An harbe tsohon kansila kan zargin satar akwati

Wannan shafi ne da yake kawo muku abubuwan da ke faruwa a game da zaɓen gwamnonin jihohin Najeriya na 2023.

Rahoto kai-tsaye

Haruna Kakangi, Abdullahi Bello Diginza, Nabeela Mukhtar Uba and Buhari Muhammad Fagge

  1. Wasu matasa na duba sunayensu a rumfar zaɓe a Taraba

    Masu zaɓe

    Wasu matasa ke nan ke duba lambar katin zaɓen su kafin layi ya zo kansu domin sauƙaƙa wa masu aikin zaɓen a rumfar zaɓe da ke gundumar Sarkin Dawaki mai ɗauke da rumfunan zaɓe guda biyu a cikin makarantar firamare a Jalingo babban birnin jihar Taraba.

    masu zaɓe

    Wasu mata da suka fito karatun allo zuwa wajen kaɗa kuri'arsu, tafiyar kusan sa'a guda daga inda suka fito zuwa rumfar zaben a Jihar Taraba.

  2. Yadda masu aikin zaɓen gwamna suka yi tawaye a Kano

  3. Gawuna ya kaɗa ƙuri'arsa a Kano

    Dan takarar gwamnan jihar Kano na jam'iyyar APC Dr Nasiru Yusuf Gawuna ya kaɗa ƙuri'ar a akwatinsa mai lamba 041 a mazabar Gawuna da ke ƙaramar hukumar Nasarawa ta jihar Kano.

    Gawuna

    Dakta Nasiru Yusuf Gawuna shi ne mataimakin gwamnan jihar Kano, kuma yake yi wa jam'iyyar APC mai mulkin jihar takarar kujerar gwamna.

    Gawuna
  4. Jami'an EFCC sun dira a Ibadan

    Ma'aikatan EFCC

    Jami'an hukumar yaƙi da yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-ƙasa, EFCC sun je rumfar zaɓe mai lamba 11, a birnin Ibadan na jihar Oyo da ke kudu maso yammacin Najeriya.

    Jam'an EFFC

    Rumfar zaɓen dai ita ce rumfar da gwamnan jihar Seyi Makinde zai kaɗa ƙuri'arsa.

    Jami'an na EFCC dai kan ziyarci rumfunan zaɓe domin hana sayen ƙuri'a, da aikata sauran laifukan da suka shafi almundahana a rumfunan zaɓen

    jami'an EFCC
  5. Tinubu ya kaɗa ƙuri'arsa a zaɓen gwamna a jihar legas

    Tinubu

    Asalin hoton, Tinubu/Twitter

    Zaɓaɓɓen shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya kaɗa ƙuri'a a rumfarsa da ke birnin Legas a kudu maso yammacin Najeriya.

    A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Tuwita, ya ce ya bi sahun sauran al'ummar ƙasar wajen gudanar da zaɓen gwamna.

    Tinubu ya ce yana kira ga 'yan ƙasar da su fita domin kaɗa ƙuri'unsu cikin kwanciyar hankali.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  6. Me ya sa zaɓen gwamnonin jihohi ke da muhimmanci a Najeriya?

  7. Za ku iya kallon shirin BBC Hausa na musamman kan zaɓen gwamnoni a shafin facebook idan ku ka latsa hoton da ke ƙasa

  8. Mai kaɗa ƙuri'a ɗaya tilo

    ...

    Rumfar zaɓe mai lamba PU 47 da ke Hausawa a Kano na da yawan masu rajista zaɓe 22.

    Ya zuwa ƙarfe 9 na safe mai kaɗa ƙuri'a ɗaya ce kawai ta bayyana a rumfar.

    Ita ma ta ce sai da ta taka sayyada tsawon kilomita huɗu kafin isa rumfar zaɓen kasancewar babu abin hawa.

  9. An fara kaɗa ƙuri'a a wasu jihohin Najeriya, Daga Umar Elleman - Lagos, da Yusuf Tijjani - Kaduna.

    Masu zaɓe

    Tuni aka fara kaɗa ƙuri'a a wasu sassan jihar Legas da ke kudu maso yammacin Najeriya.

    masu zabe

    Dama dai hukumar zaɓen ƙasar ta ce za a fara gudanar da zaɓen ne da misalin ƙarfe 8:30 na safe

    Masu zaɓe

    Jihar ta Legas dai ta kasance jihar da ta fi kowacce jiha yawan masu rajistar zaɓe a Najeriya, inda take da sama da masu rajistar zaɓe miliyan bakwai.

    Masu zaɓe

    Can ma a jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin ƙasar tuni aka buɗe rumfunan zaɓe tare da fara kaɗa ƙuri'a a wasu rumfuna, a zaɓen gwamna da ake gudanarwa.

    Masu zaɓe

    Hukumar zaɓen ƙasar ta ɓullo da amfani da na'urar BVAS domin tantance masu kaɗa ƙuri'a a zaɓen na bana, inda ake amfani da yatsa ko fuska domin tantance masu kaɗa ƙuri'a.

