An harbe tsohon kansila kan zargin satar akwati

Wannan shafi ne da yake kawo muku abubuwan da ke faruwa a game da zaɓen gwamnonin jihohin Najeriya na 2023.

Rahoto kai-tsaye

Haruna Kakangi, Abdullahi Bello Diginza, Nabeela Mukhtar Uba and Buhari Muhammad Fagge

  1. Ma'aikatan zaɓe da ƴan jarida sun sha da ƙyar a wata mazaɓa a Kano

    Ma'aikatan zaɓe

    Rahotanni daga Kano a Najeriya sun bayyana cewa an samu wata hatsaniya a mazaɓar Ja'oji har wasu ma'aikatan zaɓe da ƴan jarida suka sha da ƙyar.

    Wakilin BBC wanda ya kasance cikin ƴan jaridar da suka ɓuya a wani aji tare da malaman zaɓe, ya ruwaito cewa ɓatagarin sun kutsa cikin mazaɓar ne a dai-dai lokacin da jami'an INEC ke shirin fara ƙirgen ƙuri'u bayan da aka kammala zaɓe a mazaɓar.

    Lamarin dai ya sa dole aka dakatar da aikin har zuwa lokacin da lamarin ya lafa.

    Wakilin na BBC ya tabbatar da cewa mutanen da ke mazaɓar sun nemi mafaka a wata makaranta a lokacin da suka ga ɓatagarin.

    Ya ce ya hango ƴan daban ɗauke da muggan makamai sun kai kawo a mazaɓar, inda ya ce sun tafi da na'urar VBAS guda ɗaya daga mazaɓar.

    A cewarsa, jami'an tsaro ba su isa wajen ba a lokacin da ɓatagarin suka shiga mazaɓar.

    Tuni dai aka samu lafawar al'amarin inda kuma aka soma ƙirgen ƙuri'un a wannan mazaɓa.

  2. Za ku iya kallon shirin BBC Hausa na musamman kan zaɓen gwamnonin Najeriya kai-tsaye a shafinmu na facebook:

  3. Yadda wasu 'yan takarar gwamna suka kaɗa ƙuri'unsu

    Kauna Bauchi
    Bayanan hoto, Bala Abdulƙadir Mohammed
    Binani

    Asalin hoton, Adamu Jimeta

    Bayanan hoto, Sanata Aisha Dahiru Ahmad Binani
    ddf
    Bayanan hoto, Sanata Halliru Dauda Jika
    NNPP

    Asalin hoton, Bello Muhammad Hadi

    Bayanan hoto, Dan takarar gwamnan jihar Taraba ƙarƙashin jam'iyyar NNPP Farfesa Muhammad Sani Yahaya
    xx
    Bayanan hoto, Air Marshall Abubakar Sadique mai ritaya, ɗan takarar gwamnan jihar Bauchi ƙarƙashin jam'iyyar APC
    mmm

    Asalin hoton, media aide

    Bayanan hoto, Gwamnan jihar Borno kuma ɗan takarar gwamna ƙarƙashin jam'iyyar APC
    Maimala Buni

    Asalin hoton, Media aide

    Bayanan hoto, Gwamnan jihar Yobe kuma ɗan takarar gwamnan jihar ƙarƙashin jam'iyyar APC Maimala Buni
    mm
    Bayanan hoto, Gwaman jihar Legas wanda shi me ke naman takarar wa'adin mulki na biyu
    sx
    Bayanan hoto, Gwamnan jihar Oyo da ke kudu maso yammacin Najeriya Seyi Makinde na jam'iyyar PDP wanda shi ma ke neman wa'adin mulki na biyu.
  4. Atiku ya zargi INEC INEC kan ƙarancin fitowar masu zaɓe a jihar Adamawa

    ss

    Asalin hoton, Atiku Abubakar

    Bayanan hoto, Atiku Abubakar

    Dan takarar shugabancin Najeriya na jam'iyyar PDP a zaɓen da ya gabata Atiku Abubakar ya ɗora alhakin ƙarancin fitowar jama'a rumfunan zaɓen gwamna kan hukumar zaɓen ƙasar, da ake gudanarwa yau a faɗin ƙasar.

    Atiku Abubkar wanda ya kaɗa ƙuri'arsa a birnin Yola da ke jihar Adama ya koka kan rashin fitowar jama'a rumfunan zaɓen, wanda ya ɗora alhakin hakan kan hukumar INEC ne.

    “Abin takaici ne, rashin fitowar mutane zaɓe a yau, rashin cikakken shiri ne daga INEC ya sa ta gabatar da sakamako marar inganci a zaɓen ranar 25 ga watanb fabrairu''.

    Tsohon mataimakin shugaban ƙasar wanda ya zanta da manema labarai bayana kaɗa ƙuri'arsa ya ce yana fatan hukumar zaɓen ƙasar za ta yi amfani da wannnan dama domin gyara kura-kuran da suka yi a baya.

