Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da suka faru a Najeriya da Nijar da sassan duniya

Wannan shafin yana kawo muku labarai da rahotannin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi da ma wasu sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Nasidi Adamu Yahaya and Nabeela Mukhtar Uba

  1. Dan bindiga ya kashe mutane da dama a Jamus

    Wani dan bindiga ya bude wuta a wurare biyu da ake sayar da shisha a birhin Hanau da ke Yammacin Jamus, inda ya kashe akalla mutum takwas kana ya jikkata mutane da dama, a cewar 'yan sanda.

    A dukkan wuraren biyu da aka kai wa hari ranar Laraba, rahotanni sun ce akasarin masu zuwa mashayar Kurdawa ne.

    An gano gawar mutumin da ake zargi da kai harin a gidansa tare da gawar mahaifiyarsa.

    Masu shigar da kara na gwamnatin tarayya sun ce harin na ta'addanci ne, yayin da jami'ai suka ce akwai shaidun da ke nuna cewa maharin mai tsattsauran ra'ayi ne.

    'Yan sanda sun ce mutumin da ake zargi da kai harin ya harbe kansa.

    Jaridar The Bild ta ruwaito cewa mutumin dan kasar Jamus ne wanda aka bai wa lasisin amfani da makamai, tana mai cewa an gano harsasai da jigidar bndiga a cikin motarsa.

  2. An kama dan sanda a kan kisan dan achaba

    An kama wani dan sandan kasar Kenya bisa hannu a kisan wani dan achaba a Nairobi, babban birnin kasar.

    Ana sa ran gurfanar da dan sanda, wanda har yanzu ba a bayyana sunansa ba, a gaban kuliya ranar Alhamis.

    Ana zarginsa da hannu a kisan Daniel Mburu, wanda ya kai dansa da ya kusa nutsewa a ruwa asibiti domin ba shi kulawar gaggawa.

    Wasu mutane sun bi Mr Mburu da gudu saboda ya shiga da babur dinsa bangaren kula da masu larurar gaggawa na asibitin, kuma an kira 'yan sanda su sa baki bayan an yi hatsaniya da shi.

    Lokacin da suke ce-ce-ku-ce ne aka harbe shi a kirji lamarin da ya yi sanadin mutuwarsa.

  3. Kotu ta hana fitar da 'yan China daga Kenya

    Wata kotu a Kenya a dakatar da fitar da 'yan China hudu daga kasar, duk kuwa da cewa an gano su cikin wani bidiyo suna yi wa wani dan kasar Kenya bulala.

    A makon jiya ministan harkokin gida Fred Matiang ya sanya hannu kan wata takarda da ta umarci jami'an tsaro su fitar da 'yan kasar ta China daga Kenya.

    Sai dai kotun ta yi umarni a kara tsare su tsawon kwana 15. Amma ba a tuhume su da aikata laifi ba.

    An kama mutanen hudu ne ranar tara ga watan Fabrairu bayan jami'an tsaro sun kai samame a wurin sayar da abinci mai suna Chez Wou Restaurant da ke Kileleshwa a wajen birnin Nairobi.

    An yi zargin cewa sun yi wa dan kasar Kenyan bulala ne saboda ya yi jinkirin zuwa aiki.

  4. Za a yi wa ‘yan Boko Haram ruwan addu’o'i

    Gwamnan jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya ayyana ranar Litinin 24 ga watan Fabrairun 2020 a matsayin ranar da za a gudanar da azumi da addu'o'i domin neman sauki kan Boko Haram.

    Ya bayyana haka ne yayin wani jawabi na minti shida da ya yi wa jama'ar jihar a ranar Laraba.

    Sai dai gwamnan ya ce ba wai ranar hutu ba ce domin za a je aiki a ranar Litinin din.

    Ya bayyana cewa wasu za su ga wannan lamarin kamar wani sabon salo, amma hakan ya zo ne sakamakon kiraye-kirayen da jama'a ke yi na yin azumi da addu'o'i.

    Karanta cikakken labarin a nan: Mutanen Borno za su yi azumi kan Boko Haram.

  5. Budewa

    Sashen Hausa na BBC ne yake yi muku barka da warhaka. Da fatan zaku kasance tare da mu tsawon wannan rana domin sanin halin da duniya ke ciki, musamman ma abubuwan da ke aukuwa a Najeriya da Nijar da makwabtansu, har ma da wasu sassan duniya. Kada ku manta za ku iya bibiyarmu a shafukan sada zumunta da muhawara. Mun gode

  6. Rufewa

    A nan muka kawo karshen labarai da rahotannin da muke kawowa kai tsaye a wannan shafin.