    Masuz aɓe

    Can ma a jihar Nasarawa da ke arewa ta tsakiyar ƙasar tuni aka fara kaɗa ƙuri'ar a wasu rumfunan zaɓen.

    masu zaɓe
  10. Ma'aikatan zaɓe na wucin gadi sun ja tunga a Kano kan rashin biyansu haƙƙoƙinsu, Zahradden Lawan - Kano

    Ma'aikatan wucin gadi

    Jami'an INEC na wucin gadi sun ja tunga a mazabar Gawuna da ke ƙaramar hukumar Nasarawa a jihar Kano da ke arewacin Najeriya, suna masu cewa ba za su karɓi kayan aiki ba har sai an biya su hakkokinsu na aikin da suka yi a baya.

    ma'aikatan wucin gadi

    Ma'aikatan sun ce ba za su fara aiki ba har sai an biya su ko kuma an yi alƙawari a rubuce cewa za a biya kafin su yadda su karɓi kayan aiki a mazaɓar.

    Ma'aikatan wucin gadi

    Jami'an wucin gadin waɗanda masu yi wa ƙasa hidima ne, sun ce sun yi aikin zaɓen shugaban ƙasa a ranar 25 ga watan Fabrairu, amma har yanzu ba a biya su ba.

    Sun ce an biya sauran ma'aikatan da suka yi aiki tare amma su masu yi wa ƙasa hidima, har yanzu ba a biya su ba, sun ce a baya sun yi ƙorafi, ga jami'an hukumar zaɓen kuma an karɓi asusun ajiyarsu, amma sun ce an samu matsala ne wajen tura kuɗin.

    Wakilinmu da ke Kano ya ce jami'an hukumar zaɓen na kan tattaunawa da ma'aikatan domin kawo ƙarshen matsalar.

  11. Muhimman abubuwa huɗu kan fita a kaɗa kuri'a a ranar zaɓe

  12. Matakan da za a bi domin kaɗa ƙuri'a ranar zaɓe - INEC

  13. Yadda jami'an zaɓe ke shirya rumfunan zaɓe

    Tuni jami'an zaɓe suka fara shirya rumfunan zaɓe domin fara gudanar da zaɓen gwamnnoni a jihohin Najeriya

    Jami'an zaɓe
    jami'an zaɓe
    malaman zaɓe
    malaman zaɓe
  14. Assalamu alaikum

    Masu bin mu a wannan shafi barkan ku da sake dawowa shafi na kai-tseye a wannann safiya ta Asabar da ake gudanar da zaɓen gwamnoni a jihohin Najeriya.

    Ku kasance da mu domin kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a sassan ƙasar musamman kan zaɓen na gwamnonin da ake gudanarwa.

    Kuna kuma iya ziyartar shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.

    Haruna Ibrahim Kakangi tare da Abudullahi Bello Diginza ke fatan kasancewa tare da ku a daidai wannan lokaci.

    Za ku iya zuwa ƙasa domin karanta labaran da muka kawo muku a jiya Juma'a.

  15. Korona za ta daina barazana ga lafiyar al'umma a bana – WHO

    WHO

    Asalin hoton, REUTERS

    Shugaban hukumar lafiya ta duniya WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya ce yana da kwarin gwiwa a wannan shekarar zai ayyana cutar korona a matsayin annobar da ba ta kai matakin barazanar lafiya ga alummar duniya ba.

    Michael Ryan, daraktan sashen ayyukan gaggawa na hukumar WHO ya ce, hukumomin lafiya da dama za su kai matakin da za su bayyana annobar a matsayin barazana ga lafiya wadda za ta ci gaba da kashe rayuka, amma ba za ta iya katse harkokin yau da kullum ba.

    Mista Ryan ya ce, za a iya bayyana cutar tamkar wani nau’i ne na mura.

    Annobar korona ta hallaka dubban al'umma a sassan duniya tun bayan barkewar ta a farkon shekarar 2020.

  16. INEC ba ta sanya ranar zaɓen cike gurbi ba

    .

    Asalin hoton, INEC

    Hukumar zaben Najeriya ta ce har yanzu ba ta sanya ranar gudanar da zabukan cike gurbi na majalisar dokokin tarayya da aka soke ba.

    A cikin wata sanarwa da ta fitar, wadda ta samu sa hannun shugaban sashen yada labaru na hukumar Festus Okoye, INEC ta ce babu gaskiya game da bayanan da ake yadawa kan cewa za a gudanar da zabukan a lokaci daya da zaben gwamnoni da na majalisar wakilan jiha da za a yi ranar 18 ga watan Maris, 2023.

    An dai samu wurare da dama da aka soke zabe ko kuma aka ayyana su a matsayin wadanda ba su kammala ba, bayan zaben da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabarairu.

    Cikin irin wadannan gundumomi har da daukacin zabukan majalisar dattijai daga jihar Sokoto.

    Hukumar ta ce sai nan gaba ne za ta sanya ranar gudanar da wadannan zabuka bayan zaben gwamnoni da na majalisun dokokin jihohi.

