An harbe tsohon kansila kan zargin satar akwati

Wannan shafi ne da yake kawo muku abubuwan da ke faruwa a game da zaɓen gwamnonin jihohin Najeriya na 2023.

Rahoto kai-tsaye

Haruna Kakangi, Abdullahi Bello Diginza, Nabeela Mukhtar Uba and Buhari Muhammad Fagge

  1. Putin zai karɓi bakuncin shugaban China a Moscow

    Yakin Ukraine

    Asalin hoton, Reuters

    Shugaba Vladimir Putin na Rasha zai karbi bakuncin takwaransa na China Xi Jinping, wanda zai kai ziyara ƙasar a mako mai zuwa.

    Gwamnatocin Beijing da Moscow sun bayyana cewa shugabannin biyu za su tattauna game da muhimman haɗin gwiwa, kana za su rattaba hannu kan wasu muhimman yarjejeniyoyi.

    Sai dai ba a yi cikakken bayani kan yarjejeniyoyin ba.

    A ranar Litinin mai zuwa shugabannin biyu zasu haɗu yayin wata liyafar cin abinci, inda washe gari za su fara cikakkiyar tattaunawa.

    Taron manyan shugabannin na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Beijing ta ke kokarin bijiro da wasu muhimman tsare-tsare guda 12 waɗanda ake sa ran za su taimaka wajen kawo karshen yakin Ukraine.

    To sai dai matsayar da China ta ɗauka na rashin cewa uffan game da yakin wani abin tambaya ne, kansancewa gwamnatin Beijing na cigaba da karfafa huldarta da Moscow.

    Wasu rahotanni sun ce ana sa rana shugaba Xi zan tattauna da kafar bidiyo da shugaba Volodymyr Zelensky na Ukraine bayan kamala ziyararsa a Moscow, koda yake har yanzu ba a tabbatar da hakan ba.

  2. Gasar Zakarun Turai: Real Madrid za ta kara da Chelsea, Man City da Bayern Munich

    UCL DRAW

    Asalin hoton, REX FEATURES

    Real Madrid za ta fafata da Chelsea a daf da na kusa da na karshe a Champions League na bana.

    Real ta kawo wannan matakin, bayan da ta fitar da Liverpool da cin 6-2 gida da waje a kakar bana.

    Ita kuwa Chelsea ta yi nasarar yin waje da Borussia Dortmund da cin 2-1 gida da waje.

    Mai rike da kofin Premier League, Manchester City za ta kara da Bayern Munich, mai Champions League shida.

    Inter Milan za ta yi tata burza da Benfica, mai rike da kofin Serie A, AC Milan za ta fuskanci Napoli.

    Idan Chelsea da Manchester City su kai zagayen gaba, kenan za su iya haduwa a daf da karshe, wata kila AC Milan ko Napoli ta fuskanci Inter Milan ko Benfica a daya wasan daf da karshe.

  3. Kwalara ta kashe mutum 37 a Habasha

    Ethiopia

    Hukumomin lafiya a Habasha sun ce cutar kwalara ta ɓarke a ƙasar tare da hallaka mutum 37 a cikin watanni shida da suka gabata a wani yanki da ya sha fama da fari.

    Cutar ta fara ɓarkewa ne tun a watan Agustan bara a lardin Oromia da kuma Somale, larduna kuma da MDD ta ce suna fuskantar mummunan fari da ba a taɓa gani cikin shekara 40.

    Hukumomi sun sanar da kafa cibiyoyin jinya domin shawo kan cutar.

    Hukumar lafiya a ƙasar ta bayyana cewa ɓarkewar cutar kyanda ta kashe mutane 148 a cikin watanni 18 da suka gabata.

  4. New Zealand na shirin haramta amfani da TikTok

    Shafin TikTok

    Asalin hoton, Getty Images

    New Zealand ta zamo ta ƙasa ta baya-bayan nan da ta ɗauki tsattsauran matakan amfani da kafar sada zumunta na Tiktok mallakin China.

    Jami'ai sun ce za a haramta amfani da manhajar a karshen watan nan, kama daga dukkan wayoyin salula da na'urorin majalisar ƙasar.

    A jiya Birtaniya ta haramta amfani da TikoTik a dukkan wayoyin salula na gwamnati.

    Haramcin da Amurka ta yi wa jami'anta kan Tikotok zai fara aiki zuwa karshen watan nan.

    Sai dai TikTok ya yi watsi da zarge-zargen cewa China za ta din ga satar bayanan sirrin ƙasashe.

  5. EFCC ta gurfanar da ɗan Indiya a kotu bisa zargin satar kuɗi

    ...

