Rundunar sojin Najeriya ta dauki matakai kan Covid-19
Rundunar sojin Najeriya ta ce ta dauki matakai daban-daban a bariki-bariki 19 da ke fadin kasar domin hana yaduwar cutar coronavirus.
Sanarwar da mai magana da yawun rundunar, Kanar Sagir Musa, ya aike wa manema labarai ranar Talata ta ce matakan da ta dauka sun hada da samar da abubuwan wanke hannu da man wanke hannu na sanitizer da kuma auna yanayin zafin jikin ma'aikatanta a bariki-bariki.
"Alal misali, hedikwatar rundunar soji wacce ke kulawa da lafiya da ke Victoria Island Lagos ta dauki matakai domin dakile cutar kamar yadda hafsan sojin kasa Laftanar Janar Tukur Yusufu Buratai ya yi umarni.
Ma'aikatan lafiya a Bonny Cantonment sun zage dantse wurin tantance mutanen da ke shiga da fita daga bariki ta hanyar gwada yanayin zafin jikinsu da kuma tabbatar da cewa sun wanke hannuwansu da zummar hana kamuwa da cutar," in ji Kanar Musa.
Sanarwar ta kara da cewa rundunar za ta ci gaba da tabar da tsaftar jami'anta da sauran ma'aikata a yunkurin hana kamuwa da coronavirus.

Asalin hoton, Nigeria Army

Asalin hoton, Nigeria Army


















