Mutum sama da miliyan daya sun kamu da coronavirus a duniya

Wannan shafin na kawo muku abubuwan da ke faruwa a duniya baki daya dangane da annobar coronavirus.

Rahoto kai-tsaye

Nasidi Adamu Yahaya, Awwal Ahmad Janyau, Usman Minjibir and Umar Mikail

  1. Wadda ta fara kamuwa da coronavirus a Kenya ta warke

    Wata matashiya 'yar kasar Kenya wadda ita ce ta fara kamuwa da cutar coronavirus a kasar ta ce ya warke sumul bayan kwana 23 ana yi mata magani.

    Matashiyar dai ta shaida wa 'yan jarida cewa ta ziyarci Amurka a watan Disambar 2019, amma kuma ta yi zargin cewa ta kamu da cutar ta coronavirus ne a jirginta na komawa kasar tata ne daga birnin London a farkon watan Maris.

    Ta kara da cewa ya kamata mutane su san cewa cutar coronavirus gaskiya ce to amma tana da magani.

    Matashiyar ta kuma ta tattauna da shugaba Uhuru Kenyatta ta kafar intanet.

    Kauce wa YouTube
    Ya kamata a bar bayanan Google YouTube?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da Google YouTube suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Google YouTube da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba. Ana yi samun tallace-tallace YouTube

    Karshen labarin da aka sa a YouTube

  2. Kasashen duniya 7 da ba su san annobar coronavirus ba

    • Sao Tome and Principe
    • Malawi
    • Comoros
    • Lesotho
    • SudanTa Kudu
    • Yemen
    • Koriya ta Arewa
  3. Sakataren tsaron Burtaniya ya warware daga coronavirus

    Wallace

    Asalin hoton, Getty Images

    Sakataren tsaro na Burtaniya, Ben Wallace ya zama mutum na hudu da ya kamu da cutar coronavirus a Burtaniya, inda ya killace kansa a 'yan kwanakin baya.

    Mista Wallace ya ce yanzu haka ya warke kuma yana aiki kamaryadda ya saba.

    Firai minista Boris Johnson da sakataren lafiya, Matt Hancork su ma duk suna can a killace bayan gwajin cutar ya nuna suna dauke da coronavirus din.

  4. Adadin masu dauke da coronavirus ya kai 195 a Ghana

    Jami'ai sun ce mutum uku sun warke daga cutar a Ghana.

    Asalin hoton, Getty Images

    An samu karin mutanen da suka kamu da coronavirus a Ghana lamarin da ya kai adadin masu dauke da cutar a kasar ya kai 195.

    Ministan lafiya Kwaku Agyeman Manu ne ya bayyana hakan a taron manea labarai a Accra, babban birnin kasar anar Laraba.

    Jami'ai sun ce mutum uku sun warke daga cutar a Ghana.

    Kazalika an sallami mutum 49 su je gida su ci gaba da killace kansu har sai an tabbatar sun warke daga coronavirus.

    A gefe guda, jami'an tsaro na can suna farautar wani mai dauke da cutar ta covid-19 bayan ta tsere daga wurin da aka killace ta a Tamale.

  5. An dage gasar Champions League da Europa saboda coronavirus

    Champions League

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar Kwallon Kafa ta Turai, Uefa ta sanar da dage wasannin Champions League da Europa League har sai baba ta gani.

    Shi ma kwamitin wasannin tarayyar ta Turai ya dage dukkanin wasannin kungiyoyin kwallon kafa na kasashen nahiyar da ya kamata su yi wasanni a watan Yuni.

    Hukuncin dai ya ya biyo bayan ganawar da kungiyoyi 55 da ke karkashin Uefa suka yi .

    Dama dai tuni Uefa ta dage gasar maza ta Euro da ya kamata a fara a wannan bazara zuwa 2021 sakamakon annobar coronavirus.

  6. An fara gwajin coronavirus a jihar Ebonyi

    Hukumar yaki da yaduwar cututtuka a Najeriya, NCDC, ta ce an soma gwajin cutar coronavirus a jihar Ebonyi da ke kudu maso gabashin kasar.

    Wata sanarwa da NCDC ta wallafa a shafinta na Twitter ranar Laraba, ta ce an bude dakin gwajin cutar ne a Asibitin Koyarwa na Alex Ekwueme da ke Abakaliki, babban birnin jihar.

    Yanzu an samu dakunan gwajin cutar bakwai kenan a Najeriya, ko da yake har yanzu babu ko daya a arewacin kasar.

