Kamala Harris da Mike Pence: Abin da ya sa muhawarar ƴan takarar mataimakan shugaban Amurka ke da muhimmanci

Asalin hoton, Getty Images
Lokaci ya yi da masu takarar mataimakan shugaban ƙasar Amurka za su hau kan dandalin muhawara su ma. Za su baje-kolin nasu ra'ayoyin.
Zaƙuwar da ake nuna wa kan son ganin yadda za ta kaya ta sa muhawar za ta zama irin wacce ba a taɓa yi ba tsakanin ƴan takarar mataimakin shugaban ƙasa.
Wasu na kiran ta mafi muhimmanci a tarihin ƙasar, saboda tana zuwa ne a lokacin da shugaban Amurka ke jinyar cutar korona, ƙwayar cutar da ta kashe Amurkawa 200,000 ta kuma kama miliyoyi. Sannan ga rikicin da ya dabaibaye Kotun Ƙolin ƙasar, da rikicin nuna wariyar launin fata da dai sauran su.
Tsaya. Su waye za su yi muhawarar?
A gefe guda akwai Kamala Harris, matar da ke son zama mataimakiyar shugaban Amurka a karon farko a tarihi.
Kamala, mai shekara 55, wadda ƴar majalisar dattawa ce, kuma tana daga cikin masu uzurawa gwamnati daga jam'iyyar adawa a majalisar, sannan tsohuwar lauya ce.
A ganinta tana yi wa wani nutsattesen mutum maiataimaki ne wanda bai fiya yin kuskure ba a gaban 'yan jarida yayin da suka sa shi a gaba. Kazalika, ba kare kansa kawai yake yi ba. Zai yi ta ƙoƙarin samun ta inda zai jefa magana, kamar yadda ya taɓa yi a baya.
Mr Pence mai shekara 61 yana da taushin zance kuma mai addini ne, kirista ne daga jihar Indiana. Duk da bambance-bambancensu, Mike Pence wani ginshiƙi ne ga uban gidansa tswon shekara huɗu, kuma kansu a haɗe yake kan kowane irin batu da ya taso ko ce-ce-ku-ce.
Su wane ne suka zaƙu da muhawarar?
Muhawarar ƴan takarar shugaban ƙasa ba su cika zama matsala ba a tarihin shugaban ƙasa, amma a wannan shekarar abin zai mutane za su mayar da hankali kan yadda mataimakan biyu za su fafata a junansu.
Ganin cewa Trump ya sha fama da cuta, hakan na tuna wa masu kaɗa ƙuri'a cewa za su zaɓi 'yan takara masu yawan shekaru.
Muhawarar farko tsakanin Trump da Biden ba a bayyana wasu cikakkun tsare-tsaren gwamnati ba, kamar yadda wasu suka riƙa fatan ji daga kowanne ɗan takara game da ƙasarsu.
Kuma ma za ta iya zama muhawara ta ƙarshe, ya dogara kan yadda jikin Trump ya kasance.
Cibiyar Brookings ta kira wannan muhawara mafi muhimmanci ta 'yan takarar mataimaka shugaban ƙasa.
Yaushe ne kuma a ina zan iya kallon muhawarar?
Ranar Laraba ce da ƙarfe 9:00 zuwa 10:00 na safiya agogon Amurka (ƙarfe 2:00 zuwa 3:00 na rana agogon Najeriya) kuma ita ce fafatawa ɗaya tilo tsakanin 'yan takarar.
Sashen Ingilishi na BBC zai riƙa kawo sharhi kai-tsaye game da hirar a shafinsa na intanet sannan kuma a haska a talabijin kai-tsaye daga birnin Salt Lake na Jihar Utah.
Muhawara biyu ta gaba su ne:
- Ranar 15 ga Oktoba a Miami, Florida
- Ranar 22 ga Oktoba a Nashville, Tennessee
Ko rashin lafiyar Trump ta kawo wani sauyi?
Masu shirya muhawarar na sane cewa Trump zai iya shafa wa Biden da kuma mai shiga tsakani a muhawarar, Chris Wallace, cutar korona. Saboda haka ba za su so haka ta faru ba.
Hukumar shirya muhawarar 'yan takarar shugaban ƙasa ta amince a bayar da tazarar ƙafa Kamala 12 tsakanin Kamala Harris da Mike Pence - a baya, nisan ƙafa bakwai ne kawai - yayin muhawarar.
Kazalika, za a saka gilashi a gaban kowanne ɗan takara domin kare kamuwa da cutar. Sannan mutum ƙasa da 200 ne kaɗai za su kasance a Kingsbury Hall, wanda ke cikin Jami'ar Utah.
Sai dai wani na kusa da Mike Pence ya shaida wa CBS News cewa mataimakin shugaban ƙasar ba ya son a saka gilashin.
Ko za a samu hatsaniya kamar na farko?
Da wuya hakan ta faru, Mike da Kamala na da tsauri amma kuma suna da wayewa, saboda haka abu ne mawuyaci ya zama kamar na Trump da Biden.
A 2016, an yabi Pence game da yadda ya cinye abokin takararsa na Democrat, Tim Kaine, da kuma yadda ya riƙa kare Trump.
Ita kuwa Kamala Harris a matsayinta na lauya, kodayaushe a nutse take. Ta yi kaca-kaca da Biden a lokacin da suke muhawarar neman tikitin jam'iyyar Democrat.











