Shugaba Muhammadu Buhari na ganawa da hafsoshin tsaron kasar a fadar gwamnati da ke Abuja.
Jaridar The Nation ta rawaito cewa mutanen da suka hallara a wurin ganawar da ke gudana yanzu haka sun hada da sakataren gwamnati, Boss Mustapha da shugaban ma'aikata ga shugaban kasa, Abba Kyari da ministan tsaro Manjo Janar mai ritaya, Bashir Salihi Mahashi da ministan Harkokin cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola da kuma bai wa shugaban kasa shawara kan harkar tsaro Babagana Monguno.
Hafsoshin tsaron da suka hallara a wurin ganawar su ne hafsan hafsoshin kasar, Janar Gabriel Olonisakin da hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Tukur Buratai da hafsan sojin ruwa, Vice Admiral Ibok Ekwe Ibas da hafsan sojin sama, Air Marshall Sadique Abubakar da kuma sifeto janar na 'yan sanda Mohammed Adamu.
Sauran su ne darekta janar na hukumar leken asiri ta NIA, Ahmed Rufa’i Abubakar da darekta janar na hukumar tsaro ta farin kaya, DSS, Yusuf Magaji Bichi.
Babu wanda ya yi wa manema labarai karin bayani dangane da dalilin taron da aka fara da karfe 10 na safiyar Alhamis.
Sai dai a kan iya alakanta shi da kiraye-kirayen da majalisun dokokin Najeriya suka yi ta yi a ranar Laraba kan tabarbarewar harkar tsaro a kasar, ciki da masu kira da a cire hafsoshin tsaron.