    Sai dai ta ce akwai wasu zabuka guda biyu na majalisar dokokin tarayya wadanda ta jinkirta, wadanda a cewar sanarwar su za su gudana ne tare da na jihohi.

    Na farko shi ne na mazabar majalisar dattijai ta Enugu ta gabas, wanda aka jinkirta domin bai wa jam’iyyar LP damar gudanar da zaben fitar da gwani.

    Na biyu kuma shi ne zaben dan majalisar wakilan tarayya na mazabar Esan Central/Esan West/Igueben da ke jihar Edo wanda aka dage saboda matsalar da aka samu da takardun kada kuri’a.

    Hukumar ta ce wadannan ne kawai zabukan cike gurbi na majalisar dokokin tarayya da za a yi a lokaci guda da zaben gwamnonin jiha.

  17. Buhari ya isa Daura zaɓen gwamna

    Buhari Sallau

    Asalin hoton, Buhari Sallau

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya isa Daura ƙasarsa ta haihuwa a jihar Katsina da ke arewacin Najeriya, domin zaɓen gwamna da 'yan majalisu da za a yi a gobe Asabar.

    Za a gudanar da zaɓen gwamnan ne a johohi 28 cikin 36 da ƙasar ke da su, amma za a yi na 'yan majalisar jihohi a duka faɗin kasar.

    Zabe a jihar Katsina zai yi zafi tsakanin Yakubu Lado na jami'iyyar PDP da Dikko Radda APC da Nura Khlail NNPP sai kuma Jaafar Jino da ke takara a PRP.

    Buhari Sallau

    Asalin hoton, Buhari Sallau

    Buhari Sallau

    Asalin hoton, Buhari Sallau

    Buhari Sallau

    Asalin hoton, Buhari Sallau

  18. Za a sake buɗe makarantu a yankin Tigray bayan shekar uku

    .

    Asalin hoton, Human Rights Watch

    Bayan kwashe shekara uku ana rikici, yanzu an fara shirin sake buɗe makarantu a yankin Tigray da ke arewacin Habasha, rikici ne tsakanin yan ƙungiyar TPLF da gwamnatin ƙasar ya tilasta rufe makarantun.

    Yayin yaƙin basasar an lalata makarantu da dama wasu kuma an sace kayan cikinsu.

    A 2021, ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Human Rights Watch ta ce an lalata kashi ɗaya cikin huɗu na makarantun yankin Tigray sakamakon yaƙin.

    Kuma ba a biyan malaman makarantun yankin albashi tsawon shekara biyu a jere.

    “Suna tunanin fara karatu a tsakiyar watan Afrilu amma ba a kai ga amincewa ya zuwa yanzu,” Unicef ta shaida wa BBC.

    Duka tsarin ilimi na Tigray ya lalace. Tun daga watan Yulin bara an samu yara da ba sa zuwa makaranta kimanin miliyan 2.3.

  19. ICC ta bayar da sammacin kama Shugaban Rasha Putin

    BBC

    Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC ta aika takardar sammaci ga Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin da kuma shugaban hukumar kula da kananan yara na kasar, inda ake tuhumarsu da laifukan yaƙi a Ukraine.

    Ana kuma tuhumarsu da laifin tilasta wa ƙananan yara wajen tisa keyarsu daga Ukraine zuwa Rasha.

    ICC tace akwai hujjoji da ta dogara da su da ke nuna cewa Mista Putin ya taka muhimmiyar rawa wajen tilasta wa yaran barin ƙasarsu tun bayan da Moscow ta fara ƙaddamar da hare-harenta kan Ukraine watanni 13 da suka gaba.

    Takardar sammacin na nufin za a kama Mista Putin da zarar ya bar kasarsa, sai dai fadar Kremlin ta bayyana sammacin da cewa abin takaici ne da kuma ba za a lamunta ba.

  20. An tsaurara tsaro a Najeriya gabanin zaɓen gwamna da 'yan majalisu

    Getty Images

    Asalin hoton, Getty Images

    An tsaurara tsaro a jahoji 28 cikin jahohi 36 na Najeriya inda za a gudanar da zaɓen gwamnoni da na ‘yan majalisun dokokin jahohi a gobe Asabar.

    Babban sifeton ‘yan sandan Najeriyar, Usman Baba, ya ayyana dokar hana zirga-zirgar ababen hawa a jahojin daga karshe 12 na tsakar daren Juma’a har zuwa karfe shida na yammacin ranar Asabar bayan kamala zaɓukan.

    Rahotanni sun ce an samu hatsaniya a tsakanin magoya bayan jam’iyyu a Jahar Legas, inda gwamnan Jahar mai ci na jam’iyyar APC, Babajide Sanwo-Olu, yake fuskantar zazzafar adawa daga ɗan takarar gwamnan Jahar na jam’iyyar Labour, Gbadebo Rhodes-Vivour.

    Jam’iyyar ta Labour ce dai ta samu kuri’u mafi yawa a zaɓen shugaban ƙasa da ya gudana watan jiya.