Abubuwan da suka faru a Najeriya da Nijar da duniya
Wannan shafin namu na kawo muku irin wainar da ake toyawa a Najeriya da Niger da Kamaru da Chadi da Ghana da sauran kasashen Afirka da ma fadin duniya.
A Najeriya, masana na ci gaba da kokarin ceto wasu harsuna da ke cikin barazanar bacewa a doron kasa.
A cewar masana akwai wasu daga cikin harsunan gida a Chadi, wadanda masu magana da su, ke raguwa a duniya, kuma matukar ba a dauki mataki ba, to babu shakka za su kare.
Wannan ta sa nan gaba a yau, Cibiyar nazarin Harsunan Najeriya ta Jami'ar Bayero Kano za ta gudanar da wani taron kara wa juna sani na duniya don lalubo hanyoyin kare harsunan.
Kyautar Gwarzon dan kwallon Afirka na 2019
Asalin hoton, Getty Images
Hukumar kwallon kafa ta Afirka, CAF za ta bayyana gwarzon dan kwallon kafa na nahiyar da babu kamarsa a 2019 ranar Talata.
Cikin guda ukun da za a zabi gwarzon bana sun hada da dan wasan tawagar Algeria da Manchester City, Riyad Mahrez da na Masar da Liverpool, Mohamed Salah da na Senegal da Liverpool, Sadio Mane.
Mane da Salah sun taimaka wa Liverpool ta lashe kofin Zakarun nahiyoyi, kuma Salah na takara karo na uku a jere.
Mahrez shi ne ya ja ragamar Aljeria ta lashe kofin nahiyar Afirka da aka yi a Masar, inda Mane ya taimaka wa Senegal zuwa wasan karshe a 2019.
Haka kuma za a bayyana gwarzuwar 'yar kwallon Afirka da babu kamarta a 2019.
Wadanda ke takara sun hada da Ajara Nchout ta tawagar Kamaru da kungiyar Valerenga da Asisat Oshoala ta Najeriya Barcelona da 'yar wasan tawagar Afirka ta Kudu mai taka leda a Beijing Phoenix, Thembi Kgatlana.
Koci-Koci da daraktan tsare-tsare da kyaftin din mambobin tawagogin kwallon kafar Afirka ne za su yi zaben gwarzayen Afirka na 2019.
Za a bayyana wadanda suka yi fice a Afirka a wani biki da CAF za ta gudanar a otal mai suna Hurghada da ke Masar.
Yara ne suka tayar da gurneti ba Boko Haram ba - Sojojin Kamaru
Asalin hoton, Getty Images
Rundunar sojin Kamaru ta ce abun fashewar dyhallaka mutum tara sannan ya raunata mutum 26 a Gamboru da ke makwabtaka da jihar Borno ba Boko Haram ba ne suka tayar da bam.
Sojojin sun ce bayan tsananta bincike sun gano cewa wasu kanana yara ne da ke wasa da gurneti suka haddasa al'amarin.
Mai da yawun rundunar sojin ta Kamaru Cyrille Serge Atonfack Guemo ya ce yara kanana guda biyu ne suna wasa sai suka tsinki gurnet inda suka kai kasuwa domin sayarwa, a inda gurnetin ya tashi.
Da farko dai kafafen yada labaran kasar sun ruwaito cewa kungiyar Boko Haram ta dauki alhakin kai harin.
Cikin wadanda suka jikkata har da wadanda suka fada cikin ruwa.
An kama daruruwan 'yan gudun hijirar Sudan a Nijar
'Yan sanda a Nijar sun damke 'yan gudun hijira 'yan asalin Sudan sama da 300 bayan wata zanga-zanga da suka yi a garin Agadez wanda hakan ya yi sanadiyar kusan kona sansanin 'yan gudun hijira.
Tun a watan da ya gabata 'yan gudun hijiran suke zanga-zanga a gaban ofishin Hukumar Majalisar Dinkin Duniya Mai Kula Da 'Yan Gudun Hijira (UNHCR) inda suke kira da a dubi lamarinsu domin tura su kasashen Turai.
A karshen makon nan ne dai 'yan sandan kasar suka afka musu domin tarwatsasu.
