Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
George Floyd: Twitter ya daina amfani da wasu kalmomi
Kamfanin sada zumunta na Twitter zai daina amfani da kalmomi irin su 'master' wato "ubangida", 'slave', wato "bawa" da kuma "blacklist" wanda ke nufin 'haramci' da zummar kyautata kalamansa yayin sadarwa.
Ana yawaita yin amfani da kalmomin wajen sarrafa tsarin shafukan sada zumunta tun da aka kirkiri kamfanonin shekaru da dama da suka wuce.
Shi ma bankin Amurka JPMorgan ya dauki irin wannan mataki a yayin da kamfanoni da dama suke kokarin daina nuna wariyar launin fata sakamakon kisan dawasu 'yan sanda farar-fata suka yi wa wani akar-fata mai suna George Floyd a birnin Minneapolis.
Masana sun ce za a yi asarar miliyoyin dala wajen maye gurbin wadannan kalmomi kuma matakin zai dauki watanni da dama kafin a kammala shi.
A tsarin intanet, "ubangida" na nufin babban makunni da ke sarrafa "bayi," ko kuma yake samar da irin su da dama. "Blacklist" na nufin abubuwan da aka haramta ba su wata dama, mana'a shafukan intanet da aka haramta.
Ranar Alhamis, sashen injiniyanci na kamfanin Twitter ya wallafa jerin sakonni da yake so "ya kawar domin ya maye gurbinsu da kalamai masu armashi". Kalaman sun hada da "jadawalin farar-fata" wanda za a maye gubinsa da "jadawabin da za a bari" da kuma "ubangida/bawa" wanda za a maye gurbinsa da "shugaban/mabiyi".
A watan jiya, mutumin da ya kafa kamfanin Twitter Jack Dorsey ya bayar da gudunmawar $3m ga shirin Know Your Rights Camp na tsohon dan wasan Colin Kaepernick domin "fafutukar neman 'yanci da zaman lafiya" ga al'umomi marasa rinjaye.
Kamfanin JPMorgan ya ce yaa duba yiwuwar soke amfani da tsofaffin kalmomi na intanet a yayin da ake ci gaba da fafutukar kamfe na kare 'yancin bakar-fata Black Lives Matter a duniya. Ya ce kalmomin sun fito a wasu tsare-tsaren fasahar sadarwarsa.