayani kan iyalinta (tana da 'ya'yan mijinta da take riko) da kuma martabarta. Yadda ta girma a hannu a hannun mahaifiyarta ba tare da mahaifinta ba da kuma yadda take a matsayin ruwa-biyu shi ne abin da Ms Harris take gabatarwa a matsayinta na 'yar takara.

Ms Walsh ta kara da cewa nuna iyali ya zama wani abu muhimmi ga maza da ke takara. A baya bayan nan ne kawai mata 'yan siyasa suka soma bayyana fafutukar da suka yi a rayuwa a matsayin abin da ya kamata a lura da shi wajen zabensu.

A gefe guda, idan namiji ya yi magana a kan iyalinsa, hakan na taimaka wa wajen nuna shi a matsayin "mutum mai iyali", amma "babu wanda ke tantama kan kan fafutukar da ya yi da kuma abubuwan da ya fi bai wa fifiko", ko kuma mayar da hankali kan mutumin da ke kula da 'ya'yansa.

Idan muka yi waiwaye za mu ga yadda batun iyali ya yi tasiri lokacin da Sarah Palin ta tsaya takarar mataimakiyar shuggaban kasa a 2008.

A lokacin tana gwamna a jiar Alaska amma kafafen watsa labarai da wasu 'yan jam'iyyar Democrat sun rika binciken kwakwaf a kanta. A lokacin, Mrs Palin tana da 'ya'ya biyar, ciki har da jaririn da ke fama da cutar gilu.

Wasu sun rika cewa tana so ta yi watsi da dawainiyar iyalanta domin tsayawa takara.

Sarah Palin

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, 'Yar takarar mataimakiyar shugaban kasa ta jam'iyyar Republican Sarah Palin a 2008

Sai dai ana samun sauyi kan irin wannan kallo - ko da yake ba zai yiwu a daina yi wa mata 'yan siyasa tambayoyi kan dawainiyar iyalinsu ba.

A baya-bayan nan a zaman sauraren ba'asi kan matar da aka naɗa a muƙamin alƙalin Kotun Ƙoli, Amy Coney Barrett, 'yan jam'iyyar Republican sun nuna cewa matsayinta na mai 'ya'ya bakwai zai ba ta damar yin aikin alƙalanci fiye da wasu.

Sarah Palin in 2008

Asalin hoton, Getty Images

Waɗanne irin kalamai maza suka yi a kanta?

Mr Trump ya bayyana Ms Harris a matsayin mai kawo sauyi, maras ɗa'a, kuma muguwa tun ranar da ta zama mataimakiyar Mr Biden.

Abokin hamayyarta Mr Pence bai sha zagi ba, amma mun ga yadda rawar da ya taka a muhawarar da suka yi.

Katse hanzari na cikin abubuwan da ake yi yayin muhawara. Amma Ms Walsh ta ce Mr Pence zai iya yin amfani da wata dabara da za ta nuna cewa shi na daban ne.

"Ya yi amfani da ita ta hanyar da ya share ta cikin dabara," in ji ta. "Idan mace ce ta yi haka, wato ta ci gaba da magana, za a yi ta maganganu a kan cewa ba ta rufe bakin ta."

Yaya abubuwa suke sauyawa?

Ms Walsh ta ce tun 2018, lokacin da aka samu karin matan da ke takara a harkokin siyasa, matan sun soma sabawa da fadin abin da suka ga dama ba tare da yin shayi ba.

"Ba sa zurfafa tunanin kan 'yaya ya kamata na yi' sai dai kawai suna yin abin da suka ga y fi dacewa," a cewarta. "Mun ga yadda a shekarar 2018 inda 'yan takara da dama ke tattaunawa batutuwan da a baya mata sun gwammace kada su ce uffan a kan."

Batutuwan sun hada da yin magana a kan ƙananan yara, da rashin samun matsuguni, ko kuma tattaunawa a kan matsaloln rashin kudu da mutum ke fama da su.

A shekarar 2017, tsohuwar Sakatariyar Wajen Amurka Condoleezza Rice, ta yi kira ga mata da kada su bari "matsalolin kalaman nuna wariyar launin fata na wani su zama nasu".

Condoleezza Rice

Asalin hoton, Getty Images

"Wannan shi ne abin da muke fada a kan mata: Idan ka shiga daki, idan wani ya yi tunanin wulakanta, kar ka yarda da hakan. Ka yi masa raddi," a cewarta a wajen taron KPMG kan shugabanci.

"Idan aka hana ka samun abin da kake ganin ka cancanta ka samu, akwai abin da zai biyo bayan haka - kuma ya kamata ta tunkare shi."

Ms Walsh ta ce daga Geraldine Ferraro zuwa Sarah Palin da Hillary Clinton, dukkansu 'yan takara ne da suka yi waiwaye kan abubuwan da suka faru a baya.

Kuma yanzu da aka samu 'yar takarar mataimakin shugaban kasa bakar fata 'yar asalin Indiya, "an samu gagarumin sauyi a duniya", in ji ta.