Mutum sama da miliyan daya sun kamu da coronavirus a duniya

Wannan shafin na kawo muku abubuwan da ke faruwa a duniya baki daya dangane da annobar coronavirus.

Rahoto kai-tsaye

Nasidi Adamu Yahaya, Awwal Ahmad Janyau, Usman Minjibir and Umar Mikail

  1. Labarai da dumi-dumi, Karin mutum biyar sun warke daga coronavirus a Najeriya

    Gwamnatin jihar Legas a Najeriya za ta sallami karin mutum biyar da suka warke daga cutar coronavirus.

    Mai taimaka wa Shugaban Najeriya kan kafofin sadarwa na zamani Bashir Ahmed ne ya wallafa hakan a shafinsa na Twitter kuma ya tabbatar mana da hakan ta wayar tarho.

    Sai dai har yanzu hukumar da ke yaki da yaduwar cututtuka ta Najeriya ba ta tabbatar da warkewar tasu ba.

    Idan ta tabbata sun warke din, jumullar wadanda suka warke daga cutar a Najeriya sun zama takwas.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  2. Mece ce na'urar ventilator?

    .

    Asalin hoton, Dyson

    Na'urar ventilator wata na'ura ce ta musamman da ke taimaka wa mara lafiya wajen yin numfashi a duk lokacin da wani ciwo ya sa huhunsa bai iya fitar da numfashi da kyau.

    Wannan zai bayar da dama ga mara lafiya ya yi numfashi har ya samu lafiya idan yana da rabon warkewa.

    Gwamnatoci a fadin duniya na ta kokarin samo dubban wadannan na'urori tun bayan barkewar cutar coronavirus.

  3. Sanatocin Najeriya sun bayar da rabin albashinsu don a yaki coronavirus

    .

    Asalin hoton, @NGRSenate

    Majalisar dattawan Najeriya ta bayyana aniyar sanatocin kasar na bayar da rabin albashinsu domin taimakawa a yaki annobar coronavirus.

    Mukaddashin mai magana da yawun majalisar dattawan, Godiya Akwashiki ne ya sanar da hakan a ranar Litinin.

    Ya bayyana cewa 'yan majalisar za su fara bayar da rabin albashinsu tun daga watan Maris din 2020 har zuwa lokacin da za a samu saukin wannan annoba a kasar.

    Ya kuma yaba wa ma'aikatun gwamnati da ke bada himma wajen ganin cewa an yaki wannan cuta da coronavirus.

    Sanatocin sun yi kira ga jama'ar kasar kan bin dokoki da kuma ka'idoji da aka bayar domin kiyaye kai daga wannan cuta.

  4. An samu karin mutum biyar da suka kamu da coronavirus a Tanzania

    Adadin mutanen da suka kamu da coronavirus a Tanzania ya kai 19, bayan ma'aikatar lafiyar kasar ta tabbatar da karin mutum biyar da suka kamu da cutar ranar Litinin.

    A cikin mutum biyar din da suka kamu cutar, mutum biyu daga tsuburin Zanzibar suke, yayin da sauran mutum uku suna birnin Dar es Salaam.

    Dukkan mutum ukun da ke Dar es Salaam 'yan kasar Tanzania ne masu shekaru tsakanin 21 zuwa 49.

    Dukkansu sun yi mu'amala da mutanen da ake zargi suna dauke da cutar.

    Dukkansu sun yi mu'amala da mutanen da ake zargi suna dauke da cutar

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Dukkansu sun yi mu'amala da mutanen da ake zargi suna dauke da cutar
  5. Filayen da aka mayar asibiti saboda coronavirus

    Ganin yadda coronavirus ke kara yaduwa a fadin duniya da kusan mutum 735,000 da suka kamu da ita, ana ta kokarin ginin asibitocin wucin gadi sakamakon karancin wajejen killace masu dauke da coronavirus a fadin duniya.

