Iraniyawa sun yi jana'izar Soleimani

Asalin hoton, Getty Images
Dandazon masu nuna alhini ne suka yi wa titunan birnin Tehran tsinke domin yi wa kwamandan sojin kasar, Qasem Soleimani jana'iza.
A ranar Juma'a ne dai aka kashe Soleimani yayin wani harin jirgi maras matauki da Amurka ta kai bisa umarnin shugaba Donald Trump.
Shugaban addinin Iran, Ayatollah Khamenei ne ya ja sallar inda har yake zubar da hawaye.
Kasar Iran dai ta sha alwashin "daukar fansar" kisan Soleimani, inda a ranar Lahadi ta fice daga yarjejeniyar nukiliyar Iran ta 2015.
Soleimani, mai shekara 62 na jagorantar dakarun kasar ta Iran a samame daban-daban a yankin Gabas ta tsakiya, inda Amurka take daukar sa a matsayin "dan ta'adda".
Shugaba Trump ya ce Soleimani na kitsa "karin hare-hare" a kan Amurka da Amurkawa a Iraqi da sauran sassan duniya.

Asalin hoton, Getty Images
