Cutar pneumonia ka iya kashe yara fiye da miliyan daya a Najeriya - Unicef
Majalisar Dinkin Duniya ta ce kimanin yara miliyan da dubu dari hudu ka iya mutuwa a shekaru 10 masu zuwa sakamakon cutar sanyin huhu, wato pneumonia.
Hukumar kula da kananan yara ta Majalisar, Unicef ce ta yi wannan hasashen inda take fadin cewa Najeriya ka iya zama kasar da tafi yawan mutuwa sakamakon cutar ta pneumonia.
Bisa kididdigar da ta Unicef ta yi ta ce ta gano yara milyan 6.3 ka iya mutuwa saboda cutar numfashin a fadin duniya.
Unicef ta ce ta gano kasar India ce za ta iya kasancewa ta biyu wajen cutar numfashi ga kananan yara, inda kuma jamhuriyar dimokradiyyar Congo ke biye mata baya a matsayi na uku.
Hukumar ta Unicef ta yi gargadi ga hukumomi da su kara kaimi wajen kara yawan rigakafin cutar numfashin ta numoniya.
To amma hukumar ta wallafa a shafinta na Twitter cewa Najeriya na yin irin wannan rigakafin.