    Sai kuma ranar Alhamis idan Allah ya kai mu muke fatan dawowa domin ci gaba da kawo wasu sabbin labarai da rahotannin.

    Idan kuka duba kasa, za ku ga abubuwan da suka faru a Najeriya da sassan duniya yau Laraba.

  7. Birtaniya na son kulla alakar kasuwanci da kamfanin Dantata

    Jakadar Birtaniya a Najeriya, Miss Catriona Laing, ta jagoranci wata tawaga ta jami'an gwamnatin Birtaniyar kai ziyarar hadin gwiwa ga kamfanin Dantata Foods and Allied Products.

    Catriona ta je Kano ne don karfafa dangantakar Birtaniya da gwamnati da masu hannun jari da nufin habaka alakar kasuwanci da tattalin arziki tsakanin ƙasashen ta hanyar 'yan kasuwa masu zaman kansu.

    Ziyarar na zuwa ne bayan taron habaka kasuwanci da tattalin arziki tsakanin Birtaniya da Afirka da aka gudanar a Janairun 2020 a birnin London.

    Bayanin na kunshe ne cikin sanarwar da shugaban kamfanin na Dantata Foods and Allied Products.

  8. Kotu ta bayar da umarnin mayar wa Dasuki fasfonsa

    Wata babbar kotu da ke Maitama a Abuja, babban birnin Najeriya ta bayar da umarnin mayar wa tsohon mai bai wa shugaban kasa shawara kan lamuran tsaro, Kanar Muhammad Sambo Dasuki mai ritaya fasfonsa.

    Kotun karkashin alkali Hussein Baba-Yusuf ce ta umarci magatakardan kotun da ya mika wa Dasuki fasfo din ta hannun lauyansa domin sabunta takardar saboda wa'adinsa ya riga ya cika tun bayan da kotu ta kwace fasfo din.

    Umarnin kotun zai bai wa Dasuki damar samun biza domin zuwa asibiti bayan shekara hudu da ya yi tsare a hannun hukuma.

    Dasuki da wasu mutum hudu suna fuskantar shari'a ne a kotun bisa zarginsu da cin amana da kuma almundahana.

    Matakin alkali Baba-Yusuf ya zo ne bayan wata kara da lauyan Dasuki, Mr Ahmed Raji ya shigar bisa sashe na 1 da 2 da 491 da kuma 492 na dokar hukunta manyan laifuka ta 2015.

    Da yake yanke hukunci kan karar ta Dasuki, alkalin ya ce tun da EFCC bata kalubalanci batun ba, ya kamata a amince da ita.

  9. Dan majalisa a Uganda ya shiga zauren majalisar da kwalbar farin dango

    Wani hoton bidiyo da ya bazu kuma ya dauki hankalin ma'abota kafafen sada zumunta shi ne na wani dan majalisa a Uganda da ya shiga harabar majalisar da wata kwalba makare da farin dango.

    David Obala wanda yake wakiltar mazabar Ngora a gabashin kasar ya shiga zauren majalisar ranar Talata da kwalbar domin nuna bacin ransa game da jan kafar da gwamnati take na yaki da barkewar farin dango da ke addabar albarkatun gona a sassan yankin - lamarin da ke haifar da fargaba kan karancin abinci.

    Bayan da wani dan majalisar ya kalubalancesa an tilasta wa Mr Obala mika kwalbar ga mutumin da ke tabbatar da an bi tsari a majalisar.

    Shugaban majalisar ya bukaci karin haske game da kokarin da ake na yi wa farin dangon feshi.

    Jaridar Daily Monitor a kasar ta wallafa hoton bidiyon Mr Obala rike da kwalbar farin dango:

  10. Chloroquine tana maganin coronavirus

    An gano cewa maganin zazzabin cizon sauro na Chloroquine phosphate wanda aka fi amfani da shi a nahiyar Afirka musamman a shekarun 1980 da 1990 yana warkar da cutar numfashi ta coronavirus.

    Ma'aikatar kimiyya da fasaha ta kasar China ce ta bayyana hakan ranar Laraba.

    Gidan talbijin na China Global Television Network ya ruwaito cewa daukacin masana a kasar sun amince a yi amfani da Chloroquine phosphate domin maganin cutar Covid-19 virus, wadda aka fi sani coronavirus.

