Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kutse a Twitter: Me ya jawo kuma me ya sa za a damu?
- Marubuci, Daga Joe Tidy
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakili kan harkokin Intanet
- An wallafa
Ana ci gaba da dasa ayar tambaya kan kutsen da aka yi a shafukan Twitter na wasu manyan mutane a ranar Laraba - sai dai abu ɗaya da za a yarda da shi, shi ne wannan kutsen shi ne mafi muni.
An damfari dubban mutane bayan an yi kutse ga shafukan manyan mutane inda aka buƙaci mutane su aika gudunmawar dala dubu ɗaya na kuɗin bitcoin, da fatan samun ninkin kuɗinsu.
Masu kutsen sun tura saƙonni akalla ga mutum miliyan 350 masu amfani da shafukan Twitter.
Sai dai da alama sun samu kuɗi kimanin dalar Amurka 110,000 cikin sa'o'i ƙadan da suka yi damfarar.
Gagarumin jan hankali
Wannan wani hari ne kan sirri da tsaro.
Masana na ganin cewa masu kutsen sun yi ɓarna fiye da yadda ake tunani.
Twitter na da masu amfani da shafin sosai a Amurka da Japan da Rasha da kuma Birtaniya.
Tambayoyi masu amfani
Twitter wata kafa ce da wasu manyan mutane kuma sanannu a duniya suka zaɓi amfani da ita.
Abubuwan da suke wallafawa na taimakawa wajen motsin kasuwannin kuɗi da kuma jawo wani juyi na siyasa.
Ganin cewa akwai zaɓen shugaban ƙasar Amurka ƙasa da watanni huɗu masu zuwa, akwai tambayoyi da ya kamata a yi kan ko za a iya dogara da shafin a lokacin zaɓen.
Ba a yi kutse kan shafin Shugaban ƙasar Donald Trump ba.
'Shafukan da aka fi hari'
Sai dai da dama na jira su gani kan ko abokin karawarsa Joe Biden zai ce wani abu a Twitter bayan afkuwar wannan lamarin.
"Mun san cewa Rasha na ƙoƙarin tsoma kanta kan harkar zaɓen 2020 kamar yadda ta yi a 2016," in ji Dakta Heather Williams daga Jami'ar King's College ta Ingila.
"Rikirkita shafukan sada zumunta ba ƙaramin aikinsu bane.
"Wannan kutsen da aka yi ya nuna yadda babu tsaro a tattare da shafukan sada zumunta da kuma yadda Amurkawa ba wuya an ci galba kan su ta fannin labaran ƙarya."
'Mafi muni a tarihi'
Tasirin da wannan kutsen ya yi na ƙara faɗaɗa ba wai Twitter kaɗai ba, amma ga dukan shafukan sada zumunta.
Abin da aka fi gani shi ne masu kutsen sun samu damar kutse cikin shafin manyan mutanen, wanda hakan ya ba su damar samun kalmar sirri ko kuma password na shafin.
Shafin Twitter ya tabbatar da wani jerin saƙon da ya wallafa inda ya ce: "Mun gano abin da muke tunani kamar haɗin gwiwa ne daga wasu mutane domin kai hari ga ma'aikatanmu ta hanyar samun damar yi musu kutse ga kayan aikinsu."
Rashin gaskiya
Masu kutsen sun yi amfani da wata hanya ta gano kalmar sirri ta shafinsu da kuma bin manyan mutanen ta adreshinsu na email domin damfarar su don su samu bayanai daga wurinsu.
Ko kuma zai yi wu waɗanda suka yi kutsen sun haɗa baki da wasu ma'aikatan kamfanin domin basu bayanai su kuma su biya su.
Kamfanin Twitter zai fuskanci matsin lamba matuƙa a halin yanzu.
"Wannan kutsen ya shafi mutuncin kamfanin Twitter," in ji shugaban ɓangaren intanet na ƙungiyar tattalin arziƙi ta duniya wato Willian Dixon.
"Wannan ya kasance wani babban kutse ga masu amfani da shafin Twitter"
"Mafi girma a tarihin duniya"
Karin labarai masu alaka
'Bayanai masu muhimmanci'
Kamfanin na Twitter bai amsa tambayoyin 'yan jarida ba, sai dai ya ce yana ɗaukar matakai na taƙaita masu samun damar ganin sirrin bayanai na kamfanin, wato ma'aikata.
Kamfanin ya ce yana kuma ƙoƙarin dubawa kan ko akwai wani laifi daban da masu kutsen suka yi ƙoƙarin tafkawa ya yin kutsen.
Shugaban kamfanin ya ce akwai yiwuwar cewa masu kutsen sun ɗora hannunsu kan wasu bayanai na sirri da bai kamata su samu ba.
"Akwai yiwuwar sun kutsa cikin saƙonnin mutane na ɗan wani lokaci," in ji Mathew Hodgson.
Zancen cewa Twitter na da damar kwace shafukan mutane duk da tsaron da shafukan suke da su zai iya razana wasu mutane.
Sai dai masana sun ce hakan na cikin tsarin irin waɗannan kamfanonin.
An yi ƙoƙarin jin ta bakin Facebook da Snapchat da Instagram da Youtube kan matakan da za su ɗauka, sai dai babu wanda ya bayar da amsa.