Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da suka faru a Najeriya da Nijar da sassan duniya

Wannan shafin yana kawo muku labarai da rahotannin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi da ma wasu sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Nasidi Adamu Yahaya and Nabeela Mukhtar Uba

  1. Rufewa

    A nan kuma kawo karshen labarai da rahotannin da muke kawowa kai tsaye a wannan shafin.

    Sai kuma ranar Litinin idan Allah ya kai mu da za mu ci gaba da kawo wasu labarai da rahotannin.

    Za ku iya duba kasa domin ganin irin wainar da aka toya a Najeriya da sassan duniya yau Juma'a.

  2. Hotuna: Buhari ya gana da shugaban Burkina Faso

    Shugaban Najerita Muhammadu Buhari ya gana da shugaban Burkina Faso Mr Roch Kabore.

    Shugaba Kabore ya ziyarci Buhari ne a fadarsa da ke Abuja, babban birnin kasar.

    Mai taimaka wa Buhari kan kafafen sada zumunta, Bashir Ahmad ne ya wallafa hotunan haduwar shugabannin a Twitter.

  3. 'Gara a bar daliban kenya a Wuhan'

    Mai magana da yawun gwamnatin Kenya, ya ce gara a bar daliban kasar da ke China a can, saboda a rage hadarin yaduwar cutar coronavirus a Kenyan.

    Mr Cyrus Oguna, ya ce gwmnatin kasar ta aika wa dalibanta da ke China kudin da ya kai fiye da dala 108,728 domin su ciyar da kansu.

    Ya kara da cewa, ofishin jakadancinsu da ke Beijing a yanzu haka na kula da wasu mata masu juna biyu guda 2 a birnin.

    Ya ce har yanzu ana duba yiwuwar dawo da daliban, amma ya danganta da abin da aka tattauna a kai.

    Akwai dai 'yan Kenya kusan 100 a China, kuma 91 daga cikinsu dalibai ne.

  4. Za a yi zaben shugaban kasa a Togo ranar Asabar

    Masu kada kuri'a a Togo za su yi zaben shugaban kasa a ranar Asabar.

    Shugaban da ke kan mulkin kasar Faure Gnassingbé, zai kara da abokan hamayya shida ciki har da babban abokin hamayyarsa Jean-Pierre Fabre.

    Za dai a bude rumfunan zabe ne da misalin karfe 7 na safe agogon kasar.

    Fiye da masu kada kuri'a miliyan 3 da dubu dari biyar ne suka yi rijistar zabe.

    A karon farko, za a bai wa 'yan kasar da ke zaune a wasu kasashe damar zabe, koda yake mutum 300 ne kadai suka iya yin rijistar kuri'arsu.

    Mr Gnassingbé, na jam'iyya mai mulki na neman kujerar ne a karo na hudu.

    A bara ne kundin tsarin mulkin kasar ya ba wa shugaban kasar damar sake tsayawa takara abin da ya janyo gagarumar zanga-zanga a kasar.

    Iyalan Mr Gnassingbé ne dai suke mulkin kasar tsawon shekara 50.

  5. An yi bikin auren makafi a Somalia, Daga Bella Hassan BBC News Somali

    Tawagar wasu sabbin ma'aurata - angwaye hudu da amarensu - dukkansu makafi sun yi aure a wani bikin hadaka da aka yi a Mogadishu, babban birnin Somalia.

    Angwayen hudu da daya daga cikin amaren sun yi gwagwarmaya wajen tara kudin bikin auren.

    A al'adance, iyalai a Somalia ne ke tara kudi domin gudanar da bikin aure amma a wannan karon an samu kamfanoni da suka bayar da tallafi.

    Daya daga cikin amaren Samira ta shaida wa BBC cewa akwai kalubale wajen samun miji kuma ta fuskanci matsala wajen hada kudin gudanar da bikin.

    Amma Samira ta shawarci mutane masu bukata ta musamman da kada su yanke kauna da samun abokan rayuwa.

    Angonta, Maslah Ali, ya fada wa BBC abin da ya ja hankalinsa game da matarsa.

    ''Na fara sonta a lokacin da nake koyar da ita. Daliba ce mai jajircewa kuma wata rana za ta zama uwa ta gari ga 'ya'yanmu,'' a cewarsa.

