Ban kwana
Jama'a nan muka kawo karshen rahotannin kai-tsaye, sai kuma gobe idan Allah ya kai mu.
Umar Mikail ne da Sagir Saleh ke maku fatan mu kwana lafiya.
Ku duba kasa domin ganin abubuwan da suka faru a yau Litinin.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Shafin da ke kawo labaran abubwan da ke faruwa kai tsaye a Najeriya da Nijar da Kamaru da Ghana da Chadi da sauran sassan duniya
Sagiru Kano Saleh and Halima Umar Saleh
Jama'a nan muka kawo karshen rahotannin kai-tsaye, sai kuma gobe idan Allah ya kai mu.
Umar Mikail ne da Sagir Saleh ke maku fatan mu kwana lafiya.
Ku duba kasa domin ganin abubuwan da suka faru a yau Litinin.
'Yan sanda sun gurfanar da wani mai suna Enejo Isah a gaban kotu a yankin Mpape da ke birnin Abujan Najeriya bisa zargin satar ayaba da ta kai darajar naira miliyan 1.8.
Ana zargin Enejo Isah, wanda ke zaune a unguwar Mpape, da laifin sata da kuma shiga gonar wani ba tare da izini ba, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na NAN ya ruwaito.
Lauya mai shigar da kara M.M. Austin ya fada wa kotun cewa a ranar 11 ga watan Janairu ne Enejo mai shekara 26 ya shiga gonar ayaba mallakar Emmanuel Tanko, inda ya saci ayabar da ta kai darajar naira miliyan 1.8.
Ya kuma yi zargin Enejo da hada kai da wani mai suna Solomon, wanda yanzu haka ya tsere, wurin aikata laifin. Ya kuma ce Emmanuel ya kai rahoton lamarin ne ga ofishin 'yan sanda na Mpape.
Austin ya ci gaba da cewa laifin ya saba wa sashe na 97 da kuma 288 na kundin shari'ar manyan laifuka. Sai dai Enejo ya musanta zargin.
Mai Shari'a Salihu Ibrahim ya bayar da belin wanda ake zargi kan naira miliyan 1 tare da mai tsaya masa mutum daya, sannan ya dage sauraron karar zuwa 30 ga watan janairu.
Ma'aikatar lafiya ta jihar Kaduna ta tababtar da mutuwar wani matashi sakamakon kamuwa da zazzabin Lassa a jihar.
Jaridar Punch ta ambato kwamishinan lafiyar jihar Amina Baloni, a rahoton kamfanin dillancin labaran Najeiya, cewa mutumin ya rasu ne jiya Lahadi.
Ta ce sakamakon gwajin da aka yi kan mutum 11 da ake zargin suna dauke da kwayar cutar, ya nuna cewa bakwai daga cikinsu ba sa dauke da ita.
Mutum 38 da ake zargi suna dauke da kwayar cutar na samun kulawa, yayin da ake kokarin dakile yaduwarta.
Ta kuma karyata jita-jitar rufe asibitin koyarwa na Barau Dikko domin killace masu dauke da kwayar cutar, inda ta ce asibitin ya dauki matakan takaita ziyartar majinyata ne domin kawar da kamuwa da wasu cutuka masu yaduwa, ban da zazzabin Lassa.
Gwamnatin jihar Legas ta haramta sana'ar haya da babura wato Okada a wasu sassan jihar.
Haramcin ya shafi babura masu kafafu uku (keke NAPEP) da baburan acaba na kamfanonin sufuri na Opaya da Gokada a jihar.
Sanarwar na kunshe ne a cikin sakon da hadimin gwamnan kan kafafen sadarwa na zamani Jibril Gawat ya wallafa a shafinsa.
Sanarwar kakan na dauke ne a sakon da hadimin gwamnan kan kafafen sadarwa na zamani Jibril Gawat ya wallafa a shafinsa.
Kananan hukumomin da sabuwar dokar wadda za ta fara aiki ranar 1 ga wata Fabrairu mai zuwa ta shafa su ne Apapa, lLagos Mainland da Surulere da Eti Osa da Lagos Island da Ikeja.
Kotu ta dage sauraron karar da aka shigar na tsohon babban alkalin Najeriya Mohammed Adoke zuwa ranar Alhamis 30 ga watan nan na Janairu.