    An mayar da filin wasa na Pacaembu da ke Sao Paulo a Brazil asibitin wucin gadi mai daukar gadaje 200

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, An mayar da filin wasa na Pacaembu da ke Sao Paulo a Brazil asibitin wucin gadi mai daukar gadaje 200
    An fara wannan ginin asibitin a Rafah da ke zirin Gaza wanda aka fara a tsakiyar watan Maris

    Asalin hoton, AFP

    Bayanan hoto, An fara wannan ginin asibitin a Rafah da ke zirin Gaza wanda aka fara a tsakiyar watan Maris
    Dakin taro na ExCel kenan da ke birnin Landan  da aka mayar asibiti mai daukar gadaje 4,000

    Asalin hoton, PA Media

    Bayanan hoto, Dakin taro na ExCel kenan da ke birnin Landan da aka mayar asibiti mai daukar gadaje 4,000
    .

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Wani filin kwallo a birnin Legas da ke Najeriya kenan aka mayar wurin killace masu coronavirus na wucin gadi.
  6. Kasashen Afirka na bayar da tallafi ga masu karamin karfi

    .

    Asalin hoton, TASS

    A daidai lokacin da adadin masu dauke da coronavirus ke kara karuwa a kasashen Afirka, gwamnatocin kasashe da dama na daukar matakai domin tallafa wa masu karamin karfi wadanda dokar hana fita ta shafa da sauran matakan da aka dauka.

    A kasar Rwanda wadda ke da mafi yawan masu dauke da cutar a Gabashin Afirka, Shugaba Paul Kagame ya bayyana cewa ana raba abinci ga wadanda suke cikin hali na bukata, duk da cewa jama'a da dama na cewa ba su samun wannan tallafin.

    A kasar Kenya, ma'aikatar aikin gona ta kasar ta bayyana cewa za ta rarraba hatsi ga masu karamin karfi a kasar, inda kuma kungiyoyin addinai da kuma kungiyoyi da 'yan kasuwa na yin kira da a bayar da tallafin abinci.

    A wasu kasashen, ana daukar matakai masu tsauri ga masu bijire wa dokokin da aka saka. A kasar Ethiopia, 'yan sanda sun harbe wani mutum har lahira sakamakon take dokar da ya yi ta hana zuwa mashaya.

    • An saka sabuwar ranar fara gasar Olympics

      An bayyana sabuwar ranar da za a gudanar da gasar Olympics ta duniya wadda za a yi a Tokyo.

      Ana sa ran fara gasar ne daga 23 ga watan Yuli zuwa 8 ga watan Agustan 2021 kamar yadda kwamitin gasar ya sanar.

      An dage gasar ta Olympics ne wadda aka so a fara 24 ga watan Yulin wannan shekara sakamakon annobar coronavirus.

      Za kuma a fara gasar ta masu nakasa a ranar 24 ga watan Agusta zuwa 5 ga watan Satumbar 2021.

    • Yarima Charles 'na samun sauki' ya fita daga killacewa

      .

      Asalin hoton, Reuters

      Yarima Charles wanda da ne ga sarauniyar Ingila ya fito daga killacewa, bayan ya shafe kwanaki bakwai a killace a Scotland sakamakon gwaji da ya nuna yana dauke da coronavirus.

      An yi wa matarsa Cornwall mai shekaru 72 gwajin cutar sai dai babu alamun cewa ta kamu da cutar.

      Wani jami'in fadar sarauniya ya bayyana cewa Yariman a halin yanzu yana cikin koshin lafiya kuma yana bin umarnin gwamnati.

    • Firai Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu zai killace kansa

      Ana dab da killace Firai Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu bayan da aka gano wani cikin mataimakinsa na dauke da coronavirus, kamar yadda jaridar Haaretz ta ruwaito.

      Ofishinsa ya ce Netanyahun tare da wasu masu ba shi shawara za su killace kansu.

      A ranar Litinin ne aka gano mataimakin nasa ya kamu da cutar. Ofishin Firai Ministan ya ce matakin killace kan kariya ce kuma an dauke shi ne ma tun kafin sakamakon gwajin abokin aikin nasa ya fito.

    • Za a yi wa 'yan majalisar dokokin Kenya gwajin coronavirus

      Za a yi wa 'yan majaisar dokokin Kenya 50 gwajin coronavirus a yayin da ake ci gaba da nuna fargabar cewa sun kamu da cutar daga wani abokin aikinsu wanda aka tabbatar yana dauke da ita, a cewar jaridar the Daily Nation.