Jami'ai a kasar sun bayyana cewa wasu daga cikin 'yan gudun hijirar sun kona kusan dakunan katako 300 a sansanin.
Wakilin UNHCR da ke yankin tsakiya na Mediterranean ya wallafa hotuna a shafinsa na Twitter dangane da dakunan da aka kona.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Gwamnatin Kaduna ta hana sayar da gas a cikin unguwanni
Asalin hoton, El Rufa'i Twitter
Gwamnatin jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya ta ba da umarnin hana sayar da Gas din yin abinci a shagunan da ke unguwannin jama'a kwanaki kadan bayan wani ibtilain fashewar tukunyar gas a unguwar Sabon Tasha.
Mahukunta a jihar sun ce daga yanzu ana umartar masu sayar da gas din su koma rukununin unguwannin masana'antu ko ma bayan gari don kiyaye aukuwar irin wannan matsala a nan gaba.
Lamarin da ya faru a ranar Asabar ya yi sanadin mutuwar mutum shida ciki har da wani fitaccen masanin makamashin nukiliya da kasar ta ke alfahari da shi.
Asalin hoton, El Rufa'i Twitter
Asalin hoton, El Rufai Twitter
Buhari ba zai bayyana kadarorinsa ba'
Asalin hoton, Getty Images
Mai magana da yawun shugaban Najeirya, Femi Adeshina ya ce babu
wata doka da ta wajbata wa Shugaba Buhari bayyana wa 'yan kasa kadarorinsa.
Femi na wannan magana ne da yammacin ranar Litinin a lokacin
shirin gidan talbijin na Channels TV mai suna Politics Today.
Mai magana da yawun na shugaba Buhari ya mayar wa da kungiyar
SERAP martani ne wadda a ranar Lahadi ta nemi shugaba Buhari da mataimakinsa
farfesa Yemi Osinbajo da su bayyana wa 'yan kasa kadarorinsu.
Har wa yau, kungiyar ta SERAP ta kuma umarci gwamnonin jihohin
kasar 37 da su ma su bayyana kadarorin nasu.
SERAP, a wata snaarwa da ta fitar ranar
Lahadin ta ce "rashin bayyana kadarorin shugaba na dasa alamar tambaya
dangane da gaskiyarsa da rikon amanarsa.”
To sai dai mai maganar da yawun shugaban
ya ce ba haka ba ne inda ya ce babu wata doka da ta wajabta wa shugaban kasa
bayyana kadarorinsa.
Ko ya ya sunan wannan tsuntsu?
Asalin hoton, Getty Images
Farawa
Masu bibiyarmu da fatan kun tashi lafiya. A yau Talata za mu ci gaba da kawo muku irin wainar da ake toyawa a Najeriya da Niger da Kamaru da Chadi da Ghana da ma sauran kasashen Afirka da duniya baki daya. Da fatan za ku biyo mu.
Janye sojojin Chadi zai janyo karin hare-hare a Najeriya
Bayanan sautiMalam Kabiru Adamu
Masu sharhi kan lamuran tsaro na ci gaba da tsokaci kan
hare-hare da ake ci gaba da samu jefi-jefi a kasashen yankin Tafkin Chadi inda
mayakan Boko Haram da na kungiyar ISWAP ke kai wa sojoji da fararen hula
farmaki.
Ko a karshen mako, rahotanni na cewa an yi artabu tsakanin sojin
Nijeriya da mayakan da ake jin na ISWAP ne a kusa da garin Jakana dake kan
hanyar Maiduguri zuwa Damaturu inda aka samu hasarar rayuka a bangarorin
biyu.
Kuma a makon da ya
gabata masu tayar da kayar baya sun kai hari a yankunan Michika da Madagali na
jihar Adamawa.
A bangare guda kuma rundunar sojin Chadi ta ce ta janye
sojojinta na rundunar hadingwiwar kasashen yankin wadanda ke aiki a cikin
Nijeriya.
Malam Kabiru Adamu, mai sharhi ne kan lamuran tsaro kuma ya yi wa
Is’haq Khalid karin bayani kan yadda yake kallon lamarin.