    Sai dai NCDC ta ce ana ci gaba da aiki domin samar da dakunan gwajin cutar ta covid-19 a Maiduguri, Kano, Sokoto, Fatakwal, Jos da kuma Kaduna.

    A baya dai, 'yan arewacin Najeriya sun koka kan rashin samar da dakin gwajin coronavirus a yankin nasu.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  7. Coronavirus: Gwamnati na raba wa talakawa kudade a Abuja

    Gwamnatin Najeriya ta fara raba tallafin kudi naira dubu ashirin ga marasa karfi musamman a yankunan karkara daga cikin shirye-shiryenta na tallafi da ake kira Cash Transfer.

    Gwamnatin ta ce tana bada kudin ne domin rage radadin rashi da wasu 'yan kasar ke fama da shi, a wani mataki na yaki da talauci a fadin kasar baki daya musamman wannan lokaci na coronavirus.

    Ministar Ma'aikatar Agaji da Ci Gaban Al'umma, Sadiya Umar Farouk ta shaida wa BBC cewa suna bayar da kudin ne ga masu karamin karfi da suka da hada marayu da masu bukata ta musamman da mata marasa karfi da kuma wadanda mazajensu suka mutu.

    Ta ce dubu biyar ya kamata a bai wa mutanen amma yanzu gwamnati na raba dubu ashirin ne domin rage masu radadi.

    "Tun 2016 gwamnati ta fara raba tallafin ga masu karamin karfi, amma saboda coronavirus, shugaban kasa ya bukaci a ninka wa mutane kudaden zuwa N20,000 maimakon dubu biyar, saboda mutane su samu saukin radadin halin da aka shiga," inji Ministar.

    Ta kuma ce gidaje sama da dubu biyar ne za a bi ana rabawa mutane kudaden a yankin karamar hukumar Kwali a Abuja.

    Ministar ta bayyana cewa sun yi amfani ne da rajistar sunayen mutanen da suka amfana da shirin farko na rage talauci a tsakanin al'umma.

    Sannan kuma an ninka tallafin ne domin sake rage musu radadin wahalhalun tattalin arziki da za su shiga sakamakon dokar hana fita domin yaki da coroinavirus.

    Bayanan sautiRahoton Buhari Muhammad Fage
  8. Coronavirus: Alkaluman wadanda ke mutuwa na karuwa a Burtaniya

    Jumullar mutum 2,352 sun mutu sakamakon cutar coronavirus a Burtaniya, inda hakan ke nufin alkaluman mamatan sun karu da 563 daga ranar Talata.

    Sashen kula da lafiya na Burtaniya ya an yi wa mutum 152,979 gwajin coronavirus ya zuwa karfe 9 na safiyar ranar Larabar nan, inda mutum 29,474 ke dauke da cutar.

    Burtaniya dai na daya daga cikin kasashen duniya da annobar cutar ta coronavirus ke kisan jama'a masu dama.

  9. Covid-19: An saki dubban fursuna a Algeria

    Algeria ta kasance kasa ta baya bayan nan a Afirka da ta saki fursunoni a kokarin hana yaduwar coronavirus.

    Shugaba Abdelmadjid Tebboune ya yi afuwa ga fursuna kusan 5,000 wadanda saura wata 18 ko kasa da haka su kammala wa'adin zaman gidan yari.

    Ita ma Ethiopia ta saki dubban fursuna daga gidan yari.

  10. Covid-19: Gwamnatin Kaduna ta sassauta dokar hana fita

    Gwamnatin Kaduna da ke arewacin Najeriya ta ce za ta sassauta dokar hana fita da ta kakaba wa mazauna jihar saboda hana yaduwar coronavirus.

    A sakon da gwamnatin ta wallafa a shafinta na Twitter ranar Laraba, ta ce an sassauta dokar daga karfe uku na ranar Laraba, 1 ga watan Afrilu zuwa ranar Alhamis, 2 ga watan na Afrilu, 2020.

    Ta ce ta dauki matakin ne domin bai wa mazauna jihar damar sayen kayan abinci da sauran kayayyaki.

    Mutum uku ne suka kamu da covid-19 a Kaduna, ciki har da gwamnan jihar Nasiru El-Rufai.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  11. Mutum 233 sun kamu da Covid-19 a Kamaru, Daga Bongben Jisi, wakilin BBC Pidgin a Kamaru

    Ministan lafiyar Kamaru, Manaouda Malachie, ya tabbatar cewa mutum 233 ne suka kamu da kwayar cutar coronavirus a kasar.

