Yadda wasannin Premier mako na 16 suka gudana
Muna kawo maku rahotanni da sharhi kan wasannin Premier League kai-tsaye yayin da suke faruwa.
Rahoto kai-tsaye
Umar Mikail and Buhari Muhammad Fagge
An tafi hutun rabin lokaci, Aston Villa 1-2 Leicester
GOAL '47, Aston Villa 1-2 Leicester
Iheanachiooooo GOAL '40, Aston Villa 0-2 Leicester
Iheanachio ya kara biyu!
Kwallo ta biyu kenan ga dan Najeriyar a cikin mako guda kuma karon farko kenan da mai horarwa Brendan Rodgers yake fara wasan Premier da shi.
Iheanachio ya dawo kan ganiya, na tabbata har a Najeriya ana maraba da wannan hazakar tasa.
Ashe shi yasa Leicester ta saka fan miliyan £25 ta sayo shi!
Iheanachio, Aston Villa 0-1 Leicester
Ya kamata a ce Iheanachio ya ci ta biyu, ba don dan bayan Villa ya zugure kwallon da Vardy ya ba shi.
Jamie Vardy ya kafa tarihi, Aston Villa 0-1 Leicester

Asalin hoton, Getty Images
Jamie Vardy ya zama dan wasa na farko a Premier da ya ci kwallo a wasa takwas a jere tun bayan shekarar 2015 da Vardy shi da kansa ya ci a wasa 11 a jere.
A takaice dai Vardy ya karya wa Vardy tarihin da ya kafa.
Kauce wa XYa kamata a bar bayanan X?Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Aston Villa 0-1 Leicester, Aston Villa 0-1 Leicester
Leicester City ta zama kamar Liverpool ba ta da gida bata da waje, su duka basu san bakunta ba.
Jinjina ga kungiyoyin biyu.
GOAL '27, Norwich 1-0 Sheffield United
Alexander Tettey.
Kwallo ta farko ga Norwich haka kuma ta farko ga Tettey a Premier.
GOAL '20, Aston Villa 0-1Leicester
Jamie Vardy ya yi abin da ya saba. Kwallo ta farko a yau.
Kwallo ta 15 ga Jamie Vardy a jumlace.
Vardy zai iya goge tarihin da ya kafa na cin kwallo a wasa 11 a jere a Premier, yanzu ya ci kwallo a wasa takwas a jere.
Kauce wa XYa kamata a bar bayanan X?Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Redmond, Newcastle 0-0 Southampton
Redmond ya kamata ya ci wannan kwallon amma mai tsaron raga Martin Dubravka ya bige ta.
Norwich 0-0 Sheffield United, Norwich 0-0 Sheffield United
Alamu na nuna yau Norwich ta fito ne neman maki uku.
Sheffield United tana nuna jajurcewa game da rike kwallon.
Aston Villa 0-0 Leicester, Aston Villa 0-0 Leicester
Mai tsaron raga Tom Heaton ya fito da kwallon.
Kwallon ta fi karfi a kafar Villa.
Mummunan hari, Aston Villa 0-0 Leicester
Anwar El Ghazi ya dako wa Leicester turke, da yanzu kwallon ta saya.
Aston Villa 0-0 Leicester, Aston Villa 0-0 Leicester
A karon farko a Premier ta bana, kocin Leicester ya fara wasa da Kelechi Iheanacho, ba mamaki hakan na da alaka da rawar da ya taka a wasan da kungiyar ta yi da Everton, wanda aka tashi 2-1.
Iheanacho ya ci daya sannan ya bayar aka ci daya.
Wasan ya dauki harama.
Man United ta doke Man City a wasan hamayyar Manchester, Man City 1-2 Man United

Asalin hoton, Getty Images
Manchester United ta casa Manchester City har gida da ci 2-1, ta kuma koma matsayi na biyar a gasar Premier.
Wannan ne karon farko da aka doke Man City da kwallo biyu har gida tun da Pep Guradiola ya zama kocinta.
A minti na 22 ne da fara wasan Banardo Silva ya doke Rashford a cikin yadi na 18, abin da ya sa alkalin wasa ya bayar da finareti bayan duba na'urar VAR.
Rashford ne ya buga finaretin ya kuma ci a daidai minti na 23 wadda ita ce kwallonsa ta 10 a gasar Premier ta bana.
A minti na 29 kuma Anthony Martial ya kara kwallo ta biyu a ragar City, wanda hakan ya sa United ta ja ragamar wasan har aka juya hutun rabin lokaci.
City ce ta fi rike kwallo a wasan duka amma yawan kai hari da kuma saurin zuwa raga United ta fi.
Ana saura minti biyar a tashi daga wasan Nicolas Otamendi ya ci wa City kwallon daya da ta samu, bayan wani bugun kwana.
Man United ta doke Tottenham da Man City a mako guda, maki shidan da ta samu ya ba ta damar matsawa kusa da gurbin shiga gasar Champions League, inda yanzu take ta biyar da tazarar maki biyar tsakaninta da Chelsea wadda ke ta hudu.
A tarihi, wannan ne wasan hamayyar Manchester na 149 a Premier - Man United ta ci 57, Man City ta ci 45, an yi canjaras 47.
Yanzu Liverpool ta bai wa Man City tazarar maki 14, kuma a tarihin Premier babu wata kungiya da ta taba lashe gasar idan har ta saman teburi ta ba ta tazarar maki 14.
Kazalika, makin da Guardiola ya samu a wannan kakar shi ne mafi karanci a cikin wasa 16 na farkon kaka tun sanda ya fara aikin horarwa - maki 32.

Asalin hoton, Getty Images
Garin Machester ja ne ba shudi ba!, Wasa ya kare
An doke Man City da kwallo biyu har gida a karon farko tun da Pep Guradiola ya zama kocinta.
Yanzu Liverpool ta bai wa Man City tazarar maki 14, kuma a tarihin Premier babu wata kungiya da ta taba lashe gasar idan har ta saman teburi ta ba ta tazarar maki 14.
Kazalika, makin da Guardiola ya samu a wannan kakar shi ne mafi karanci a cikin wasa 16 na farkon kaka tun sanda ya fara aikin horarwa - maki 32.
Man United ta cinye Tottenham da Man City a mako guda, maki shidan da ta samu ya ba ta damar matsawa kusa da gurbin shiga gasar Champions League, inda yanzu take ta biyar da tazarar maki biyar tsakaninta da Chelsea wadda ke ta hudu.

Asalin hoton, Getty Images
Wasa ya kare, Man City 1-2 Man Utd
Katin gargadi, Man City 1-2 Man Utd
An bai wa Walker katin gargadi
An kara minti '5, Man City 1-2 Man Utd
United ta yi canji biyu, Man City 1-2 Man Utd
Alshley Young ya karbi Luke Shaw, Axel Tuanzebe