  6. Shugaba Buhari ya karbi bakuncin Doctors Without Borders

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin tawagar kungiyar likitoci ta Doctors Without Borders ranar Juma'a a fadarsa da ke Abuja, babban birnin kasar.

    Kungiyar ta yi fice wurin gudanar da ayyukan agaji da jinkai a duk fadin duniya.

    Fadar shugaban kasar ta wallafa wani hoton bidiyo a Twitter da ke nuna yadda shugaban yake musabaha da mambobin kungiyar.

    Kungiyar ta samu jagorancin Dr Christos Christou, shugaban kungiyar na duniya.

    Ga kuma wasu hotuna daga ganawar da suka yi.

  7. Sojin Faransa sun kashe 'yan ta'adda 50 a Mali

    Rundunar sojin Faransa ta ce ta kashe kimanin 'yan IS 50 a Mali.

    Ta ce daya daga cikin wadanda suka mutu dan kungiyar IS ne reshen yankin Sahel.

    Faransa ta ce ta kwace makamai tare da lalata babura kusan 30 a samamen da ta kai a tsakiyar birnin Mopti.

    An dai yi amfani da jiragen yaki da jirage masu saukar ungulu wajen kai samamen.

    An samu karuwar hare-haren ta'addanci a Mali da Burkina Faso da kuma Nijar.

    Sama da sojojin Faransa 5,000 ne ke zaune a yankin.

  8. Ana zaben 'yan majalisa a Iran

    Iraniyawa na kada kuri'a a zaben 'yan majalisar dokoki, wanda da alama zai ba wa manyan makusantan jagoran juyin juya halin kasar Ayatollah Ali Khamenei damar sake karfafa siyasar su.

    A yayin da yake jefa kuri’ur sa, Ayatollah Khamenei, ya yi kira ga jama’a su fita rumfunan zabe da wuri don kada kuri'a domin tabbatar da cimma bukatun kasar.

    Masu sukar jagorancinsa, sun yi kira da a kauracewa zaben, bayan hana masu sassaucin ra’ayi tsayawa takara.

  9. EFCC ta kama kwamishina a jihar Kano saboda zargin almundahana

    Hukumar yaki da masu yi wa arzikin kasa ta'annati a Najeriya EFCC, ta ce ta kama kwamishinan ayyuka na musamman a jihar Kano.

    A shafinta na Twitter EFCC ta ce ta kama Mukhtar Ishaq Modibbo ranar Alhamis bisa zarginsa da almundahanar N76m.

    Ana zarginsa da karkatar da wasu kudade mallakin karamar hukumar birni a lokacin da yake shugaban karamar hukumar.

  10. An ware N9.3 bn don hana ba-haya a kwararo a Ekiti

    Gwamantin jihar Ekiti da ke kudu maso yammacin Najeriya ta ware N9.3bn domin yaki da masu yin ba-haya a kwararo.

    Jaridar Vanguard ta ambato gwamnan jihar Kayode Fayemi yana cewa za a yi amfani da kudin wajen gina gidajen ba-haya a fadin jihar.

    Gwamna Fayemi ya kara da cewa jami'an lafiya za su soma zagaya wa gida-gida domin su tabbatar an bi dokar haka masai akalla guda daya a kowanne gida.

    Rahotanni sun ambato ministan albarkatun ruwan Najeriya, Suleiman Adamu, wanda ya halarci taron, yana bayyana dabi'ar 'yan kasar ta yi ba-haya a waje a matsayin abin kunya.

    A shekarar da ta wuce, majalisar dinkin duniya ta ayyana Najeriya a matsayin kasa ta biyu da aka fi yin ba-bahaya a waje.

  11. Ana bita kan cutar numfashi ta covid-19 a Najeriya

    Rahotanni daga Najeriya na cewa an fara wani taron bita don horar da jami`an kiwon lafiya daga nahiyar Afirka a kan hanyoyin kare kai daga harbuwa da cutar numfashi ta covid-19 da aka fi sani da coronavirus.

    Akalla jami`an lafiya daga kasashe talatin da biyar ne suke halartar bitar, wadanda ake sa ran za su koma gida su horar da takwarorinsu.

    Cibiyar da ke yaki da yaduwar cututtuka ta Najeriya ce ta shirya bitar tare da hadin-gwiwa da babbar cibiyar ta nahiyar Afirka da kuma kungiyar tarayyar turai da wasu kungiyoyi.