    An samu karin mutum 10 da suka kamu da cutar ranar Laraba daga cikin mutum 81 da aka yi wa gwaji, inda jumulla yanzu ake da mutum 233, a cewar ministan.

    Ya shawarci 'yan kasar su rika daukar matakan kare kansu, ciki har da rufe hanci sannan su rika kula da tsafta.

    Ranar Talata, Kamaru ta tabbatar da karin mutum 81 da suka kamu da cutar, sannan aka samu mutum 30 a daren, yayin da aka samu karin mutum 51 da safe.

    Manaouda ya ce galibin mutanen da ke dauke da cutar, wadanda suka koma kasar daga kasashen waje ne.

  12. Halin da ake ciki a duniya dangane da coronavirus

    Coronavirus

    Asalin hoton, Getty Images

    Spaniya tana rasa mutum 864 a kullum, inda mutum fiye da 9,000 suka mutu a kasar sakamakon coronavirus.

    Yawan mutanen da suka mutu a Iran sun ya zarta 3,000, bayan da aka samu karin mutuwar 138 a awanni a 24.

    Yanzu haka akwai fiye da mutanen da suka harbu da cutar ta coronavirus fiye da 800,000 a fadin duniya.

  13. Somalia ta haramta ninkaya saboda Covid-19

    Hukumomi a Mogadishu, babban birnin Somalia sun haramta yin ninkaya a fitaccen wurin shakatawar nan na Lido a kokarin da suke yi na hana yaduwar coronavirus.

    An bukaci otal-otal da gidajen abinci da ke kusa da wurin shakatawar su tabbatar da bin ka'idojin kare tsafta kan yadda za a kare mutane daga kamuwa da cutar.

    Galibin wurin shakatawar yana cike da jama'a da rana ko kuma a karshen mako.

    Somalia, wacce ke murmurewa daga yakin basasa, ta tabbatar da mutum uku da suka kamu da Covid-19, ko da yake ana fargabar idan cutar ta yadu za ta iya fin karfin ma'aikatan lafiyar kasar.

    Galibin wurin shakatawar yana cike da jama'a da rana ko kuma a karshen mako

    Asalin hoton, Getty Images

  14. Yarima Charles ya nuna kansa a karon farko

    Yarima Charles mai jiran gadon sarautar Birtaniya ya fito ya nuna kansa a karon farko bayan ya warke daga cutar coronavirus.

    Yariman na Wales a cikin wani bidiyo da aka wallafa a Twitter ya yi kira ga mutane su yi fatan samun’ kyakkyawan lokaci.’

    Ya ce killacewa ya kawo karshe, amma ya yi gargadin cewa bayar da tazara tsakanin juna, sabon al’amari ne da ba ya da dadi

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  15. Mutum 800,000 ke dauke da coronavirus a duniya

    Yanzu mutum 800,000 ke dauke da cutar coronavirus a fadin duniya.

    Duk da cewa cutar ta fara barkewa ne a China a bara, amma yanzu ta bazu sassan duniya, kuma yanzu ta fi yaduwa a Turai fiye da China.

    Yanzu cutar coronavirus ta fi yaduwa a kasashen Spain da Italiya da Jamus da Amurka inda aka fi yawan masu dauke da ita.

    Ta yaya zan kare kaina?

    Abin da ya fi kamata a yai shi ne yawan wanke hannu da ruwa da sabulu.

    Coronavirus tana yaduwa ne idan mutum da ke dauke da ita ya yi tari har kwayoyin cutar suka yadu a cikin iska.

    Da zarar wani ya shaki isakar ko kuma ya taba wajen da kwayoyin cutar suka fada akai, sannan ya taba idonsa ko hancinsa ko bakinsa, to zai iya kamuwa.

    Don haka yin tari da atishawa a cikin toli fefa, da gudun taba fuskarku da hannayen da ba a wanke ba, da kuma gujewa yin alaka ta kut da kut da mutanen da suka kamu na da matukar muhimmanci wajen hana yaduwar cutar.

    Kwararru a fannin lafiya sun ce takunkumin rufe fuska ba ya tasiri sosai wajen kariya.

    Hanyoyi kariya daga coronavirus
  16. Kasar da aka haramta kalmar 'coronavirus'

    Turkmenistan ba kasar da ake jin labarinta ba ce a-kai-a-kai - an fi saninta da gwamnatin kama-karya da kuma arzikin iskar gas mai dumbin yawa.

    Sai dai kasar, wadda ke tsakiyar nahiyar Asiya, ta tsaurara mataki game da amfani da kalmar 'coronavirus'; hasali ma an haramta amfani da ita kwata-kwata a kasar.