    Sai dai har yanzu INEC ɗin ba ta mayar da martani kan zargin ba.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  5. Ƴan daba sun tarwatsa masu zaɓe a wasu sassan Najeriya

    Kano

    Asalin hoton, Others

    Rahotanni daga sassa daban-daban na Najeriya na cewa ƴan daba sun tarwatsa masu zaɓe a sassan ƙasar.

    Kano: Wani hoto ya nuna yadda masu matasa da ake zargin ƴan daba ne sun tarwatsa kayan zaɓe, suka kuma kori jama'a a ƙaramar hukumar Rogo. Lamarin ya faru ne a a lokacin da ake zaɓen gwamnnoni da na ƴan majalisun dokoki.

    Lagos: Rahotanni daga kafofin sada zumunta da dama sun nuna cewa an samu tashin hankali a wasu rumfunan zaɓe a cibiyar kasuwancin ƙasar ta Najeriya.

    Wata tauraruwar fina-finan Nollywood Chioma Akpotha ta wallafa wani bidiyo a shafinta na Instagram inda ta yi zargin cewa wasu mutane sun kai mata hari da wuƙa.

    "Ban iya ma fito da waya ta ba lokacin da yaran nan suka zo, suka ringa dukan motata, suka fasa min madubin gefe na mota..." tana magana ne a lokacin da take barin rumfar zaɓen.

    Bayelsa: Rahotanni na cewa wasu ƴan daba sun kwace tare da lalata kayan zaɓen ɗan majalisar dokoki a rumfuna masu lamba 02 da 03 da 04 da kuma rumfa ta 05 a mazaɓa ta biyar a ƙaramar hukumar Ogbia a jihar Bayelsa, kamar yadda kafofin yaɗa labarai na jihar suka rawaita.

    A nasa ɓangaren, gwamna Douye Diri ya yi Allah wadai da da harin da kakkausar murya, yana mai kira ga babban sufeton ƴan sanda na ƙasa da kwamishinan ƴan sandan jihar Bayelsa su maido da zaman lafiya a yankin, kamar yadda mai taimaka masa a harkokin kafofin watsa labarai Daniel Alabrah ya tabbatar a shafinsa na Faceook.

  6. Mazauna wani rukunin gidaje a Legas sun ƙi yarda su yi zaɓe

    masu zaɓe

    Mazauna rukunin gidajen Victoria Garden City 'VGC' da ke Legas sun ce ba za su kaɗa ƙuri'unsu ba, har sai jami'an zaɓe sun amince da gudanar da zaɓen a rumfar zaɓen da suka saba gudanar da zaɓensu shekaru da dama da suka gabata.

    Mazauna rukunin gidajen da BBC ta zanta da su sun zargi jam'ain zaɓe da sauya musu inda suka saba gudanar da zaɓen a baya wato cikin rukunin gidajen, inda a wannan karon suka kafa rumfar a ƙofar shiga rukunin gidajen.

    "Mun ƙi yin zaɓe saboda rumfar zaɓen da jami'an zaɓe suka kafa ba ta kan ƙa'ida. A baya mun saba gudanar da zaɓen a cikin unguwarmu, mun kwashe shekaru masu yawa ana yin haka, to don me ya sa a yau za su sauya mana rumfar zaɓe?"

    "idan sun ga dama su ce ba mu yi zaɓe ba, ba za mu je waje domin zaɓe ba, bayan ga inda muka saba yi a baya'', kamar yadda wata matashiya ta shaida wa BBC.

    "Bai dace INEC ta sauya mana rumfar zaɓe ba a ranar zaɓe bayan ba su sanar da mu ba'', in ji wani mazaunin rukunin gidajen.

  7. An samu ƙarancin masu fita zaɓe a Kaduna

    zaɓe

    Rahotonni daga jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya sun ce an samu ƙarancin fitowar masu kaɗa ƙuri'a a zaɓen gwamna da na ƴan majalisar dokoki da ake gudanarwa a jihar.

    Bayanai sun nuna cewa tun misalin ƙarfe 8:30 na safe aka fara kaɗa ƙuri'a a wasu sassan birnin.

    A mafi yawan rumfunan zaɓen da BBC ta ziyarta a cikin birnin Kaduna an ga ƙarancin fitowar mutane domin kaɗa ƙuri'a, ba kamar yadda aka gani a zaɓen shugaban ƙasar da ya gabata ba, inda mutane da dama suka fito.

    Wani mai kaɗa ƙuri'a mai suna Malam Baba ya shaida wa BBC cewa a mazaɓarsa da ke unguwar Kawo mutane ƙalilan ne suka fito zaɓe.

