Yadda 'yan bindiga suka kone mutane a Katsina
Wasu 'yan bindiga sun kai hari a garuruwa biyu na yankin karamar hukumar Batsari ta jihar Katsina da ke arewacin Najeriya.
Ganau sun shaida wa BBC cewa 'yan bindigar sun hallaka mutane da dama kuma sun banka wa gidaje wuta a kauyukan Dankar da Tsanwa.
SP Gambo Isa, jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar, ya tabbatar wa BBC faruwar lamarin yana mai cewa an kai hare-haren ne da yammacin Juma'ar da ta gabata.
Ya ce gaba daya mutane akalla talatin ne suka mutu a tagwayen hare-haren.
Wani ganau da ba ya so a bayyana sunansa ya shaida wa BBC cewa "cikin garin Dankar abin da na gani mutum takwas aka kashe."
Ya kara da cewa maharan basu kyale marasa lafiya da ke kwance a asibiti ba don kuwa sun je har wani asibiti a Dankar sun harbe masu jinya.
Za ku iya karanta cikakken rahoton a nan: Yadda 'yan bindiga suka kashe mutum 30 a Katsina