A dawo mani da 'yata ko ta haihu ko akasin haka – Mahaifin Leah Sharibu

An wallafa

Nathan Sharibu mahaifin Leah Sharibu, matshiyar nan da Boko Haram take rike da ita tun bayan sace ta daga garin Dapchi na jihar Borno a Najeriya a 2018, ya ce shi dai a dawo masa da 'yarsa "ko tana da ciki ko babu".

A jiya Asabar ne dai wasu jaridu a Najeriya suka ruwaito cewa Leah Sharibu mai shekara 14 (lokacin da aka sace ta) ta samu ciki daga wani babban kwamandan Boko Haram da ya aure ta kuma suke zaune a wajen Najeriya.

A wata hira da ya yi da sashen Pidgin na BBC, mahaifin Leah ya nuna damuwar ganin 'yar tasa ko da ta haihu ko ba ta haihu ba.

"Ni dai kawai ina bukatar ganin 'yata ko ta haihu ko ba ta haihu ba. Ina bukatar 'yata a raye...abin da nake bukata kenan," in ji Nathan.

Cikin kadawar murya ya kara da cewa: "Abin bacin rai ne, babu abin da zan iya cewa, na bar komai a hannun Allah."

Mahaifiyar Leah ta ce ba za ta iya tabbatar da sahihancin labarin cikin na 'yarta ba domin babu wanda ya fada mata wani abu mai kama da hakan, a intanet kawai ta karanta a jiya Asabar.

"Ko gaskiya ne ko akasin haka ni ba abin da zan iya cewa," ta bayyana ta wayar salula.

"Tun sanda suka sace 'yata babu jami'in gwamnati da ya ce mana uffan," in ji shi.

Leah Sharibu wadda za ta cika shekara 17 da haihuwa a watan Mayu mai zuwa, na daya daga cikin 'yan matan da kungiyar Boko Haram ta sace a garin Dapchi na Jihar Borno a Arewa maso Yammacin Najeriya ranar 19 ga Fabarairun 2018.

Daga baya gwamnatin Najeriya ta ce 'yan bindigar sun sako 106 daga cikinsu amma suka rike Leah da kuma wasu.