    Asalin hoton, FACEBOOK/EFCC

    Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ta gurfanar da wani ɗan ƙasar Indiya mai suna Chandra Prakash Singh, a gaban wata kotu da ke jihar Legas saboda zargin satar kuɗi da ya kai $ 200,000.

    Hukumar ta ce a ranar 16 ga watan Disamban 2020 wanda ta ke zargin ya cire kuɗi $90,000 daga wasu asussa na bankin da ba mallakinsa ba wanda kuma ya saɓawa doka.

    Sai dai wanda ake zargi ya musanta aikata laifin da ake tuhumarsa da shi.

    A don haka ne, lauya mai gabatar da ƙara B.B Bala ya bukaci da a ci gaba da tsare shi, har sai an sake saka ranar ci gaba da sauraron shari'ar.

    Sai dai lauya mai kare wanda ake ƙara, Efe Solomon Izokor, ya roki kotu da ta ba da belin wanda ake zargi.

    Amma Barrister Bala ya bukaci lauyan da ya rubuta bukatar neman belin sannan ya kawo ta gaban kotun domin ba ta damar amsawa yadda ya kamata.

    Mai shari'a Oweibo ya ɗage zaman sauraron karar zuwa 27 ga watan Yunin 2023.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  6. Ana shirin binne ɗan wasan Ghana Chiristian Atsu

    Christian Atsu

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Za a binne ɗan kwallon mai shekara 31 anjima a yau a garin mahaifarsa

    Ɗaruruwan mutane, ciki har da shugaban ƙasar Ghana suka yi bankwana da gawar Christian Atsu, wanda ya mutu a girgizar ƙasa da ta afku a Turkiyya a watan da ya gabata.

    Ana gudanar da shirin binne shi ne a Accra, babban birnin ƙasar Ghana.

    Cikin mutanen da suka halarci wajen binne ɗan wasan akwai matarsa da kuma 'ya'yansa da wakilan kungiyar kwallon kafar kasar da kuma na tsohuwar kungiyarsa ta Hatayspor da ke Turkiyya.

    An mayar da gawar Atsu zuwa Ghana ne kimanin wata ɗaya da ya gabata bayan gano ta a cikin ɓaraguzai.

    Za a binne shi zuwa anjima a yau a mahaifarsa da ke kudu maso gabashin ƙasar Ghana.

    Atsu mai shekara 31 ya shafe tsawon rayuwarsa ta kwallon kafa a gasar Firimiyar Ingila, inda ya buga wa kingiyoyi kamar Chelsea da Newcastle da kuma Everton wasa.

    Christian Atsu

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, A baya-bayan nan ne magoya bayan kungiyar Newcastle United suka girmama Atsu ta hanyar yin tafi na minti ɗaya
    Christian Atsu

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Wasu mata kenan a wajen da ake shirin binne ɗan kwallon kusa da fadar shugaban ƙasa
    Christian Atsu

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Nan kuma wasu mutane ne ke sanye da huluna kwallo yayin da suke maci
  7. Koriya ta Arewa ta kare matakinta na harba makami mai linzami cikin teku

    KCNA VIA REUTERS

    Asalin hoton, KCNA VIA REUTERS

    Koriya ta Arewa ta kare matakin gwajin makami mai linzamin da ta yi a jiya Alhamis wanda ya faɗa tekun Japan.

    Arewar ta ce martani ne kan atisayen sojin Amirka da na Koriya ta Kudu da ke gudana a yankinsu.

    Hotunan da aka yaɗa a shafukan intanet, sun nuna shugaba Kim Jong Un, na kallon yadda kaddamar da makamin mai linzamin tare da 'yar sa a gefe.

    Tun daga ranar Lahadin makon da ya gabata, Koriya ta Arewa ta harba makamai masu linzami sau uku, lokacin da shugaban Koriya ta Kudu ke ganawa da Firaministan Japan a karon farko cikin shekaru 12.

  8. Jihohin da za a iya samun matsala a sakamakon zaɓen gwamnoni - CDD

  9. Yadda ake shirye-shiryen watan Ramadan a masallacin Ka'aba

    Mataimakin sarkin Makkah ya duba yadda ake shirye-shirye a masallacin Ka’aba gabanin watan Ramadana.

    Haramain Sharifain

    Asalin hoton, Haramain Sharifain

    Haramain Sharifain

    Asalin hoton, Haramain Sharifain

    Haramain Sharifain

    Asalin hoton, Haramain Sharifain

    Haramain Sharifain

    Asalin hoton, Haramain Sharifain

  10. Jami'an tsaro da masu zanga-zanga sun yi arangama a Senegal

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Masu zanga-zanga sun yi artabu da ƴan sanda a Dakar, babban birnin Senegal a ranar Alhamis a lokacin da jagoran 'yan adawa Ousmane Sonko ya bayyana a gaban kotu.

