Yadda wasannin Premier mako na 16 suka gudana

Muna kawo maku rahotanni da sharhi kan wasannin Premier League kai-tsaye yayin da suke faruwa.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Buhari Muhammad Fagge

  1. An tashi daga wasa, Tottenham 5-0 Burnley

  2. An kara minti '4, Watford 0-0 Crystal Palace

  3. An kara minti '3, Tottenham 5-0 Burnley

  4. Liverpool ta yi canjn karshe, Bournemouth 0-3 Liverpool

    An cire Alex Oxlade-Chamberlain an sako Xherdan Shaqiri.

  5. Katin gargadi, Watford 0-0 Crystal Palace

    An bai wa Kiko Femenia katin gargadi bayan doke Zaha da ya yi.

  6. Ismaila Sarr, Watford 0-0 Crystal Palace

    Ismaila Sarr yana kokari, amma ya tada hankalinsa a wasan.

  7. Mohamed Salah, Bournemouth 0-3 Liverpool

    Mo Salah

    Asalin hoton, Getty Images

    Mohamed Salah ya ci kwallo 63 a wasa 100 na Premier.

    'Yan wasa uku ne kacal suka fi dan kasar Masar din zira kwallaye a wasansu 100 na farko - Alan Shearer (79), Ruud van Nistelrooy (68) da kuma Sergio Aguero (64).

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  8. Watford na neman Finareti, Watford 0-0 Crystal Palace

    bayan wani mummunan hari da Watford ta kai, yanzu tana neman bugun daga kai sai mai tsaron gida.

  9. Zaha, Watford 0-0 Crystal Palace

    Zaha ba ya komi a wannan wasa, sai dai kuma dan wasa ne da cire shi ka iya zama koma baya ga Palace.

  10. Liverpool ta yi canji, Bournemouth 0-3 Liverpool

    Andy Robertson ya fita, Curtis Jones ya shigo kuma wannan ne wasan farko na matashin dan wasan.

  11. GOAL '74, Tottenham 5-0 Burnley

    Sissoko ya ci ta biyar.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  12. Burnley ta yi canji, Bournemouth 0-3 Liverpool

    Aaron Lennon tsohon dan wasan Tottenham ya shigo ya maye gurbin Robbie Brady.

  13. Watford 0-0 Crystal Palace, Watford 0-0 Crystal Palace

    Hankali ya dawo kan wannan wasan domin ganin wainar da ake toyawa.

    Sauran wasannin biyu a iya cewa an kammala su.

  14. , Tottenham 5-0 Burnley

    Chris Wood ya fita, Matej Vydra ya shigo - wasansa na farko kenan cikin sama da wata guda.

  15. Bournemouth ta ci kwallon satar gida, Bournemouth 0-3 Liverpool

  16. Bournemouth ta yi canji, Bournemouth 0-3 Liverpool

    Callum Wilson ya fita Dan Gosling ya maye gurbinsa.

  17. GOAL '54, Bournemouth 0-3 Liverpool

    Salah ya jefa ta shi. Da ma ya kwana biyu ba a ji duriyarsa ba.

    Kwallo ta bakwai kenan da ya ci a bana a Premier.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  18. Kaaaaaane GOAL '53, Tottenham 4-0 Burnley

    Wannan kafar damar ta Harry Kane azaba ce! Ya kara ta biyu!

    Ko Kane zai iya cin kwallo uku a yau?

    Da ma a baya ya taba cin Burnley uku shi kadai.

    Kwallo ta tara kenan da Kane ya ci a Premier ta bana.

    Sau 14 ya taba cin kwallo uku rigis a wasa daya tun sanda ya fara buga tamaula a matsayin kwararre.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  19. Liverpool na neman ta uku, Bournemouth 0-2 Liverpool

    Liverpool ta matsu ta kara ta uku yayin da Salah ya bai wa Keita kwallo, wanda shi kuma ya yi kokarin neman Alexander-Arnold amma dan wasan bayan bai iya buga kwallon ba.

  20. , Watford 0-0 Crystal Palace

    Riedewald ya canji Jeffrey Schlupp

    Da alama tsoorn jin rauni ne ya sa aka maye gurbin dan wasan.