      Majalisar dokokin ta aike wa ma'aikatar lafiya sunayen 'yan majalisar da ma'aikatansu da take so a yi wa gwajin cutar, in ji jaridar.

      Kazalika tana so a tursasa musu killace kansu.

      Rahotanni sun ce dan majalisa Kamoti Mwamkale ya kamu da cutar bayan ya yi mu'amala da mataimakin gwamnan lardin Kilifi - wanda ya kamu da cutar bayan ya koma kasar daga Jamus.

      Jaridar ta ambato wata majiya a majalisar tana cewa ana duba lafiyar Mr Mwamkale.

      An bayar da rahoton cewa ya halarci zaman majalisa ranar 17 ga watan Maris tsawon minti 19 kuma ana hasashen cewa ya halarci tarukan kwamitin majaisar.

      An tabbatar da mutum 42 da suka kamu da coronavirus a Kenya. Kasar ta rufe kan iyakokinta sannan ta sanya dokar hana fita ba dare ba rana.

    • Fiye da mutum 154,000 sun warke daga coronavirus

      Alkaluman baya bayan nan sun nuna cewa fiye da mutum 154,000 suka warke daga cutar coronavirus a duk fadin duniya.

      Jami'ar Johns Hopkin, wacce ke bayar da bayani kai-tsaye game da halin da ake ciki a kan cutar, ta kara da cewa sama da mutum 732,000 suka kamu da cutar a duniya.

      A cewarta, mutum 34,686 ne suka mutu sakamakon harbuwa da coronavirus, kuma yanzu haka an fi kamuwa da cutar a Amurka ya zuwa ranar Litinin.

      Ga jerin kasashe goma da suka fi kamuwa da cutar da kuma adadin wadada ta harba ya zuwa Litinin:

      Amurka- 143,055

      Italiya - 97,689

      Spain - 85,195

      China - 82,198

      Jamus - 62,435

      Faransa - 40,723

      Iran - 38,309

      Birtaniya - 19,788

      Switzerland - 15,069

      Belgium - 11,899

    • Labarai da dumi-dumi, Covid-19: Fiye da mutum 800 sun mutu a Spain a kwana daya

      Spain ta bayar da rahoton mutuwar karin mutum 812 sakamakon harbuwa da coronavirus tun ranar Lahadi.

      Jami'ai sun ce an samu fiye da sabbin mutum 6,400 da suka kamu da cutar.

    • Man fetur ya yi faduwar da bai taba yi ba a shekara 18 da suka wuce

      Farashin danyen man fetur ya yi faduwar da bai taba yin irin ta ba cikin shekara 18 da suka wuce a yayin da ake ci gaba da fama da annobar coronavirus.

      Gangar mai samfurin Brent ta fadi zuwa $23.03 kan ko wacce ganga daya ranar Litinin, kuma wannan ita ce faduwa ma fi girma da ya taba yi tun watan Nuwamban 2002.

      Baya ga rashin bukatar danyen man fetur, a farkon watan nan an yi ce-ce-ku-ce kan farashin man fetur tsakanin Saudiyya da Russia.

      Sai dai wai mai sharhi ya ce rashin bukatar danyen man fetur din a matakin da aka dauka na dakile coronavirus shi ne babban abin da ya kawo faduwar farashin.

      Gangar mai samfurin Brent ta fadi zuwa $23.03 a ganga daya ranar Litinin

      Asalin hoton, Getty Images

    • An samu karuwar masu dauke da coronavirus a kasashen Gabashin Afirka

      An samu karuwar mutanen da suka kamu da coronavirus ta kasashen Gabashin Afirka.

      Alkaluman baya bayan nan sun nuna cewa mutum 10 sun kamu da ita a Rwanda ya zuwa Lahadi, inda jumulla ake da mutum 70 - mafi yawa a yankin.

      A cikinsu, mutum shida sun shiga kasar ne daga Dubai, biyu daga Afirka ta Kudu, daya daga Najeriya yayin da dayan kuma ya je daga yankin Gabashin Afirka, a cewar da sanarwar da ma'aikatar lafiyar kasar ta fitar.

