Real Madrid za ta kara da Chelsea a Champions League

Asalin hoton, Getty Images
Real Madrid za ta fafata da Chelsea a daf da na kusa da na karshe a Champions League na bana.
Real ta kawo wannan matakin, bayan da ta fitar da Liverpool da cin 6-2 gida da waje a kakar bana.
Ita kuwa Chelsea ta yi nasarar yin waje da Borussia Dortmund da cin 2-1 gida da waje.
Mai rike da kofin Premier League, Manchester City za ta kara da Bayern Munich, mai Champions League shida.
Inter Milan za ta yi tata burza da Benfica, mai rike da kofin Serie A, AC Milan za ta fuskanci Napoli.
Idan Chelsea da Manchester City su kai zagayen gaba, kenan za su iya haduwa a daf da karshe, wata kila AC Milan ko Napoli ta fuskanci Inter Milan ko Benfica a daya wasan daf da karshe.
Jadawalin quarter finals a Champions League
- Inter Milan da Benfica
- Real Madrid da Chelsea
- Manchester City da Bayern Munich
- AC Milan da Napoli
Wasannin daf da na kusa da na karshe
Ranar 11 ga watan Afirilun 2023
- Inter Milan da Benfica
- Real Madrid da Chelsea
Ranar 12 ga watan Afirilun 2023
- Manchester City da Bayern Munich
- AC Milan da Napoli
Real Madrid ce za ta fara karbar bakuncin Chelsea a Santiago Bernabeu a wasan farko ranar 11 ga watan Afirilu.
Sannan Chelsea ta karbi bakuncin wasa na biyu a Stamford Bridge ranar 19 ga watan Afirilu.
Chelsea tana da Champions League biyu, ita kuwa Real ita ce mai rike da na bara kuma na 14 jimilla.
Za a fara buga wasannin farko ranar Talata 11 da kuma Laraba 12 ga watan Afirilu, sannan a yi wasa na biyu tsakanin 18 da kuma 19 ga watan Afirilu.
Za a fara wasan farko a daf da karshe daga ranar 9 da 10 ga watan Mayu, sannan a buga zagaye na biyu ranar 16 da 17 ga watan Mayu.
Za a buga wasan karshe ranar Asabar 10 ga watan Yunin 2023 a Istanbul a filin wasa Ataturk Olympic Stadium.