    An dade ana amfani da maganin wurin magance zazzabin cizon sauro gabanin sauron ya soma bijire wa maganin.

    Kafar watsa labaran kasar ta Xinhua ta ruwaito cewa an yi gwajin chloroquine a fiye da asibitoci goma da ke Beijing, babban birnin kasar China da wasu larduna biyu, "kuma yana aiki sosai".

  11. Hotuna: Yadda aka yi zaman majalisar zartaswa a wannan makon

    Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya jagoranci zaman majalisar zartarwa ranar Laraba.

    Ana gudanar da taron ne duk mako a fadar shugaban kasa da ke Abuja, babban birnin kasar.

    Ga hotunan yadda aka yi zaman majalisar zarwartar na wannana mako:

  12. Amurka ta gargadi Afirka ta Kudu kan kwace filaye ba bisa ka'ida ba

    Sakataren harkokin wajen Amurka, Mike Pompeo, ya yi kashedin cewa kudirin gwamnatin Afirka ta kudu na kwace filaye ba tare da biyan diyya ba zai zama babbar annoba ga tattalin arzikin kasar.

    Mr Pompeo ya bayyana hakan a Ethiopia a ziyarar da yake a yankin Afirka.

    ''Afirka ta kudu na tafka muhawara game da samun damar kwace filayen mutane ba tare da biyan diyya ba.Hakan babbar annoba ce ga tattalin arziki'' kamar yadda ya fada wa kamfanin diullancin labarai na Bloomberg.

    Tattalin arzikin kasashen Afirka na bukatar ''dokoki'' da girmama dukiyoyin al'umma da zai bude kafofin zuba hannayen jari,'' a cewarsa.

  13. An kai sabon hari a Chibok

    Rahotanni daga Borno a arewa maso gabashin Najeriya na cewa wasu mahara da ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram ne sun kai hari garin Koringilum da ke karamar hukumar Chibok.

    Rahotanni sun ce maharan sun kutsa garin ne a motoci da Babura tare da kone wata makarantar firamare, da kuma kwashe kayan abinci.

  14. Coronavirus ta bulla Iran

    Kasar Iran ta tabbatar da bullar cutar Covid-19 wato coronavirus bayan da aka tabbatar da cewa mutane biyu sun kamu da ita.

    Ma'aikatar lafiya ta kasar ta ce an gano wadanda suka kamu da cutar a lardin tsakiyar Kum.

    A Gabas ta Tsakiya, Hadaddiyar Daular Larabawa ce ta fara tabbatar da bullar cutar a kasarta bayan da aka samu mutum tara da ke dauke da kwayar cutar kuma dukkaninsu 'yan asalin China ne.

    A Afirka kuma kasar Masar ce ta fara samun bullar cutar.

    Kasashe da dama da manyan kamfanonin jiragen sama a yankin sun dakatar da zirga-zirgar jiragen saman China a wani bangare na yin taka tsan-tsan kan barkewar annobar cutar.

  15. An hana dan hamayya takarar shugaban kasar Benin

    An haramta wa babban dan hamayyar Benin tsayawa takara a dukkan zabukan kasar tsawon shekara hudu sannan aka nemi ya biya tarar $8,200 saboda samunsa da laifin kashe kudi fiye da kima a lokacin yakin neman zaben shugaban kasar na 2016.

    Hakan na nufin Lionel Zinsou ba zai iya tsayawa takara a zaben shugaban kasar da za a yi shekara mai zuwa ba, sai dai idan kotun daukaka kara ta soke haramcin da aka yi masa.

    Lauyan Mr Zinzou,Robert Dossou, ya shaida wa kafar watsa labarai ta Jeune Afrique cewa: "Burinsu a bayyane yake - suna so su ce Lionel Zinsou bai cancanci tsayawa takara ba.Wadanda ke kan mulki suna so su kawar da duk dan takarar da zai iya kalubalantarsu a zaben 2021."

    Gwamnatin Benin ta sha musanta irin wannan zargi. A watan jiya, Ministan shari'a Séverin Quenum ya gaya wa kafar watsa labaran cewa ba sa yin katsalandan a tsarin shari'ar kasar da niyyar cin riba irin ta siyasa.

  16. 'Cire hafsoshin tsaron Najeriya barazana ne ga kasar'

    Sakataren gwamnatin Najeriya ya ce cire manyan hafsoshin tsaro zai haifar da baraka tare da yin barazana ga hadin kan kasa.

