Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da suka faru ranar Juma'a

Shafin da ke kawo labaran abubwan da ke faruwa kai tsaye a Najeriya da Nijar da Kamaru da Ghana da Chadi da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

Sagiru Kano Saleh and Halima Umar Saleh

  1. Abin da ya sa shugaban majalisar dattawa ya koka kan matsalar tsaro a Najeriya

    A wannan makon ne Shugaban Majaliasar Dattijan Najeriya Sanata Ahmad Lawan ya bayyana cewa lamarin tsaro a kasar ya yi lalacewar da bai kamata a ce an zura masa ido ba.

    Ba kasafai dai shugaban majalisar ke fitowa yana suka kan yadda al'amura ke tafiya ba a kasar, kasancewar ana yi masa kallon na hannun daman Shugaba Buhari.

    Alhaji Bashir Hayatu Jantile (Gentile) mataimaki ne na musamman ga shugaban majalisar ta dattijai, kuma Yusuf Ibrahim Yakasai ya tambaye shi ko me ya sa Ahmad Lawan din ya fito fili yana wannan magana a yanzu?

    Ga yadda hirar tasu ta kasance:

  2. Ana dab da kwace iko da gari mai muhimmanci a Syria

    Rahotanni daga arewa maso gabashin Syria na cewa dakarun da ke bayan gwamnati na gab da kwace iko da garin Ma'aratul Numan mai muhimmanci.

    Dakarun Shugaba Basharul Assad da luguden wuta ta sama da sojin Rasha ke taimakawa sun shiga kudancin birnin Idlib a jiya Talata, an kuma yi mummunar gwabzawa tsakaninsu da 'yan tawaye.

    Kafar yada labaran Syria ta ruwaito cewa sojojin sun karbe iko da kusan rabin Idlib.

    Zafafa luguden wuta a maboya ta karshe da 'yan tawayen Syria ke ciki ya janyo dubun-dubatar farar hula tserewa tare da nufar iyakar kasar da Turkiyya.

    Garin Ma'aratul Numan yana wata hanya da ta rabu gida biyar da take sada ka da biranen kasar, ta kuma hada Syria da wasu kasashe da take cinikayya da su ciki har da Jordan da Turkiyya.

  3. Japan ta kwashe mutanen kasarta daga Wuhan na China don guddun cutar Corona

    Hukumomi a kasar China na nuna fargaba yadda adadin wadanda cutar Coronavirus ta hallaka ke kara yaduwa.

    Kawo yanzu mutane 132 ne suka mutu wasu 6,000 sun kamu da ita, adadin da ya rubanya wanda cutar SARS da ta haddasa shekaru 17 da suka gabata.

    Jami'an lafiya a China na hasashen cutar za ta ci gaba da yaduwa da hallaka mutane cikin mako guda.

    Su kuwa 'Yan Japan da aka kwaso daga birnin Wuhan na kasar China sun bayyana sa'idar da suka samu a lokacin da suka isa birnin Tokyo.

    Gwamnatin kasar ce ta aike da jirgi na musamman dan kwashe su, wanda aka cika shi da jami'an lafiya domin tantance lafiyarsu kafin ma su hau jirgin.

    A Jamus wani mutum mai shekara 32 ya kamu da cutar daga wata 'yar China da suke samun horo a Baveria.

    Wani jirgin da Amurka ta yi haya na kan hanyarsa ta zuwa Alaska, yayin da kasashen New Zealand da Australia da Tarayyar Turai su ma na shirin yadda za su kwaso jama'arsu daga China a daidai lokacin da cutar Coronavirus ke kara yaduwa.

  4. Labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya a yau

    Masu bin mu a wannan shafi assalamu alaikum. Halima Umar Saleh ce ke muku sallama a daidai wannan lokaci da za mu fara kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da Kamaru da sauran sassan duniya a yau Laraba 29 ga watan janairun 2019.

    Zuwa anjima abokan aikina Usman Minjibir da Umar Mika'il za su karbe ni.

    Domin karanta labaran abubuwan da suka faru a jiya Talata sai ku duba kasa.

  5. Coronavirus ta bulla a Habasha

    An kebe wasu mutum hudu da ake zargin sun kamu da cutar Coronavirus Addis Ababa babban birnin kasar Habasha.

    Karamin ministan lafiyar kasar Lia Tadesse, ya ce mutum hudun da ke dauke da cutar 'yan kasar ne.

    Uku daga cikinsu dalibai ne da suka dawo gida daga jami'o'i a kusa da birnin Wuhan inda cutar ta fi kamari.

    Tun ranar Larabar makon jiya ne kasar ta fara tantance matafiyar da ke shiga kasar daga China. Zuwa yanzu an tantance mutum 22,000 da suka iso kasar a kokarin dakile yaduwar cutar ta Coronavirus.