    Ya kuma ce babu mata sosai a rumfar zaɓen nasa.

    A sassan ƙasar da dama dai rahotonni na cewa mutane ba su fito zaɓen ba kamar yadda suka fita zaɓen shugaban ƙasa.

  8. Abdussalami Abubakar ya kaɗa ƙuri'arsa

    Abdusalami Abubakau

    Tsohon shugaban mulkin sojin Najeriya Abdussalami Abubakar ya kaɗa ƙuri'arsa a jihar Naija da ke tsakiyar Najeriya.

    Abdussalami Abubakar shi ne shugaban kwamitin zaman lafiya na harkokin zaɓen Najeriya

  9. Me ya sa zaɓen gwamnonin jihohi ke da muhimmanci a Najeriya?

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo
  10. Buhari ya shawarci 'yan Najeriya su zaɓi ra'ayinsu

    Buhari

    Asalin hoton, Nigerian Presidency

    Shugaban Najeriya Muhammdu Buhari ya shawarci 'yan ƙasar da su bi ra'ayinsu wajen zaɓar shugabanni na gari, a ɓangaren zartarwa da na majalisa, yana mai cewa zamanin sayen ƙuri'a ya wuce.

    A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasar Malam Garba Shehu ya fitar, jim kaɗan bayan shugaban ƙsar ya kaɗa ƙuri'a, Muhammadu Buhari ya ce a yanzu mutane sun waye da zaɓen ra'ayinsu.

    “Ina sane yanzu ba kamar da ba ne, mutane ba su da kuɗin da za su ja ra'ayin masu kaɗa ƙuria, kamar yadda suke yi a baya. A yanzu idan mutum ya kawo kuɗi, mutane za su karɓa kuma su zaɓi ra'ayinsu.

    Shugaba Buhari ya yaba wa kafofin yaɗa labaran ƙasar bisa rawar da ya ce sun taka wajen wayar da kan 'yan ƙasar wajen sanin haƙƙokinsu a matsayinsu na 'yan ƙasa, tare da samar musu kafar kalubalantar shugabanninsu kan alƙawuran da suka ɗaukar musu.

    ''Kafofin yaɗa labarai suna yin abin da ya dace wajen wayar da kan mutane, tare da ba su damar tofa albarkacin bakinsu. Za ka ji ana yi wa shugabanni tambayoyi masu tsauri a lokutan da ake hira da su a gidajen talabijin da radiyo da sauran kafofi, kuma a kodayaushe 'yan jarida na tabbatar da cewa an amsa waɗannan tambayoyi''.

    Daga ƙarshe shugaban ya ce bai yi mamakin nasarar da Bola Ahmed Tinubu ya samu a zaɓen shugaban ƙasar da ka gudanar ranar 25 ga watan Fabrairun da ya gabata ba.

  11. 'Ba zan yi zaɓen gwamna ba saboda ban ji daɗin zaɓen shugaban ƙasa ba'

    Madam Victoria Briggs

    A lokacin zaɓen shugaban ƙasa an samu mutane da dama waɗanda suka fito domin kaɗa ƙuri’a a Port Harcourt na jihar Rivers.

    A zaɓen na shugaban ƙasa wanda ya gudana a ranar 25 ga watan Fabarairu, mutane sun isa rumfuna suka jira isowar jami’an zaɓe, sai dai wannan karo ba haka abin yake ba.

    Madam Victoria Briggs ta ce ba ta ji daɗin yadda aka yi zaɓen shugaban ƙasa ba, shi ya sa ba za ta yi zaɓen gwamna ba.

    “Ba na murna, wancan zaɓen da muka yi an watsar da ƙuri’unmu, saboda haka mene amfanin na sake fitowa kaɗa ƙuri’a?”

    A rumfar zaɓe ta 04, yanki na 02 aikin zaɓe na ci gaba da gudana, amma babu mutane da yawa.

    A lokacin zaɓen shugaban ƙasa an samun jinkirin isowar masu aikin zaɓe a wannan mazaɓa, amma a wannan karo komai ya iso kan lokaci.

    Sai dai kuma masu kaɗa ƙuri’a sun ƙi fitowa.

    Mutane ba su fito kaɗa ƙuri'a ba a mazabar PHALGA, yanki na 2 da 4
  12. Ƴar takarar gwamnan Rivers ta kaɗa ƙuri'a

    Beatrice Itubo

    Asalin hoton, King Onunwor

    Bayanan hoto, Beatrice Itubo

    Ƴar takarar gwamnan jihar Rivers ƙarƙashin jam'iyyar Labour (LP) Beatrice Itubo, lokacin da take kaɗa ƙuria a rumfar zaɓen mazaɓa ta 1, yankin na 6 a ƙaramar hukumar Emohua da ke jihar ta Rivers.