  12. Rakuman Australia sun kubuta daga hari a Libya

    An kwashe rakumi 3,000 da aka shigar da su Libya daga tashar jirgin ruwa da ke Tripoli bayan da kai harin makamin roka.

    Babban birnin Libya, Tripoli shi ne inda gwamnatin kasar mai samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya take, kuma tana fuskantar hare-hare kusan tsawon shekara daya daga dakarun Janar Khalifa Haftar wanda suka mamaye gabashin kasar.

    Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya rawaito cewa an debe rakuman daga tashar cikin daren Laraba zuwa birnin Zawiya da ke da nisan kilomita 45.

    Sai dai an sace wasu rakuman a kan hanya a cewar Reuters.

    Wasu rahotannin na cewa wata kungiyar 'yan ta'adda ta kwace rakuma 125 lokacin da suke wucewa ta Janzour da ke wajen Tripoli.

    An kuma yada hotunan rakuma masu yawa yayin da suke barin Tripoli a kafafen sada sumunta.

  13. Mai goyon bayan IS ta tabbatar da shirya harin kunar bakin wake kan majami'a

    Wata mai goyon bayan kungiyar ta'addanci ta IS ta ce ta shirya kashe kanta a harin kunar bakin wake kan Majami'ar St Paul.

    Safiyya Shaikh, 'yar shekara 36 daga Hayes a yammacin London, ta yarda da shirya ta'addanci ta hanyar tambayar wani jami'in leken asiri da ya samar da bama-bamai.

    Sama da wata biyu kafin kama ta, Shaikh ta kulla alaka da wasu jami'an leken asiri da suke bayyana kansu a matsayin miji da mata masu tsattsauran ra'ayi.

    Masu gabatar da kara sun ce ta ba da jaka biyu da take so a cika su da bama-bamai.

  14. Shugabannin Rwanda da Uganda sun yi musabaha a iyakar Gatuna, Daga Ferdinand Omondi BBC News, Nairobi

    Shugaba Yoweri Museveni na Uganda da Paul Kagame na Rwanda sun isa iyakar Gatuna gabanin tattaunawarsu kan daidaita alakar kasashen biyu.

    Ana fatan shugabannin biyu za su sa hannu kan wata yarjejeniya da za ta ba da damar yin musayar masu laifi da ake nema.

    Shugaban Angola João Lourenço da Félix Tshisekedi na Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo su ma sun halarci wajen domin taimakawa wajen kulla yarjejeniyar.

    Ganawar na zuwa ne bayan da gwamnatin Rwanda ta saki 'yan Uganda 20 da suka kammala hukuncin da aka yanke musu a kan tuhume-tuhume daban-daban da suka hada da shiga kasar ba bisa ka’ida ba.

    A wannan makon, Uganda ta saki 'yan Rwanda 13 wadanda ke tsare bisa tuhumar satar bayanai da kuma wasu laifuffuka da suka shafi tsaro.

  15. An gano gawar dan sandan da ke gadin mataimakin shugaban kasa

    Wani dan sandan Kenya wanda ake sa ran zai bayar da shaida game da badakalar sayo makaman soji da ta kai ta $395m, wadda aka yi ta tsakaci a kanta, ya mutu. An ga gawarsa ne a gidansa da ke, Nairobi, babban birnin kasar.

    An ga harbin bindiga a goshin Sajan John Kipyegon Kemei, wanda ya yi aiki a ofishin mataimakin shugaban kasar, William Ruto.

    Kafafen watsa labaran kasar sun ruwaito cewa dan sandan yana aiki ranar da tsohon ministan kasar ta Kenyan ya ziyarci ofishin mataimakin shugaban kasar tare da rakiyar wasu daraktoci daga wani kamfanin Amurka domin tattaunawa kan cinikin makamai.

    Tuni dai aka tuhumi tsohon minsitan, Rashid Echesa, da laifin yin jabun takardun kwangila.

    Kamfanin na Amurka Eco Advanced Technologies ya yi zargin cewa Mr Echesa ya mika musu yarjejeniyar kwangila ta jabu domin samar wa sojin Kenya makamai, yana mai zarginsa da damfarar su kusan $113,727 (£88,204).

    An bayar da belin Mr Echesa bayan ya musanta zargin.