Jaridar Premium Times ta ce hukumar EFCC ta gurfanar da Mohammed Adoke ne a gaban abbar kotun tarayya da ke Abuja a yau Litinin kan wasu tuhume-tuhume 42 masu alaka da rashawar.
EFCC ta gurfanar da shi ne a shari'ar da ta ke yi kan bakalar dala biliyan 1.3 na rijiyar mai ta Malabu.
A watan jiya ne hukumar ta tsare tsohon babban alkalin bayan dawowarsa daga birnin Dubai na Hadaddiyar Daular Larabawa inda a can ma aka tsare shi saboda neman sa da hukumomin Najeriya ke yi ruwa a jallo bisa zargin.
Sabon shugaban kungiyar gwamnonin jam'iyyar PDP Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sokoto ya ce kungiyar za ta yi aiki tare da kwamitin gudanarwar jam'iyyar domin inganta tsarin demokradiyya a Najeriya.
Tambuwal wanda zai gaji Seriake Dickson na jihar Bayelsa wanda wa'adinsa ke karewa nan da mako biyu masu zuwa ya bayyana haka ne a lokacin bude taron nkwamitin zartaswar jam'iyyar karo na 88 a yau Litinin.
Ya ce kungiyar za ta mayar da hankali wurin kawo ci gaban jam'iyyar. Ya kuma yi alkawarin tabbatar da ganin gwamnoni na aiwatar da manufofi da shirye-shiryen jam'iyyar a dukkan jihohin kasar.
'Yan bindiga sun kashe mutane da dama a wani harin da suka kai a jihar Filato da ke arewa ta tsakiya a Najeriya.
Gwamnan jihar Filato Simon Lalon ya tabbatar wa jaridar Daily Trust harin na karamar hukumar Bokkos inda ya mika ta'aziyyarsa ga wadanda abin ya shafa.Jaridar Punch ta ambato wani mazaunin yankin Benjamin Dogo na cewa wadanda aka kashe ya kai haura mutum 12.
Gwamnan jihar ya kuma umurci jami'an tsaro su baza komarsu wajen kamowa da hukunta miyagun da suka yi aika-aikan sannan su sanya kafar wando daya da miyagun da ke neman yin kafar ungulu ga zaman lafiyar da aka samu a jihar.
Harin na zuwa ne kasa da mako biyu bayan wani harin da aka kai a karamar hukuma Mangu inda aka kashe mutum 12, mako guda bayan wasu 'yan bindiga sun yi wa Fulani fashin shanu 73 da tumaki 23.
Mahaifin yarinyar nan da kungiyar Boko Haram ta yi garkuwa da ita a 2018 Leah Sharibu, ya bukaci a dawo masa da 'yata.
Mahaifin ya bayyana hakan ne bayan wasu rahotanni masu karo da juna cewa 'yar tasa ta haihu a hannun kungiyar.
Amma mista Nathan ya shaida wa BBC cewa shi bai damu ko 'yar tasa ta haihu ko ita kadai take ba, face kawai a dawo masa da ita.
Leah Sharibu na daga cikin dalibai fiye da 100 makarnatar 'yan mata ta Dapchi wadanda kungiyar Boko Haram ta yi garkuwa da su a 2018.
Daga bisani kungiyar ta sako sauran daliban amma ta ci gaba da rike ta inda wasu rahotanni ke cewa hakan ya faru ne saboda ta ki sauya addininta.
A watan Agustan 2018 kungiyar ta fitar da wani bidiyo inda a ciki dalibar ke kira ga gwamnati ta kubutar da ita.
Tsohon wakilin Kiru da Bebeji a Majalisar Wakilan Najeriya kuma dan takarar APC a zaben cike gurbi na mazabar, Abdulmumin Jibrin ya ce ya taya abokin takararsa na PDP Ali Datti murna, wanda ya kayar da shi a zaben na ranar Asabar, kuma ya ce ba zai kalubalanci zaben a kotu ba.
Alaka dai ta yi tsami tsakanin shugabancin jam'iyyar APC na jihar Kano da kuma Abdulmumin Jibrin kafin zaben amma an ga Abdulmumin a wasu hotuna da aka yada a shafukan sada zumunta yana durkusa wa Abdullahi Abbas, wanda shi ne shugaban jam'iyyar a Kano 'yan sa'o'i kafin fara kada kuri'a.
A wani sako da ya wallafa shafinsa na Twitter a yau Litinin, Abdulmumin ya ce ba zai sake yin magana kan batun ba kuma yana fatan 'yan jarida za su kyale shi ya sarara.