    Ma'aikatar lafiyar kasar ta ce an dauki samfurin cutar zuwa kasar Afirka ta Kudu domin gwaji.

    Coronavirus wacce bakuwar cutar dabbobi ce ta kashe mutum fiye da 100 a China yayin da wasu 4,500 ke fama da ita.

  6. Kakakin Majalisar Dokokin jihar Imo ya koma APC mai mulkin jihar

    Shugaban majalisar dokokin jihar Imo Collins Chiji ya sauya sheka tare da wasu takwarorinsa bakwai sun fice daga jam'iyyar PDP sun koma APC mai mulki a jihar.

    Collin Chiji ya sanar da sauya sanar da sauya shekarsu ne a lokacin zaman majalisar na yau Talata.

    Sauya shekar ta ba wa jam'iyyar APC mai mambobi 18 rinjaye da kashi biyu bisa ukun 'yan majalisar yayin da mambobi takwas.

    Majalisar ta dage zamanta jim kadan bayan an sanar da sunayen 'yan majalisar da suka sauya shekan, a cewar wasu jaridun kasar.

  7. Mutum 15 sun mutu a hatsarin mota a Najeriya

    Hatsarin mota ya ritsa da rayukan mutum 15 tare da jikkata wasu 38 a yau Talata.

    Babbar motar da mutanen ke ciki ta taso daga jihar Sokoto ne. Hatsarin ya sa motar ta fada a kogin Omi da ke jihar Ogun.

    Kwamandan hukumiyar kiyaye hadurra a jihar Clement Oladele ya ce an dauke gawa 15 a motar kuma sarkin Hausawan Sabon Garin Ijebu Ode inda ake shirya yadda za a yi jana'izar mamatan.

    Jami'in ya shiada wa jaridar Daily Trust cewa wasu mutu 38 da suka samu rauni kuma an kai su asibitin a garin Ijebu Ode.

  8. An bude wajen gwajin cutar Lassa biyar a Najeriya

    Hukumar dakile yaduwar cututtuka a Najeriya ta ce ta bude wasu dakunan gwaje-gwaje guda biyar don gano tare da tantance masu dauke da utar zazzabin Lassa a kasar.

    Babban Daraktan hukumar, Dakta Chikwe Ihekweazu wanda ya bayyana hakan ranar Litinin a Abuja, babban birnin kasar y ace an bude dakunan gwajin a wasu asibitoci da ke Edo da Ondo da Ebonyi da Legas da kuma guda a harabar hukumar ta NCDC a Abuja.

    Ihekweazu ya ce “a yanzu haka, ana gwajin samfurin cutar da aka samo daga wasu masu dauke da cutar a jihohin Kudu maso Kudancin kasar da kuma wasu jihohin Kudu maso yammacin kasar a asibitin kwararru na Irrua yayin da ake gwajin samfurin cutar da aka samu daga jihohin Kudu maso Yamma a asibitin koyarwa na Alex Ekueme da ke Abakaliki.

    “Wadanda kuma aka samu daga jihohin da ke arewacin kasar ana gwajinsu a cibiyar gwaje-gwaje ta NCDC a Abuja sannan kuma samfurin cutar daga yankin Kudu maso Yamma ake gwajinsu a asibitin koyarwa na jami’ar Legas yayin da sabon dakin gwajin da aka bude a cibiyar kula da lafiya ta tarayya a Owo da ke Ondo ta ke karbar samfurin cutar na jihar Ondo kadai.”

    Shugaban hukumar NCDC ya ce dakunan gwaje-gwajen wadanda aka gina kowane daya akan kudi naira miliyan 100 zasu taimaka wajen gano masu dauke da cutar ta Lassa a kasar.

    A cewarsa, an samar da matakan saukaka jigilar samfurin cutar daga jihohi zuwa wuraren gwaje-gwajen.

    Ya kuma ce hakan zai rage tsawon lokacin da ake shafewa kafin gano cutar da kuma tabbatar da ita wanda hakan na iya rage yawan mace-mace sanadiyyar cutar.

    Ihekweazu ya ce Najeriya tana bada gudummawa ta fannin nazari da kuma bincike don gano rigakafin cutar ta Lassa.

    Ya kara da cewa dakunan gwaje-gwajen zasu taka muhimmiyar rawa wajen wani bincike da za a gudanar kan Lassa Fever wanda za a fara a karshen watan Maris.

    A hannu guda kuma, mutane 25 ne ya zuwa yanzu suka mutu sakamakon fama da zazzabi yayin da aka killace wasu sama da 100 a wasu cibiyoyin kula da masu Lassa a sassan kasar.

  9. An bude titin Maiduguri zuwa Damboa

    Sojoji sun sake bude babbar titin Maiduguri zuwa Damboa bayan wata 13 da suka rufe titin saboda matsalar tsaro.