    Tuni kafar yada labaran kasar ta daina amfani da kalmar sannan aka cire ta daga takardun bayanan lafiya, a cewar rahoton kungiyar Reporters Without Borders (RSF).

    'Yan sanda a kasar za su iya kama mutanen da suka sanya takunkumin rufe fuska ko kuma suke yin hira a kan kalmar ta coronavirus.

    Turkmenistan na daya daga cikin kasashen duniya da ba a sanin halin da take ciki.

    Gwamnati tana da cikakken iko kan kafafen yada labarai na kasar sannan kuma ta rufe shafukan intanet na kafafen watsa labarai na kasashen waje (kamar na BBC) a kasar.

    Zuwa yanzu kasar ba ta bayar da rahoton bullar cutar a kasar ba, amma makociyarta Iran tana da mutum sama da 47,000 da suka kamu.

    Shugaban Turkmenistan Gurbanguly Berdimuhamedow

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Shugaban Turkmenistan Gurbanguly Berdimuhamedow
  17. Labarai da dumi-dumi, Karin mutum 12 sun kamu da coronavirus a Nigeria

    An samu karin mutum 12 da suka kamu da coronavirus a Najeriya.

    Hukumar NCDC mai yaki da yaduwar cutuka a kasar ta ce tara daga cikinsu a Jihar Osun suke, biyu a Edo da kuma daya a Ekiti.

    Ya zuwa karfe 12:30 na ranar Laraba, mutum 151 ne suka kamu da cutar coronavirus a Najeriya, tara daga ciki sun warke, sannan biyu sun mutu.

    Jihohi 11 ne cutar ta bulla kamar haka:

    Legas - 82

    Abuja - 28

    Osun - 14 Oyo- 8

    Ogun - 4

    Edo - 4

    Kaduna - 3

    Enugu - 2

    Bauchi - 2

    Ekiti - 2

    Rivers -1

    Benue - 1

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  18. Coronavirus: Mata ta yi amfani da robar ruwa a matsayin takunkumin kariya

    Wani dan siyasa a Kenya ya yi kira a nemo masa wata matashiya da aka dauko hotonta tana amfani da gora domin rufe hancinta a matsayin kariya daga kamuwa da coronavirus.

    An ga wasu daga cikin mutanen da ke cikin hoton, wanda ya watsu a shafukan intanet, suna sanye da takunkuman rufe fuska.

    Gwamnan Nairobi Mike Sonko ya wallafa sako a Twitter yana mai cewa hoton ya "sosa masa rai".

    Mutane da dama da suka yi tsokaci a kan hoton sun ce an dauke shi ne a birnin Mombasa da ke gabar teku.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  19. Covid-19: Bayanan baya-bayan nan daga yankin Asiya

    Mata guda biyu

    Asalin hoton, Getty Images

    • A India, akalla mutum 140 ne ake zargin sun kamu da coronavirus daga wani taron addini a unguwar Nizamuddin da ke birnin Delhi. Hukumomi na bin sawun dubban mutanen da suka halarci taron wanda wata kungiyar Musulmi mai suna Tablighi Jamaat ta shirya - nan ne ya fi ko ina yawan masu dauke da cutar a Indiya a yanzu.
    • A Pakistan, an mayar da wani filin taro zuwa asibitin sha-ka-tafi mai gado 1,000 a cikin kwana tara a garin Lahore. Garin yana cikin yankin Punjab ne, wanda ya fi fuskantar matsi daga cutar.
    • Gwamnatin kasar Malaysia ta nemi afuwa bayan ma'aikatar mata ta kasar ta wallafa wani zanen barkwanci a intanet tana kira ga matan aure da su yi kwalliya, su cakare sannan su daina bata wa mazajensu rai yayin dokar zaman gida da aka saka a kasar.
  20. Covid-19: Gwamnatin Kaduna ta soma raba kayan abinci

    Gwamnatin Jihar Kaduna da ke Najeriya ta ce ta soma raba kayan abinci ga marasa galihu a yayin da aka bukaci mutane su zauna a gidajensu domin hana yaduwar coronavirus.

    A sakon da gwamnatin jihar ta wallafa a shafinta na Twitter ranar Laraba, ta ce ta dauki matakin raba kayan abincin ne domin rage radadin da mutane suke ciki sakamakon hanin da aka yi musu na fita daga gidajensu.

    Ta yi kira ga masu hali su tallafa wa marasa hali da abinci.

    Mutum uku ne suka kamu da covid-19 a Kaduna, ciki har da gwamnan jihar Nasiru El-Rufai.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X