Yadda wasannin Premier mako na 16 suka gudana

Muna kawo maku rahotanni da sharhi kan wasannin Premier League kai-tsaye yayin da suke faruwa.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Buhari Muhammad Fagge

  1. GOAL '85, Man City 1-2 Man Utd

    Otamendi ne ya zare kwallo daya.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  2. Katin gargadi, Man City 0-2 Man United

    An bai wa De Bruyne katin gargadi.

  3. United ta yi canji, Man City 0-2 Man Utd

    Pereira ya maye gurbin Martial. Kuma daga shigowarsa har an bashi katin gargadi, ya yi wa Sterling keta.

  4. Magoya baya na jifa, Man City 0-2 Man Utd

    Magoya bayan City sun hana a dakko kwana sun sa jifa.

  5. Lingard, Man City 0-2 Man United

    Ya kai hari na-ci amma Ederson ya bige ta zuwa bugun kwana.

  6. Man United ba ta taba rashin nasara ba cikin wasa 170 da ta buga a Premier in dai ta ci kwallo 2 ko sama kafin a tafi hutun rabin lokaci (ta ci 167 ta yi canjaras 3).

    Ita kuma City, cikin wasa 51 da aka ci ta kwallo biyu ko sama kafin hutun rabin lokaci ba ta taba yin nasara ba (ta yi canjaras 1 an ci ta 50).

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  7. City ta yi canji, Man City 0-2 Man Utd

    An cire B. Silva an sako Mahrez

  8. Sterling da Wan-Bissaka, Man City 0-2 Man Utd

    Sterling na kokari sosai, sai dai Wan-Bissaka na bin sa duk inda ya taka a filin wasan yana hana sa rawar gaban hantsi.

  9. Fafatawar da ake yi zuwa yanzu, Man City 0-2 Man Utd

    Jadawali

    Asalin hoton, BBC Sport

  10. Katin gargadi, De Gea

    An bai wa De Gea katin gargadi saboda bata lokaci da ya yi wurin buga bugun gida.

  11. De Bruyne, Man City 0-2 Man Utd

    Lindelof ya ceci United yayin da De Bruyne ya dada wata kwallo, inda shi kuma ya saka kafa zuwa bugun kwana.

  12. David Silva, Man City 0-2 Man Utd

    David Silva a karo na biyu sai dai kwallon ta yi yawa kuma ta fita waje.

  13. An dawo wasa, Man City 0-2 Man Utd

  14. Man City 0-2 Man Utd, Man City 0-2 Man Utd

    Wannan ne karon farko da wata kungiya ta taba cin Manchester City 2-0 a minti 45 na farko a Etihad karkashin jagorancin Pep Guardiola.

    Tawagar Man United

    Asalin hoton, Getty Images

  15. City na neman finareti, Man City 0-2 Man Utd

    Amma alkalin wasa ya yi burus da bukatarsu.

  16. An kara minti '2, Man City 0-2 Man Utd

    United na kokarin kare wannan kwallon da ta sa guda biyu. City ce ke rike da ragamar wasan ya zuwa yanzu.

  17. Bugun tazara, Man City 0-2 Man Utd

    David Silva ya buga bugun tazara mai kyau amma De Gea ya yi abin da ya saba.

  18. Man City 0-2 Man Utd

    United ce ta fara cin City 2-0 a filin wasa na Etihad kafin minti 30 din farko, bayan Liverpool da ta yi irin hakan a 2015.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  19. Jesusss, Man City 0-2 Man Utd

    Saura kiris Gabriel Jesus ya zira kwallo a ragar United bayan ya saka wa kwallo kai daga yadi na shida.

    Tabbas De Bruyne na ya hango shi.

  20. David Silva, Man City 0-2 Man Utd

    David Silva ya kai wani hari amma sai caraf a hannun De Gea.