    Da ya ke bude titin a ranar Talat, babban hafsan sojin kasan Najeriya Tukur Buratai ya ce yanzu masu ababen hawa na iya bin titin da ya tashi daga Maiduguri har zuwa Biu.

    A labrin da jaridar Daily Trust ta wallafa, Buratai ya ba wa matafiya tabbacin tsaro a kan titin sannan ya umurici kwamandojin da ke yankin su tabbatar da hakan.

    A baya dai gwamnan jihar Babagana Zulum ya bukaci ministan tsaro Bashir Magashi a sake bude babban titin a lokacin da ya ziyarci ministan.

  10. Mahaifi ya tari jirgi domin tseratar da 'yarsa

    Bidiyon wani mahaifi da ya kare diyarsa da jirgin kasa ya kusa kadewa a Masar ya karade shafukan safukan sadarwa.

    Mutum ya fada kan titin jirgin kasa ne a lokacin da wani jirgi ya taho a guje inda ya je ya tseratar da diyarsa da ke kan titin jirgin.

    Shaidu sun ce yarinyar na tafiya ne a kan titin jirgin kasa yayin da jirgin da ya tinkaro a guje ya sa karaurawa.

    'Wata 'yar yarinya ta fada a kan titin jirgi. Sai mahaifinta shi ma ya yi tsalle ya fada a ciki inda ya rungume ta ya kare ta har sai da jirgin da ke tafe ya wuce. Dukkansu sun tsira.'

    Ganin haka ya sa mahaifin ya yi tsalle ya fada kan layin jirgin a tashar Ismailia ya kuma suka tsallake rijiya da baya.

    Masu sharhi na jinjina wa mutumin a matsayin 'Jarumin Uba' amma hukumar sufurin jiragen kasar a Masar na zarginsa da diyar tasa da laifin kokarin tsallaka titin jirgin da kuma kin bin hanyar karkashin kasa da aka tanada domin masu shiga jirgin kasa.

  11. Za a gina makewayi a manyan tituna a Kenya

    Wata babbar kotu ta umurci gwamnati ta gina makewayi a kan manyan tituna a Kenya.

    Mai shari'a Kossy Bor ya umurci ministan sufurin kasar ya kafa kwamitin kula da samar da makewayin.

    Kwamitin zai samu wakilci daga gwamnatin kasar da hukumomin sufuri.

    Hukuncin kotun na zuwa ne bayan wani lauya ya shigar da kara cewa samun makewayi muhimmin hakki ne.

    A lokacin sauraron karar, gwamnatin kasar da hukumomin sufuri sun yi ta nuna wa juna yatsa kan wanda ke da hakkin samar da makewayin.

    A baya matafiya a kasar kan yi amfani da makewayi a kauyuka da otal-otal da ke makwabtaka da manyan tituna.

  12. MDD ta nemi a dena cin zarafi a kasar Congo

    Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci gwamnatin Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo ta dauki mataki a kan sojojin kasar da ke take hakkin dan Adam.

    Babbar jam'ian MDD kan kare hakkin bil'adama Michelle Bachelet ta ce rahotannin da da hukumar ta samu sun nuna cewa dakaru da wasu jami'an gwamnati ne ke aikata fiye da rabin cin zarafin da ake yi a kasar.

    Ta bayyana haka ne a ziyarar d ata kai kasar inda ta ce a watan Nuwamban da ta wuce an kashe mutum 19 ta hanyar da ba ta dace ba.

    Misis Bachelet ta ce duk da hakan an samu raguwar cin zarafin da jami'an gwamnati da 'yan tawaye ke yi a kasar.

  13. Gobara ta kona kasuwar Sabo Shagamu

    Akalla shaguna 100 ne suka kone a gobarar da ta tashi a yau Talata a kasuwar Shagamu da ke jihar Ogun a Najeriya.

    Gobarar ta tashi ne a tsakar dare daga layin masu sayar da tufafi sannan ta yadu zuwa wasu sassan kasuwar, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

    Shugabanin kungiyoyin masu ruwan leda da kayan sha a kasuwar, Remo zone da kuma Adetola Soyemi, sun shaida wa jaridar cewa sama da shaguna 100 sun kone a gobarar.

    Jami'an biyu sun yi zargin gobarar ta tashi ne sakamakon matsalar wutar lantarki, sai dai ba za mu iya tabbatar da gasikyar hakan ba.

  14. Jirgi maras matuki na feshin yakar Malariya a Ruwanda, Ana yin feshi a wuraren da sauraye ke taruwa baya ga rabon maganin feshi

    Hukumomi a Ruwanda na amfani da jirage marasa matuka wajen yin feshin sauro a kokarinta na yaki da cutar malariya.