A cikin sakon bidiyon har wa yau, an gan shi a wurin yawon kamfe yana kururuwar "Kanoooo", su kuma magoya baya suna "sai Gandujeee". Babu tabbas ko hakan yana nufin zai ci gaba da biyayya ga shugabancin APC a Kano da kuma gwamnatin Abdullahi Ganduje.
Da ma dai honorabul din ya ce ba zai sake yin takarar dan majalisar tarayya ba idan ya kammala wannan wa'adin kafin daga bisani Kotun Daukaka Kara ta soke zaben nasa.
An zabe shi a matsayin Dan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazabar Kiru/Bebeji ta Jihar Kano sau biyu: a 2011 da kuma 2015.
Wata babbar kotu a Abuja ta bayar da belin tsohon sanata Shehu Sani a kan naira miliyan 10.
Jaridar Punch ta ce mai shari'a Inyang Ekwo, ya ba da belin ne bayan EFCC ta gurfanar da Shehu Sani a karon farko tun bayan tsare shi da hukumar ta yi a narar 31 ga watan Disamban 2019.
EFCC na zargin Shehu Sani da laifin karbar rashawar dala 25,000 da sunan zai ba wa manyan jami'an gwamnati.
Alkalin ya yi watsi da bukatar EFCC na ci gada da tsare Shehu Sani wanda lauyansa ya mika bukatar ba da belinsa.
Mai shari'a Inyanga Ekwo ya shardanta wa Shehu Sani kawo wani dan kasa na gari da ya mallaki kadarar naira miliyan 10 a matsayin wanda zai tsaya masa.
Ya kuma bukaci wanda ake karar ya mika kotun takardar fasfonsa sannan ta umurce shi da kar ya fita daga Najeriya ba tare da izinin kotun ba.
Zarge-zargen da EFCC ke wa Shehu Sani sun hada da karbar dala 10,000 da sunan mukaddashin shugabanta Ibrahim Magu.
Tana kuma zargin sa da karbar wani dala 15,000 cewa zai ba wa babban alkalin Najeriya toshiyar baki a kan sharia'rsa da ke gaban kuliya.
Amma Shehu Sani ya musanta zarge-zargen.
An sake kai harin rokoki a kan ofishin jakadancin Amurka da ke Iraki.
Akalla mutum uku mutu a harin wanda shi ne karon farko da aka illata jami'an Amuraka a wannan shekara.
Daya daga cikin rokokin ya lalata wani yanki na ofishin yayin da wasu karin rokoki biyu suka fadi a kusa da ofishin jakadancin.
Babu wata kungiya da ta yi ikirarin kai harin amma a baya Amurka ta zargi dakarun da Iran ke goyon baya a Iraki da hannu a hare-haren da aka kai wa ofishin nata.
Firai ministan Iraki, Adel Abdul Mahdi ya yi tir da harin yana mai cewa ci gaba da kai hari na iya mayar da kasar tamkar fagen yaki.
Amurka ta bukaci gwamnatin Iraki ta sauke nauyin da ke kanta na kare ma'aikatan jakadancin Amurka da ke kasar Iraki.
Gwamnatin Gambia ta haramta ayyukan masu fafutuka da ke adawa da matakin da saba alkawarin da shugaba Adama Baro ya dauka na gudanar da zabe a wannan shekara.
Hukumomin kasa sun tsare mutum 137 bayan dubun dubatar masu zanga zangar adawa da ci gaba da zaman shugaba Adama Barrow a kan mulki sun yi gangamin neman a gudanar da zabe a bana.
Adama Barrow ya karbi mulkin kasar ne bayan kayar da tsohon shugaba Yahya Jameh, karkashin hadakar jam'iyyun adawa tare da yi alkawarin yin mulki na shekara uku sannan ya gudanar da zabe.
Sai dai a bara an samu rabuwar kai bayan wani bangare na hadin gwiwar ya amince shugaban ya ci gaba da mulki na tsawon shekara biyar kamar yadda dokar kasar ta tanada.
Gwamantin kasar ta bayyana zanga-zangar da ta yana tayar da hankali a matsayin haramtacce da neman tayar da zaune tsaye.
Kakakin gwamnatin Ebrima G Sankareh ya zargi masu zanga-zangar wanda ya ce ba su da rajista da neman hambarar da gwamnati.