    Ousmane Sonko na fuskantar zargin ɓata sunan wani minista, a wani ƙara da zai yanke hukuncin cewa ko zai iya yin takarar shugaban ƙasa a watan Febrairun shekara mai zuwa.

    Magoya bayan Sanko wanda tuni ya ayyana kansa a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2024, sun ce shugaba Macky Sall an amfani da ɓangaren shari'a domin kawo masa cikas a zaɓen da za a gudanar, abu kuma da shugaban ya musanta.

    Ɗan siyasar na kuma fuskantar zargin aikata fyaɗe da yin barazanar kisa.

    Magoya bayansa sun yi ta jefa wa 'ya sanda duwatsu a titunan da ke kusa da kotun.

    Wani mai ɗaukar hoto da ke aiki da jaridar AFP ya ce ya gwamman matasa na jifan wata motar jami'an tsaro a babban birnin ƙasar.

    An kuma yi ta ganin hayaki na tashi a sama a kusa da wani babban shago.

  11. Ƴan sanda a Faransa sun cafke masu zanga-zanga sama da 100

    Zanga-zanga

    Asalin hoton, Getty Images

    'Yan sandan kwantar da tarzoma a Faransa, sun cafke sama da masu zanga-zanga 100 cikin dubbai da suka fantsama tiyuna domin adawa da karin wa'adin shekarun ritaya ga ma'aikata.

    An yi amfani da hayaki mai sa hawaye da feshin ruwa kan masu boren, da suka kunna wuta a dandalin Place de la Concorde.

    Tun bayan sanarwar shugaba Emmanuel Macron na kara shekaru 62 da ake da su na yin ritaya, a wani mataki da ya ce zai kawo gagarumin sauyi da ci gaba ga tsarin fanshon Faransa, aka yi ta musayar yawu kalamai tsakanin 'yan majalisar dokoki na jam'iyyun adawa, inda su ka fara bazanar kada kuri'ar yanke kauna da gwamnatin Macron.

    A bangare guda kuma kungiyoyin kwadago sun fara shirin gagarumar zanga-zanga da yajin aiki a mako mai zuwa.

  12. Hotunan yadda aka saka sabon shinge a masallacin Manzon Allah a Madina

    An sanya sabon shinge a makon nan a gaban wajen da masu ziyarar Manzon Allah S.A.W ke wucewa domin yi masa sallama.

    Musulmai daga sassa daban-daban na duniya ne ke kai ziyara masallacin Manzon Allah S.A.W.

    Haramain/Twitter

    Asalin hoton, Haramain/Twitter

    Haramain/Twitter

    Asalin hoton, Haramain/Twitter

    Haramain/Twitter

    Asalin hoton, Haramain/Twitter

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  13. Bakuwar cuta ta hallaka mutum biyar a Tanzania

    Tanzania

    Hukumomi a Tanzania sun ce wata bakuwar cuta ta kashe mutum akalla biyar a arewa maso yammacin kasar.

    Rahotanni sun kuma suna cewa wasu mutum bakwai sun kamu da cutar a lardin Kagera, inda hukumomi suka tura tawagar likitoci domin binciko da kuma gano cutar.

    Jami'an lafiya a ƙasar sun ce basu taɓa gani irin cutar ba.

    Alamomin cutar sun haɗa da tari da ciwon kai da kasala da kuma zubar jini, a cewar babban likitar gwamnati Tumaini Nagu.

    "Gwamnati ta haɗa tawagar kwararrun likitoci da turasu zuwa yankin domin gudanar da bincike da nufin gano ta,'' in ji Farfesa Nagu.

    Ta bukaci mazauna yankin da su kwantar da hankalinsu, su kuma guji mu'amala da waɗanda suka kamu da cutar.

    A watan Yulin bara, an samu mutum 20 da suka kamu da wata bakuwar cuta a lardin Lindi da ke kudancin ƙasar, inda uku suka mutu.

  14. Ƙasashen yamma na ɓata lokacinsu wajen kare 'yan luwaɗi da maɗigo - Museveni

    Museveni

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban ƙasar Uganda Yoweri Museveni ya zargi ƙasashen yamma da ɗora wa ƙasashen Afirka hakkin kare ‘yan luwadi wanda ke zuwa a daidai lokacin da ‘yan majalisar dokokin ƙasar ke shirin kaɗa kuri’a kan wani kudirin doka na adawa da masu luwaɗi da maɗigo.