      Shugaba Paul Kagame ya yi gargadin cewa za a ci gaba da samun mutanen da za su kamu da cutar a yayin da hukumomi suka ci gaba da gano mutanen da suka yi mu'amala da masu dauke da cutar.

      A halin da ake ciki kasar na cikin mako na biyu na dokar hana fita ta kwana 14 da aka kakaba mata.

      Eritrea ta tabbatar da cewa mutum shida sun kamu da cutar ranar Lahadi, inda jumulla suke da mutum 12 masu dauke da ita. Shida daga cikinsu sun je kasar ne gabanin soma amfani da dkar hana jiragen saman kasashen wajen shiga kasar, a cewar ministan lafiyar kasar.

      Biyar daga cikin masu fama da cutar mata ne masu shekaru tsakanin 32 zuwa 60. Ana bai wa dukkansu kulawa, in ji ma'aikatar lafiyar kasar.

      Kasar ta rufe dukkan makarantu sannan ta haramta shiga motocin haya. Kazalika an haramta taruwar fiye da mutum goma a wuri daya.

      Ranar Lahadi Ethiopia ta sanar da samun sabbin mutum biyar da suka kamu da coronavirus inda jumulla suka kai mutum 21. A jihar Tigray da ke arewacin kasar inda aka sanar da dokar hana fita makon jiya domin dakile cutar, 'yan sanda sun harbe wani mutum har lahira a kokarinsu na tilasta bin dokar hana bude mashaya.

      A kasar Kenya, mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar sun tashi daga 38 zuwa 42 ranar Lahadi. Sabbin mutanen da suka kamu da cutar sun hada da wani dan kasar ta Kenya da Ba'amurke da dan kasar Kamaru da kuma dan kasar Burkina Faso.

      Uganda tana da masu dauke da cutar 33 yayin da a Tanzania ake da mutum 14, ko da yake ba a samu wadanda suka kamu da coronavirus a Burundi da Sudan ta Kudu ba.

      Ba a samu wadanda suka kamu da coronavirus a Burundi da  Sudan ta Kudu ba.

      Asalin hoton, Getty Images

      Bayanan hoto, Ba a samu wadanda suka kamu da coronavirus a Burundi da Sudan ta Kudu ba
    • An saki fursunoni saboda coronavirus a Libya

      Libya ta zamo kasa ta baya bayan nan a Gabas Ta Tsakiya da ta saki fursunoni domin dakile yaduwar coronavirus.

      Gwamnatin kasar wacce kasashen duniya suka amince da ita da ke Tripoli ta bayar da umarnin sakin fiye da fursuna 400.

      Saudiyya ta bayar da umarnin sakin fursuna 250 wadanda aka tsare saboda sun aikata kananan laifuka.

      Bahrain, Masar da kuma Syria dukkansu sun dauki irin wannan mataki. Ita ma Iran, ta saki fursunoni, ko da yake an samu rahotannin da ke cewa fursunoni sun tsere daga gidan yari biyu.

      Amma ba a saki fursunonin siyasa da yawa a kasashen ba.

      Kungiyoyin kare hakkin dan adam da iyalan fursunonin siyasar sun yi kira a sake su.

      Kungiyoyin kare hakkin dan adam da iyalan fursunonin siyasar sun yi kira a sake su

      Asalin hoton, AFP

    • Coronavirus: Ganduje ya ce a yi azumi da addu'o'i

      Gwamnan Kano da ke Najeriya, Abdullahi Umar Ganduje, ya yi kira ga mazauna jihar su yi azumi ranar Litinin domin rokon Allah Ya kawo karshen cutar coronavirus da ta addabi duniya.

      Ko da yake ya zuwa ranar Litinin mutum 111 ne suka kamu da cutar a Najeriya, amma ba a samu bullar ta a Kano ba.

      Hakan ne ya sa gwamnatin jihar ta dauki matakai daban-daban wajen ganin coronavirus ba ta shiga jihar ba, ciki har da yin feshin magani a yankuna da lungunan jihar.