Enyimba ta kori kocinta Usman Abdallah
Asalin hoton, @EnyimbaFC
Kungiyar Enyimba mai rike da kofin gasar Firmiyar Najeriya ta Nigerian Professional Football League (NPFL), ta kori kocinta Usman Abdallah a ranar Litinin.
Wani bayani da kungiyar ta fitar a yau Litinin ya bayyana cewa korar ta fara aiki ne nan take, sannan ta ce Fatai Osho ne zai maye gurbinsa na rikon kwarya.
Korar Abdallah ta zo ne bayan kashin da kungiyar ta sha 0-4 a hannun Plateau United ranar Lahadi.
Enyimba tana matsayi na 13 a teburin Firimiyar bayan wasa 10, inda ta ci hudu kacal.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
"Bayan fuskantar sakamako marasa dadi, kungiyar ta amince cewa wajibi ne ta sauya salon wasanta a gida da kuma nahiyar Afirka," Enyimba ta bayyana.
Shugaban kungiyar Felix Anyansi Agwu ya ce: "Wannan mataki ba abu ne da muka dauka cikin sauki ba ko kuma hanzari".
Kungiyar PENGASSAN a Najeriya na son a cire babban daraktan Chevron
Asalin hoton, Getty Images
Kungiyar manyan ma'aikatan man fetur da iskar gas ta Najeriya, PENGASSAN reshen kamfanin mai na Chevron, ta bukaci da a sauke shugaba kuma babban daraktan kamfanin na Chevron Mista Jeff Ewing.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya ruwaito ma'aikatan kamfanin na yin zanga-zanga yanzu haka a fadin Najeriya.
Ma'aikatan sun bayyana cewa sun yi hakan ne domin bayyana rashin kwarin gwiwarsu ga shugabancin kamfanin.
Kazalika sun nemi da a sauke shi sannan kuma kada a sake nada shi a kan wani mukami "saboda rashin gaskiyarsa".
An yi garkuwa da mutum 30 a Katsina
Asalin hoton, Facebook
Rahotanni na cewa wasu masu garkuwa da jama'a sun yi awon gaba da fasinjoji kimanin 30 a karamar hukumar Batsari da ke jihar Katsina.
An dai ce da misalin karfe 6:00 na yammar ranar Lahadi ne masu garuwar dauke da muggan makamai suka yi awon gaba da mutanen da ke kan hanyarsu ta komawa gida daga kasuwar Jibiya, mai makwabtaka.
Masu garkuwar dai sun tare mutanen ne a cikin motoci guda biyu.
Dan majalisar dokokin jihar Katsina, mai wakiltar karamar hukumar ta Batsari, Alhaji Yusuf Jabir ya tabbatar wa da BBC faruwar al'amarin.
Batun satar jama'a domin neman kudin fansa dai na kara kamari a jihar Katsina.
Ko a makon da ya gabata sai da masu garkuwar suka shiga har cikin gidan wata amarya suka yi awon gaba da ita a karamar hukumar Dutsen Ma.
Jihar
Katsina na cikin jihohin da suka cimma sulhu da `yan bindiga, amma harin da ake
kaiwa a baya-bayan nan na nuna cewa sulhun na fuskantar barazana.
Tun
lokacin da gwamnatocin jihohin Katsina da Zamfara ke maganar sulhu da `yan
bindiga, wasu masu sharhi a kan harkokin tsaro sun yi gargadin cewa wasu `yan
bindigar za su iya mai da shirin wata hanyar tatsar gwamnati.
Sai an biya mu kudaden da muka kashe sannan mu bar Iraki - Trump
Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar kakaba wa Iraki takunkumi bayan da majalisar dokokin Irakin ta amincewa da korar sojojin Amurkar fiye da 5000 da ke kasar.
"Muna da sansanin sojoji mai matukar tsada da ke can. Mun kashe biliyoyin daloli wajen gina shi. Ba za mu fice daga kasar ba har sai sun biya mu abin da muka kashe."
Ana ci gaba da samun tankiya tun bayan kashe janar Qasem Soleimani da Amurkar ta yi ranar Juma'a a birnin Bagadaza.