Gwamnatin ta kuma dakatar da wasu gidajen radiyo guda biyu bisa zargin goyon bayan masu tayar da hankli.
Jim kadan bayan yanke mata hukuncin kisa sai jami'an gidan yari suka yi kama-kama suka fice da Maryam Sanda daga cikin kotu cikin yanayin sassarfa.
Sojojin saman Najeriya sun hallaka mayakan kungiyar ISWAP bayan tarwatsa sansanin kungiyar a jihar Borno.
Jiragen sojin kasar sun yi barin wuta a kan sansanonin inda suka kashe mayaka da dama.
Rundunar sojin kasar ta ce jiragenta sun kai harin sama a kan maboyar kungiyar na yankin Gashigar a jihar Borno da Tumbun Gero a kan iyakar kasar Chadi da kuma dajin Bula Bello da ke kusa da dajin Sambisa.
Jaridar Daily Trust a Najeriya ta ruwaita kakakin rundunar a cikin wata sanarwa yana cewa sun lalata kayan yakin da mayakan ISWAP din ke amfani da su a maboyar tasu.
Mutum miliyan bakwai na bukatar agajin abinci da sauran kayayyaki a kasar Itiyofia.
Kakakin hukumar kula da iftila'o'in Itiyofiya Debebe Zewede ya kasar ta ce na bukatar sama da dala biliyan daya domin sayen kayan agaji ga mutanen da ke cikin matsanancin hali.
Debebe ya ce kasar na yawan fuskantar matsalar fari wanda ke jefa mutane da kuma tattalin arziki kasar cikin mawuyacin hali.
Akalla mutum miliyan shida ne ke karbar agajin kayan abinci a cikin wannan shekara a kasar mai yawan mutan miliyan 113, wacce ita ce ta biyu wurin yawan a'umma a nahiyar Afirka.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin sanya rundunar sojin sama ta kasar a aikin kai farmakin kan 'yan bindiga masu satar mutane da shanu a jihohin Naija da Kaduna da Zamfara.
A baya bayan nan dai ana ta kokawa da hare-hare da miyagun abubuwan da 'yan bindigar ke aikatawa ga alummomin jihar Naija.
Kakakin Shugaban Najeriyar, Mallam Garba Shehu, ya yi wa BBC karin bayani kan wannan batu:
Jami'an gidan yari sun tisa keyar Maryam Sanda zuwa inda za a ci gaba da tsare ta.
Wata babbar kotun Abuja ce ta yanke hukunci bayan sauraron shari'ar zargin matar da kashe mijinta.
Maryam ta yi ta kuka da kururuwa bayan kotun ta sanar da hukuncin, yayin da aka yi ta kokarin lallaba ta.
A shekarar 2017 ne aka fara gurfanar da matar bayan mutuwar mijin nata a lokacin wata hatsaniya da aka samu tsakanin ma'auratan.
Ita dai Maryam ta musanta hannu a kisan mijin nata wanda ta ce ya zame ne ya fadi a kan kuttun shisha inda tsagin kuttun ya cake shi a kirji.
Maryam Sanda wadda wata babbar kotu a Abuja ta yanke wa hukuncin kisa ta hanyar rataya, ta yi ta kururuwa kafin jami'an gidan yari su yi awon gaba da ita.
Wata kotu a Abuja, babban birnin Najeriya, ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya a kan Maryam Sanda, matar da ta kashe mijinta.
An yanke hukuncin ne bayan gurfanar da matar bisa laifin daba wa mijinta mai suna Bilyaminu Bello wuka a shekarar 2017, sakamakon rikici a tsakaninsu.
A ranar Litinin ne kotun ta yanke hukuncin bayan dage zamanta a ranar 25 ga watan Nuwamba.
Sanar da hukuncin ke da wuya, Maryam ta yi ta kuruwa a zauren kotu.
A baya ta musanta zargin inda ta ce mijin nata ya mutu ne sakamakon rauni da ya samu bayan ya fadi a kan kuttun shisha a gidansu.
Wani jirgin fasinja ya yi hatsari a gabashin Afghanistan.
Hukumomin kasar sun ce jirin kamfanin Ariana Airlines ya fado ne a yankin Ghazni da ke Yamma da birnin Kabul.
Kakakin lardin ya ce jirgin ya fado ne sannan ya kama da wuta sakamakon wasu matsaloli.
Hukumomin kasar ba su yi karrin bayani ba tukuna.