Najeriya na cikin kasashen da makomar yara ke cikin hatsari
Najeriya na cikin kasashen da makomar yara kanana ke cikin hatsari, kamar yadda sabon binciken da aka fitar kan makomar rayuwar yara kanana a duniya ya nuna.
Rahoton wanda Hukumar Lafiya ta Duniya da Asusun kula da kananan yara na Duniya, Unicef, da mujallar lafiya ta The Lancet suka fitar ya ce Najeriya ce kasa ta 174 cikin jerin kasashe 180 da aka yi nazari akansu game da bunkasar lafiya yara.
Hakan na nufin Najeriya na daya daga cikin kasashe goma na karshe a duniya da makomar yara ke fuskantar rashin tabbas ta fuskar bunkasar rayuwarsu da lafiyarsu.
Rahoton ya ce nazarinsa kan hatsarin da makomar yaran ke ciki ya dogara ne kan mizanin tsira da rai ga kananan yara da koshin lafiyarsu wadanda suka hada da lafiya da ilmi da abinci mai gina jiki da daidaito da tazarar da ke akwai ta fuskar kudin shiga.
Binciken ya ce sama da yara Biliyan biyu ke rayuwa a kasashen da ci gabansu ke fuskantar barazana daga rikici da bala'o'i da canjin yanayi ke haddasa wa.