Kasar Iran dai ta sha alwashin daukar "fansa"
Soleimani, mai shekara 62 na jagorantar dakarun kasar ta Iran a samame daban-daban a yankin Gabas ta tsakiya, inda Amurka take daukar sa a matsayin "dan ta'adda".
Tuni dai aka yi jana'izar Soleimani a kasarsa wato Iran inda 'yan kasar suka yi dandazo a titunan kasar da sanyin safiyar ranar Litinin.
Turkiyya ta tura sojoji Libya
Shugaba Turkiyya,Recep Tayyip Erdogan ya ce dakarun kasarsa sun fara shiga kasar Libya bayan da majalisar dokokin kasar ta amince da yunkurin nasa a makon da ya gabata.
Erdogan ya ce ya dauki matakin tura sojin ne Libya da manufar taimaka wa gwamnatin da ke da goyon bayan Mjalisar Dinkin Duniya ci gaba da zama ba tare da samun barazana ba.
Gwamnatin Libya dai na rikici da masu tayar da kayar baya karkashin Janar Khalifa Haftar da ke a gabashin Libya.
Janar Haftar dai na samun goyon bayan Misra da UAE, inda kuma gwamnatin da Mjaalisar Dinkin Duniya ta kafa take da goyon bayan Turkiyya da Qatar.
'Yan tawayen dai na kokarin mamaye birnin Tripoli, inda ake zargin su da kai wnai harin sama kan wata kwalejin soji a birnin ranar Asabar inda akalla mutum 30 suka mutu.
Sai dai 'yan tawayen sun musanta aikata hakan.
Asalin hoton, Getty Images
'Yan sanda sun kama Bobi Wine
Asalin hoton, Getty Images
'Yan sanda a Uganda sun jefa hayaki mai sa kwalla sannan sun hana ftaccen mai kida da waka kuma dan majalisar Uganda, Bobi Wine yin taro a birnin Kampala na kasar.
Hakan na zuwa ne a lokacin da yake kokarin fitar da manufofinsa dangane da zaben kasar da za a yi a badi, inda yake fatan tsayawa takarar shugabancin kasar.
An dai dauki Bobi Wine wato Robert Kyagulanyi, zuwa ga wani ofishin 'yan sanda.
Shugaba Yoweri Museveni, wanda ya hau mulki shekaru 33 da suka gabata ka iya sake neman tazarce kamar yadda 'yan kasar ke zargi.
Manema labarai na cewa shugaba Musevini ba shi da hakurin jure wa abokan hamayya saboda haka Bbi Wine ka iya fuskantar kalubale daga shugaban.
Wata jarida mai zaman kanta ta wallafa wasu hotuna a shafinta na Twitter inda 'yan sanda ke tarwatsa wani taron masu neman takarar kujearar shugaban kasa.
Ana yi wa shugaba George Weah zanga-zanga
Asalin hoton, Getty Images
An fara wata zanga-zangar a birnin Manrovia na kasar Liberia kan tuhuma ga shugaban kasar, George Weah.
Kashin farko na masu zanga-zangar dai ya kutsa ne ta shingayen da 'yan sanda suka daddasa a kusa da fadar gwamnati.
Gomman 'yan sandan kwantar da tarzoma ne suke shawagi a yankin da fadar shugaban kasar take.
Masu zanga-zangar dai na neman shugaba Weah wanda tsohon dan kwallo ne ya wallafa jerin kadarorinsa na kafin kasancewarsa shugaban kasa da yanzu bayan ya zama shugaban.
Har wa yau, mutanen na son shugaba ya yi bayani dangane da dala milyan 25 da gwamnati ta fitar daga asusun ko-ta-kwana na kasar da ya kamata a yi amfani da su wajen farfado da tattalin arzikin kasar.
Rundunar 'yan sandan Najeriya na cikin shirin ko-ta-kwana kan kisan Soleimani
Asalin hoton, Getty Images
Rundunar sojin Najeriya ta baza 'yan sanda a fadin kasar bayan da Amurka ta kashe kwamandan sojin kasar Iran, Qasem Soleimani.