    Kudirin dokar da aka gabatar a farkon wannan watan, ya tanadi hukunci mai tsanani kan ƴan luwaɗi da maɗigo a ƙasar da tuni ta haramta ayyukansu. Hakan dai ya janyo suka daga kungiyoyin kare hakkin bil'adama.

    A wani jawabi da ya gabatar a gaban majalisar dokokin ƙasar a jiya Alhamis, shugaba Museveni ya ce barazanar da ƙasashen yamma ke yi na kakaba wa ƙasashen Afirka takunkumin waɗanda ke adawa da luwaɗi da maɗigo munafunci ne saboda su ma ƙasashen suna da wasu dabi'un da al'umma basu saba da su ba.

    "Ya kamata ƙasashen yamma su daina ɓata lokacinsu ta hanyar kokarin ɗora wa wasu mutane abin da suke so," in ji mista Museveni.

    Ya kara da cewa "Turawa da sauran kungiyoyi suna auren 'yan uwa da dangi, a nan auren ɗan uwa haramun ne, shin ya kamata mu sanya musu takunkumi kan auren dangi? Wannan ba aikinmu ba ne," in ji shi.

    A karkashin dokar da aka gabatar, duk wanda aka kama da laifi ko kuma ya bayyana kansa a matsayin ɗan kungiyar LGBT zai fuskanci ɗaurin shekaru 10 a gidan yari.

    Ana zargin gwamnatocin ƙasashen yamma da kungiyoyin agaji da ke aiki a Uganda da mara wa ƴan luwaɗi da maɗigo a ƙasar.

    Uganda ba ta gurfanar da kowa a gaban kuliya ba a shekarun baya-bayan nan duk da tsauraran dokokin hana luwaɗi.

  15. Burna Boy zai yi wasa a wasan karshe na Champions League

    Fitaccen mawakin Najeriya Burna Boy zai yi wasa a wasan karshe na gasar Zakarun Turai na wannan shekara wanda za a yi a birnin Santanbul na Turkiyya.

    Mawakin wanda kuma ya samu kyautar Grammy mai salon wakar afrobeat zai cace da ɗimbin mutane da za su halarci wasan karshen, a cewar wata sanarwa da UEFA ta fitar.

    "Mun yi tanadi na musamman don cacewa da masoya kwallon kafa,'' in ji Burna Boy gabanin wasan da zai yi a filin wasa na Atatürk Olympic.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  16. Ina son gwamnati mai zuwa ta ci gaba da yaki da rashawa - Buhari

    Buhari

    Asalin hoton, Bashir Ahmad/Twitter

    Shugaba Muhammadu Buhari ya ce cin hanci da rashawa ya kasance babbar barazana da ƙasashe ke ci gaba da fuskanta.

    Ya bayyana haka ne jiya a fadarsa da ke Abuja, yayin da ya karɓi bakuncin shugabannin gudanarwar Kotun Ɗa’ar Ma’aikata karkashin jagorancin shugabanta, Danladi Yakubu Umar.

    Buhari ya ce yana fatan irin kokarin da gwamnatinsa ta yi wajen yaki da cin hanci da rashawa, ita ma gwamnati mai zuwa za ta ɗora a kan haka.

    Ya bayyana Kotun Ɗa'ar Ma'aikata a matsayin muhimmiya ce wajen yaki da rashawa da gwamnatinsa ta yi cikin shekaru bakwai da suka gabata, inda ya ce irin waɗannan hukumomi suna taimakawa gwamnati wajen yaki da masu satar dukiyar ƙasa.

    "Muna fata cewa irin tubali ko kokari da ta yi a ɓangaren yaki da rashawa ya zama mai zuwa ta ɗora kan haka saboda yadda hakan ke barazana ga ƙasashe,'' in ji Buhari

    Buhari ya kuma gode wa Kotun Ɗa'ar Ma'aikatan saboda irin sadaukarwa da ta yi duk da irin matsin tattalin arziki da kuma raguwar kuɗaɗen shiga da gwamtai ta samu,'' inda ya yi alkawarin samar da sabbin tsare-tsare da za su samar da kuɗade ga hukumomin waɗanda ya ce suna da matukar muhimmanci.

    Shugaban Kotun, Danladi Umar ya yaba wa gwamnatin Buhari kan irin rawar da ta taka a fannin raya ababen more rayuwa da noma da kuma samar da ayyukan yi da sauransu.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  17. Assalamu Alaikum

    Masu bibyar mu a wannan shafi na kai-tsaye barkan mu da wannan safiya ta Juma'a - Hajja Babbar Rana.

    Ahmad Tijjani Bawage ne zai kasance da ku domin kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da makwaɓtanta da kuma sauran sassan duniya.

    Idan kun shirya sai mu fara