  16. Najeriya ta nemi Amurka ta janye hanin ba da biza

    Ministan cikin gida na Najeriya, Ogbeni Aregbesola, ya bukaci Amurka ta soke hanin da ta yi mata na bai wa 'yan kasar bizar shiga kasarta.

    A ranar Juma'a ne hanin zai fara aiki kan 'yan kasashen Najeriya da Myanmar da Eritrea da Kyrgyzstan da Sudan da kuma Tanzania.

    Jama'ar kasashen ba za su samu bizar Amurka ba da za ta iya ba su damar samun takardar izinin zama a kasar na din-din-din.

    Ministan ya yi rokon ne lokacin da jakadan Amurka a Najeriya ya ziyarce sa ranar Laraba kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Twitter.

  17. Shugaban da ake zargi da kisan matarsa ya fice daga kasarsa

    Firai ministan Lesotho Thomas Thabane ya ki bayyana a gaba kotu inda ake tuhumarsa da laifin kisan tsohuwar matarsa a shekarar 2017.

    Wani mai taimaka wa firai ministan da kuma dansa sun ce Mr Thabane, mai shekara 80 yana Afirka ta Kudu inda yake jinya.

    Tuni dai aka tuhumi matarsa ta yanzu Maesaiah Thabane da laifin kisan kai.

    Mr Thabane shi ne shugaba nna farko a kasar Kudancin Afirka da ake zargi da ake zargi da kisan kai yana kan mulki, a wani lamari da ya girgiza 'yan kasar.

    Bai ce komai a kan zargin ba.

  18. Ra'ayoyin 'yan Ghana kan jawabin shugaban kasar

    Al'ummar kasar Ghana na cigaba da bayyana ra'ayoyinsu dangane da jawabin shekara shekara da Shugaban kasar Nana Akufo Ado ya gabatar a gaban majalisar dokoki.

    Ya gabatar da jawabin a kan yanayin da kasar take ciki karo na hudu kuma na karshe a wa'adin mulkin sa na farko.

    Sai dai marasa rinjaye a majalisar dokokin sun kauracewa bayanin.

    Shugaban ya tabo batutuwa da dama da suka shafi tsaro da tattalin arziki da faduwar darajar sidi da yaki da cin hanci da rashawa da hako ma'adinai ta haramtacciyar hanya da kuma durkushewar wasu manya da kananan bankuna.

  19. PDP ta zargi gwamnatin Buhari da hana Oshimhole fuskantar shari'a

    Jam’iyyar PDP mai adawa a Najeriya ta zargi gwamnatin APC mai mulki kan jan kafa wajen kama shugaban jam’iyyar na kasa Adams Oshimhole bisa abin da ta ce kalaman tunzura magoya baya.

    PDP ta ce kalaman sun sa magoya bayansu sun kai wa Mai shari'ah Mary Odili hari saboda hukuncin kotun koli kan zaben gwamnan jihar Bayelsa.

    'Yan adawan sun zargi APC da kitsa kai hari a kan Mai shari'ar ta hanyar yin amfani da 'yan bangar da suka kai hari kan gidan sabon gwamnan jihar Bayelsa da kona sakatariyar PDP a jihar da kuma far wa gidan rediyon jihar.

  20. Masu 'ra'ayin rikau' na shirin lashe zaben majalisar dokokin Iran

    'Yan kasar Iran suna kada kuru'unsu a zaben'yan majalisar dokokin da aka yi amannar cewa masu tsattsauran ra'ayin da ke goyon bayan shugaban addinin kasar ne za su yi nasara.

    Shi ne karon farko da za a gudanar da zabe tun bayan da Amurka ta sake kakaba wa kasar sabbin takunkumai saboda shirinta na samar da makamashi da ke amfani da nukiliya, lamarin da ya gigita tattalin arzikin kasar.

    An hana dubban masu tsaka-tsakin ra'ayin addini fafatawa a zaben saboda rashin cika tsauraran ka'idojin da aka shimfida.

    Masu sanya ido sun ce hukumomin kasar na fatan mutane za su fito sosai su kada kuri'unsu saboda sun nuna wa duniya cewa 'yan kasar suna goyon bayan gwamnati.

    Masu sukar shugabannin Iran sun yi kira ga 'yan kasar su kaurace wa zaben domin bijirewa abin da suka kira take hakkin dan adam da rashin bari a fadi albarkacin baki a kasar.