A ranar Juma'a ne dai wani jirgin Amurka maras matuki ya hallaka Soleimani tare da wasu sojojin sa-kai na Iraqi a Baghdad.
A ranar Lahadi ne dai rundunar 'yan sandan ta wallafa sanarwa a shafinta na Twitter cewa sifeto janar na kasar ya umarci 'yan sandan kasar su kasance cikin ko-ta-kwana.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Rundunar dai ba ta bayar da wani dalilin daukar wannan mataki ba sai dai ana ganin hakan ba ya rasa nasaba da irin alakar da ke akwai tsakanin mabiya kungiyar Islamic Movement of Nigeria ta Sheikh Zakzaky da kasar Iran.
Ko a ranar Juma'ar da abin ya faru sai da 'yan kungiyar suka fitar da wata sanarwar Alla-wadai da kisan da Amurkar ta yi wa Qasem Soleimani, al'amarin da ke nuni da cewa 'yan kungiyar ka iya yin jerin gwanon nuna kyamar al'amarin a Najeriya.
'Yan bindiga sun kashe sojojin Najeriya hudu
Asalin hoton, Getty Images
Wasu 'yan bindiga masu ikrarin jihadi sun kashe sojojin Najeriya guda hudu sannan sun jikkata 11 yayin wani hari da suka kai wani sansanin soji da ke gabas maso arewacin Najeriya.
Kamfanin dillancin labarai ya rawaito cewa wata majiyar soji ce ta tabbatar masa da faruwar harin da aka kai ranar Lahadi.
Mayakan kungiyar IS da ke lardin Afirka ta Yamma, ISWAP sun isa sansanin sojin ne da ke Jakana kusa da birnin Maiduguri a cikin motoci kirar a-kori-kura guda shida inda suka bude wuta a kan sojin da yammacin ranar Asabar.
To sai dai majiyar ta shaida wa AFP cewa dakarun sun fatattaki 'yan bindigar bayan kwashe lokaci mai tsawo ana ba-ta-kashi
A 'yan makonnin nan dai kungiyar ISWAP ta kara kaimin kai hare-hare a yankin na arewa maso gabas, inda take harin sojoji tare kuma da shigar burtu ta hanyar kakkafa shingayen irin na sojoji da manufar yi wa jama'a kwantan bauna.
Sai dai har kawo yanzu rundunar sojin Najeriya ba ta ce uffan ba dangane da wannan hari.
Me jama'a ke fadi dangane da sanyin da ake a Arewacin Najeriya?
Bayanan sautiYadda sanyi ya rikita 'yan Najeriya
'Yan Najeriya da dama na fadin irin halin da suke ciki dangane da yanayin sanyin da ake yi a Arewacin Najeriya a bana.
Hukumar binciken yanayi a Nijeriya NIMET dai ta ce akwai yiwuwar sanyin da ake fuskanta a kasar zai karu nan gaba cikin 'yan kwanaki masu zuwa.
Ta ce sanyin da ake samu a Najeriyar ya karu ne saboda gudun iskar da ke tasowa daga arewa maso gabas mai kunshe da laima ya karu inda a wasu lokuta har takan kai gudun kilomita 100 cikin sa'a daya.
'Akwai yiwuwar sanyin da ake fuskanta a Najeriya zai karu'
Bayanan sautiFarfesa Sani Abubakar Mashi, Daraktan Hukumar binciken yanayi ta Najeriya.wato NIMET
Hukumar binciken yanayi a Nijeriya NIMET ta ce akwai yiwuwar sanyin da ake fuskanta a kasar zai karu nan gaba cikin 'yan kwanaki masu zuwa.
Ta ce sanyin da ake samu a Nijeriya ya karu ne saboda gudun iskar da ke tasowa daga arewa maso gabas mai kunshe da laima ya karu inda a wasu lokuta har takan kai gudun kilomita 100 cikin sa'a d'aya.
Al'umma da dama ne a kasashen Afirka ta Yamma musamman Najeriya ke kokawa saboda karuwar sanyi a bana.
Farfesa Sani Abubakar Mashi, Daraktan Hukumar binciken yanayi ta Najeriya.wato NIMET ne ya shaida wa BBC hakan.