Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Rashford ya buga ta bigi tirke, Man City 0-1 Man Utd
Rashford ya kara kai wani hari mai hadarin gaske, sai dai inaaaa kwallo ta daki turke ta fita waje.
Katin gargadi, Man City 0-0 Man Utd
An bai wa Banardo Silva katin gargadi, wanda ya janyo finaritin.
GOAL '22, Man City 0-0 Man Utd
Rashford ya cilla kwallo a ragar City daga bugun finareti. Sau bakwai ana bai wa United finareti a bana.
Kwallo ta 11 kenan da Rashford ya ci a Premier ta bana.
Asalin hoton, Getty Images
United na neman finareti, Man City 0-0 Man Utd
An ba ta
Ederson, Man City 0-0 Man Utd
Ederson ya bige kwallo ta kai uku wadanda duka ci ne, ba karamin abin a yaba ba ne wannan.
Victor Lindelof, Man City 0-0 Man Utd
Victor Lindelof ya taba kwallon har sau biyu da hannunsa amma alkalin wasa ya nuna halin ko in kula.
Waken magoya baya, Man City 0-0 Man Utd
Ta ko-ina waken magoya baya ne ke tashi don karfafa gwiwa a wannan wasan hamayya.
Man City 0-0 Man Utd, Man City 0-0 Man Utd
Raheem Sterling da alamun yau da karsashi a jikinsa.
Man City 0-0 Man Untd
Lingard ya kai wani hari amma Ederson ya hana ta shiga.
Man City 0-0Man Utd, Man City 0-0Man Utd
Cikin dakikun da ba su kai goma ba amma wasa ya yi zafi kamar an kai minti 30 amma City ta fi rike kwallon..
De Bruyne ya dad kwallon amma ta fita wajen raga.
Harin farko, Man City 0-0 Man United
James ya dada wa Ederson kwallo ta-ci amma mai tsaron ragar ya dawo da ita cikin fili.
To fa! An take wasan, Man City 0-0 Man United
Manchester City, Manchester City 6:30 Manchester United
Asalin hoton, Getty Images
Dan wasan tsakiyar Man City Ilkay Gundogan ya dawo fili bayan dakatarwar da aka yi masa, yayin da shi kuma Oleksandr Zinchenko ya murmure daga jinyar raunin da ya ji.
Shi kuwa Sergio Aguero ba zai buga wasan hamayyar ba.
Tun bayan da Wolves ta doke ta a gidanta a watan Oktoba, Man City ba ta taba yin rashin nasara sau biyu a jere ba a gidanta a wasan Premier.
Sai dai kuma ta barar da maki biyar a wasanni tsakaninta da manyan kungiyoiyin Premier guda shida a bana a gidanta, wanda shi ne abin da ta barar a baki daya kakar da ta gabata.
Manchester City ta barar da maki 13 a wasannin gida da waje - 16 ta barar a kakar 2018-2019 sai kuma 14 da ta barar a kakar 2017-2018.
Manchester United, Manchester City 6:30 Manchester United
Asalin hoton, Getty Images
Dan wasan gaban Man United Anthony Martial ka iya buga wasan duk da cewa ya dan yi fama da rauni, abin da ya sa bai buga wasansu da Tottenham ba.
Paul Pogba zai ci gaba da zama a benci sakamakon raunin da ya ji a idon-sawunsa, yayin da shi kuma Nemanja Matic yake dab da dawowa daga jinya.
Wasa hudu da ta yi a jere ba a ci ta ba a Premier, shi ne mafi tsawo da United ta yi tun daga lokacin da aka tabbatar da Solskjaer a matsayin kocin dindindin a watan Maris - ta ci biyu ta yi canjaras biyu.
Sai dai kuma United din wasa daya kacal ta ci a cikin 11 na baya-bayan nan a waje da ta buga - ta yi canjaras hudu ta yi rashin nasara shida.
Yanzu haka an zira wa United kwallo a dukkanin wasa 12 na Premier da ta buga, wanda shi ne mafi yawa a cikin sama da shekara 33 - an zira mata kwallo a wasa 15 a jere tsakanin Satumbar 1985 zuwa Afrilun 1986.
Tottenham ta yi wa Burnley ruwan kwallaye, Tottenham 5-0 Burnley
Tottenham ta yi wa Burnley ruwan kwallaye har biyar a wasan Premier mako na 16 a filin wasa na Tottenham Hotspur.
Tawagar Mourinho ta samu nasara karo na hudu kenan a dukkanin gasa tun bayan da ya karbi aikin horar da ita, amma a ranar Laraba ne Man United ta katse masa hanzarin cin wasa biyar a jere, inda aka cinye su 2-1 a Old Trafford.
Zakakurin dan wasa Harry Kane ne ya ci biyu tun a minti na hudu da kuma 54, sai Lucas Moura da ya ci a minti na tara.
Son Hueng-Min ya zira tasa kwallon ne mai kayatarwa a minti na 32 bayan ya jawo ta tun daga yadi na 20 na gidansu har zuwa yadi na 18 din Burnley kuma ya gara ta ta saman mai tsaron raga Nick Pope, babu abin da 'yan bayan suka iya yi.
Yanzu haka Son ne dan wasan da ya fi jefa kwallo a raga a sabon filin wasa na Tottenham Hotspur sama da saura, inda ya ci tara, ya bayar aka ci shida a cikin wasa 15 da ya buga.
Ba a tashi daga wasan ba sai da Mousa Sissoko ya kara ta biyar a minti na 74, abin da ya sa Spurs din ta matsa zuwa mataki na 5 kafin Man United da Wolves su buga wasanninsu.
Ranar Laraba Tottenham za ta ziyarci Bayern Munich a gasar Zakarun Turai ta Champions League.
Asalin hoton, Getty Images
Wasa ya kare, Watford 0-0 Crystal Palace
Da ma wasan bai cancanci wani ya yi nasara ba.
Watford ta yi kokari, wannan ne wasan farko da aka tashi ba a sa mata kwallo ba a raga tun watan Oktoba.