    Boss Mustapha ya bayyana hakan ne ranar Talata yayin da ake bikin kaddamar da littafi mai taken ''CAN, addini da shugabanci a Najeriya,'' da tsohon Sakataren gudanarwar kungiyar kiristoci ta kasar Samuel Salifu ya rubuta.

    JaridarThe Punch ta ambato shi yana cewa ''ba na ganin korar hafsoshin tsaron ya dace, ba a sallamar mutane haka kawai. Akwai ka'idoji kuma ina ganin a lokacin da ya dace za a bi wadannan ka'idojin.''

    'Yan kasar da dama dai sun sha kiraye-kirayen a sauke hafsoshin tsaron saboda yadda ake ci gaba da samun hare-haren ta'addanci kan mutane da sace-sacen jama'a a sassan kasar.

  17. 'Yan bindiga sun kai hari kan sansanonin sojin Somalia

    Mayakan kungiyar Al-Shabab sun kai hare-hare biyu daban-daban a sansanonin sojin kasa na Somalia da ke lardin Lower Shabelle.

    'Yan bindigar sun yi amfani da wata mota makare da abubuwan fashewa inda suka karya wata gada da ke kan hanyar sansanin sojin da ke Qoryoley.

    Wani kakakin rundunar ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa dakarun wanzar da zaman lafiya na kungiyar Tarayyar Afirka sun dakile hare-haren.

    Tun da sanyin safiya aka bayar da rahotannin yin gumurzu lokacin da mayakan al-Shabab suka hari wani sansanin soji da ke El Salini.

    Sojin sun ce sun yi wa 'yan bindigar illa sosai. Sai dai ba a san yawan sojin da aka kashe ba.

  18. An ceto masu aikatau daga Saudiyya da Jordan

    Ministan kwadago na Uganda ya ceto wasu mata biyu da ke aikatau a Saudiyya da Jordan.

    Ministan Frank Tumwebaze ya ce matan sun yi kiran gaggawa ga 'yan uwansu da ke Uganda wadanda kuma suka roki ministan da ya agaza musu.

    Mr Tumwebaze ya ce gwamnatin Uganda ta samu damar mayar da matan gida bisa hadin kan hukumar da ta aike su kasar wajen.

    Ministan ya wallafa wani hoto da ya dauka tare da matan a shafinsa na Twitter

    Mata 'yan Uganda da dama na barin kasarsu domin yin aikatau a Kenya da wasu kasashen.

    Wasu kuma ana tilasta musu yin aiki cikin yanayi mara dadi sannan ba sa iya tafiya kasashensu.

  19. An halatta auren mace fiye da daya a Amurka

    Majalisar Dattijai a jihar Utah da ke Amurka ta kada kuri’ar halatta auren mata fiye da daya.

    A baya dokar jihar ta tanaji daurin shekaru biyar a gidan yari ga duk wanda ya auri mace fiye da daya a jihar da mafi yawanci kiristoci mabiya darikar Mormons ne.

    Amma yanzu mutum zai iya auren mace fiye da daya ko da yake za a ci tarasa $750.

    Sai dai ana ganin dokar za ta fuskanci turjiya a majalisar wakilai.

    Wakilin BBC ya ce dan majalisar da ya gabatar da kudirin dokar ya ce dokar da ke aiki a yanzu ta jefa iyalai halin kyama tare da haifar da wata al’ada ta cin zarafi.

    Masu adawa dai na ganin dokar hatsari ce musamman ga mata kanana da ake tilasta wa auren masu manyan shekaru.

  20. An samu bullar zazzabin Lassa a Lagos

    Rahotanni daga Legas a kudu maso yammacin Najeriya na cewa a karon farko an samu bullar cutar zazzabin Lassa a jihar.

    Kwamishinan lafiya a jihar Akin Abayomi ne ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba.

    Ya ce wanda ya kamu da cutar yana kebe a asibitin koyarwa na Legas.

    Abayomi ya kuma ce ana sa ido kan lamarin inda ya yi kira ga al'ummar jihar dasu kwantar da hankalinsu.

    Gidan talabijin na Channels ya rawaito kwamishinan na cewa ya zama wajibi ga jama'a su tabbatar da tsaftar jikinsu da ta muhallansu a ko da yaushe a wani bangare na matakan kariya daga yaduwar cutar a jihar.