    Kasar na kuma amfani da jirage marasa matuka domin dakon jini zuwa cibiyoyin kula da lamfiya 21 da ke yankunan karkara.

    Kanana jiragen masu dauke da lita goma-goma na maganin sauro na yin feshin ne a matattaran sauraye da inda suke yin kwai tun kafin su kyankyashe.

    Hukumar lafiya ta kasar ta ce matayin na daga cikin hanyoyin da aka dauka bayan raba wa mutane gidan sauro da maganin feshin kwari domin yakar cutar ta Malariya.

    Shugaban hukumar Aimable Mbituyumuremyi ya ce suna yin hakan ne domin ganin bayan saurayen da ke haifar da cutar a fadin kasar.

    Cibiyar ta ce mutum miliyan 3.9 ne suka kamu da cutar malariya a shekarun biyun da suka wuce don haka feshin zai fi mayar da hankali a yankunan da aka fi kamuwa da ita.

  15. Ana neman kawo karshen Boko Haram, Kungiyoyi na neman hanyoyin da ba na soji ba domin magance matsalar

    Cibiyar bunkasa Fasahar sadarwa da ci gaba CITAD, tare da hadin guiwar Cibiyar Yada Al’adu ta Birtaniya, na neman lalubo wasu hanyoyi da ba na soji ba, domin takaitawa ko kawo karshen rikicin kungiyar Boko Haram.

    Hakan na zuwa ne sayan shafe shekara goma ana fama da rikicin kungiyar ba tare da kawo karshen tashin hankalin ba.

    Rikicin na Boko Haram ya yi sanadiyyar mutuwar dubban mutane tare tilasta wa wasu dubban daruwa gudun hijira baya ga asarar dukiya a yankin Arewa maso gabashin kasar.

  16. An dakatar da wasu masu sarautun gargajiya biyu

    A Najeriya gwamnatin jihar Zamfara ta sanar da dakatar da wasu mutane biyu masu rike da sarautun gargajiya a jihar.

    Sanarwar ta fito ne daga ma’aikatar harkokin kananan hukumomi da masarautun jihar, kuma sanarwar ta bayyana cewa tuni dakatarwar ta fara aiki tun daga jiya Litinin.

    Ga karin bayanin da Zahraddeen Lawan ya hada mana:

  17. An sanya dokar ta-baci a Nijar, Dokar ta shafi yankin Filinge

    An sanya dokar ta-baci a jamhuriyar Nijar a yankin Filingue mai makwabtaka da wasu yankunan jihar Tillabery da ke karkashin dokar.

    Sabuwar dokar wani mataki ne na riga-kafi don hana aukuwar abun da ke faruwa a wasu yankunan jihar.

    Ga rahoton Tchima Illa Issoufou:

  18. Mahara sun kashe mutum 50 a Burkina Faso, A makon jiya wasu mahara sun kashe mutum 36 a lardin Sanmatenga

    'Yan bindiga sun kashe gomman mutane a harin a wata kasuwa a Arewacin Burkina Faso.

    Akalla mutum 50 ne maharan suka kashe a kauyen Silgadji, inda hare-haren masu ikirarin jihadi ya lalata layukan sadarwa.

    Harin na kauyen Silgadji ya auku ne a ranar Asabar amma bayanin hakan bai samu ba sa daga baya.

    Kafar yada labaran kasar ta RTB ta tabbatar da faruwar hakan.

    A ranar 20 ga watan nan da muke ciki mahara sun kashe akalla mutum 36 a lardin Sanmatenga da ke kasar ta Burkina Faso.

  19. Zazzabin Lassa, Gwamnati ta fara aikin wayar da kan jama'a kan annobar

    Gwamnatin Najeriya ta umurci jami'an kula da muhalli a dukkan matakai su fara aikin wayar da kan jama'a game da cutar zazzabin Lassa da ta yi sanadiyyar mutuwar gomman mutane a kasar.

    Ministan Muhalli na kasar Mohammad Mahmood ya kuma umurci kwararru a fannin muhalli du su sanya ido domin gano matattaran beraye a masana'antu da cibiyoyin kasuwanci inda za a sa magunguna.

    Da ya sanar da hakan, ministan ya ce zuwa yanzu zazzabn cutar zazzabin Lassa ta yi ajalin mutum 29 yayin mutum 195 suka kamu da ita a jihohin kasar.

  20. Abubuwan da ke faruwa kai tsaye a Najeriya da sauran kasashe, Farawa

    Masu bibiyarmu barkanmu da wannan lokaci.

    Yau ma za mu ci gaba da kawo maku labaran abubuwan da ke faruwa kai tsaye a Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi da sauran kasashen duniya.

    Muna fatan za ku ci gaba da kasancewa tare da mu

    Don ganin labaran abubuwan da suka faru jiya sai ku yi kasa.