  13. Gwamnan Bauchi Bala Mohammed ya kaɗa ƙuri'arsa

    zaɓe

    Asalin hoton, Media Team

    Gwamnan jihar Bauchi da ke arewa maso gabashin Najeriya, kuma ɗan takarar gwaman jihar ƙarƙashin jam'iyyar PDP mai mulkin jihar ya kaɗa ƙuri'arsa.

    ...

    Asalin hoton, OTHER

    Gwamna Bala Abdulƙadir Mohammed - wanda aka fi sani da Ƙauran Bauchi - na neman wa'adin mulkin jihar karo na biyu.

    Kauran Bauchi

    Asalin hoton, Media Team

  14. Yadda ake kaɗa ƙuri'a a zaɓen gwamnonin jihohi a Najeriya

    Bayanan bidiyo, Yadda ake kaɗa ƙuri'a a zaɓen gwamnonin jihohi a Najeriya, 2023
  15. An samu rahotonnin sayen ƙuri'a a Kano

    Sayen Ƙuri'a

    Rahotonni daga jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya na cewa an ga wasu da ake zargin wakilan wasu jam'iyyun siyasa ne na raba atamfa da yaduka har ma da kuɗi.

    Hotuna da BBC ta samu sun nuna yadda mutane suke karɓar irin waɗannan atamfofi, yayin da wasu kuma suka ƙi karɓa.

    sayen kuri'a

    Jihar Kano dai na ɗaya daga cikin jihohin da ake ganin zaɓen gwamna zai yi zafi sosai tsakanin 'yan takara.

  16. Osinbajo tare da matarsa sun kaɗa ƙuri'unsu

    Osinbajo

    Asalin hoton, Nigerian Presidency

    Mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo tare da mai ɗakinsa Mrs. Dolapo Osinbajo sun kaɗa ƙuri'unsu.

    Mataimakin shugaban kasar tare da matarsa sun kaɗa ƙuri'un ne a zaɓen gwamna da na 'yan majalisar dokokin jihohi da ake gudanarwa a jihohin ƙasar.

    Mista Osinbajo tare da Mrs Dolapo sun kaɗa ƙuri'un ne a ƙaramar hukumar Ikenne ta jihar Ogun da ke kudu maso yammacin Najeriya.

  17. Shugaba Buhari ya kaɗa ƙuri'arsa a Daura

    Buhari

    Asalin hoton, Buhari Sallau/Facebook

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kaɗa ƙuri'a a mazaɓarsa da ke Daura ta jihar Katsina a zaɓen gwamna da na 'yan majalisar dokokin jiha da ke gudanar a ƙasar.

    A ranar 25 ga watan Fabarairu ne aka zaɓi Bola Ahmed Tinubu a matsayin sabon shugaban ƙasa, wanda zai maye gurbin shugaban Buhari a kan karagar mulkin ƙasar.

    Shugaban ƙasar na kan wa'adin mulkinsa na ƙarshe, inda zai sauka daga mulki ranar 29 ga watan Mayu mai zuwa.

  18. NDLEA ta kama wakilan jam'iyya da katunan cirar kuɗi 'na sayen ƙuri'a'

    NDLEA

    Asalin hoton, NDLEA/Twitter

    Jami'an hukumar yaƙi da hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Najeriya (NDLEA) ta kama wasu mutum huɗu da ɗaruruwan katunan cirar kuɗi domin sayen ƙuri'a a jihar Ogun da ke kudu maso yammacin Najeriya.

    A wani saƙo da hukumar ta wallafa a shafinta na Twitter ta ce an loda wa kowanne kati naira 10,000, tare da saka masa lambobin sirri, waɗanda ake zargin na sayen ƙuri'a ne.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  19. An fara zaɓen gwamna da wuri a jihar Rivers, saɓanin zaɓen shugaban ƙasa

    Masu zaɓe

    An fara kaɗa ƙuri'a a wasu rumfunan zaɓe a birnin Fatakwal na jihar Rivers da ke kudu maso kudancin Najeriya.

    A wannan karon an samu nasarar rarraba kayan aikin zaɓen a kan lokaci, saɓanin lokacin zaɓen shugaban ƙasa da ya gabata, inda masu kaɗa ƙuri'a suka yi ta jiran isar ma'aikatan zaɓe zuwa rumfunan zaɓen.

    Masu zaɓe

    A wannan karon ma'aikatan zaɓen ne ke jiran masu kada ƙuri'a a rumfunan zaɓen, domin su fito su kaɗa ƙuri'unsu.

    Rahotonni na cewa a wannan karon mutane ba su fito zaɓen ba, idan aka kwatanta da zaɓen shugaban ƙasa.

  20. Tanadin da Hukumar Zaɓe (INEC) ta yi wa masu buƙata ta musamman

    Bayanan bidiyo, Latsa hoto domin kallon bidiyo