      Ganduje ya yi kiran ne ranar Lahadi a yayin da yake kaddamar da kwamitin mutum 38 da zai bayar da tallafi ga talakawa wadanda za su zauna a gidajensu a matakin dakile yaduwar cutar.

      “Kazalika ina kira da al'ummar wannan jiha da su zage dantse wurin yin addu'o'i a masallatanmu a sallolin farilla biyar kowacce rana da kuma masallatan Juma'a domin ganin an dakile coronavirus daga jiharmu da kasarmu da ma duniya baki daya," in ji Gwamna Ganduje.

      Ganduje

      Asalin hoton, Kano government

    • Covid-19: An rufe babban kantin sayar da magani a Abuja

      Kwamitin da ke sanya ido kan aiki da dokokin yaki da coronavirus a Abuja ya rufe wani babban kantin sayar da magunguna da sauran kayayyaki.

      A sakon da ya wallafa shafinsa na Twitter ranar Litinin, kwamitin ya ce ya rufe kantin H-Medix Supermarket and Pharmacy da ke unguwar Wuse 2 ne saboda ya ki bin dokokin kare kai daga kamuwa da cutar.

      Kauce wa X
      Ya kamata a bar bayanan X?

      Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

      Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

      Karshen labarin da aka sa a X

    • Fiye da mutum 723,000 sun kamu da coronavirus

      Alkaluman da cibiyoyin da ke bibiyar yaduwar coronavirus suka fitar ranar Litinin da safe sun nuna cewa fiye da mutum 723,740 ne suka kamu da cutar a fadin duniya.

      Jami'ar Johns Hopkin, wacce ke bayar da bayani kai-tsaye game da halin da ake ciki a kan cutar, ta kara da cewa mutum 34,018 ne suka mutu, yayin da mutum 152,042 suka warke daga coronavirus ya zuwa safiyar ta Litinin.

      Ga kasashe goman farko da suka fi kamuwa da cutar:

      Amurka - 143,025

      Italiya - 97,689

      China - 82,152

      Spain - 80,110

      Jamus- 62,435

      Faransa - 40,723

      Iran - 38,309

      Birtaniya - 19,784

      Switzerland - 14,829

      Netherlands - 10,930

      Johns Hopkins

      Asalin hoton, Johns Hopkins

    • Coronavirus ta tura Abba Kyari Lagos

      Shugaban ma’aikatan fadar shugaban Najeriya, Abba Kyari, ya koma jihar Lagos domin a sake gwada shi kan cutar coronavirus.

      A wata saarwa da ya fitar ranar Lahadi, Abba Kyari, ya ce yana samun sauki daga cutar amma akwai bukatar a sake gwada shi.

      “Na rubuta wannan wasika ne domin na sanar da ku cewa bisa shawarar likitoci, zan koma Lagos anjima a yau [Lahadi] domin a sake yin min gwaje-gwaje da kuma sanya ido.

      Wannan mataki ne na kula da kai: Ina samun sauki, amma a makon jiya an tabbatar ina dauke da coronavirus, annobar da ta addabi duniya. Na bi umarnin gwamnati na killace kaina.”

      Wannan ne karon farko da Abba Kyari ya bayyana cewa yana dauke da cutar tun bayan da aka bayar da rahotannin cewa yana dauke da ita makon jiya.

      Abba Kyari ya ce yana son samun karin kulawa a Lagos

      Asalin hoton, Nigeria residency

      Bayanan hoto, Abba Kyari ya ce yana son samun karin kulawa a Lagos
    • Barkanmu da warhaka

        • Marubuci, Nasidi Adamu Yahya
        • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa, Abuja

      Nasidi Adamu Yahaya ne daga nan Sashen Hausa na BBC yake yi muku barka da wannan rana ta Litinin.

      Za mu kawo muku labarai da rahotanni kan annobar coronavirus wacce ta addabi duk fadin duniya, ko da yake za mu fi mayar da hankali a kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da makwabta.

      Za ku iya ci gaba da tafka muhawara da bayyana ra’ayoyinku a shafukanmu na sada zumunta a BBC Hausa.