Abubuwan da suka faru a Najeriya da Nijar da duniya

Wannan shafin namu na kawo muku irin wainar da ake toyawa a Najeriya da Niger da Kamaru da Chadi da Ghana da sauran kasashen Afirka da ma fadin duniya.

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir and Umar Rayyan

  1. Mutum 65 Gobara ta kashe a Kaduna a 2019

    Gobara

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar kashe gobara ta jihar Kaduna ta bayyana cewa an samu afkuwar gobara sau 523 sannan kuma mutum 65 ne suka mutu a jihar a tsakanin watan Janairun 2019 zuwa Disamba.

    Babban daraktan hukumar Mista Paul Aboi ne ya bayyana hakan ranar Laraba a wata hira da kamfanin dillancin labarai na NAN, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

    Ya ce akasarin gobarar ta faru ne sakamakon rashin kulawa da kyau yayin amfani da kayayyakin lantarki da kuma rashin sanin yadda za a tunkari wayar lantarki da ba a rufe take ba.

    Aboi ya kara da cewa an fi samun afkuwar gobarar a watan Dismaba."Akasari gobara ta fi afkuwa daga watan Disamba zuwa Afrilu saboda gari a bushe yake a wannan tsakanin," in ji Aboi.

    Sannan ya ce sun ceto mutum 63 da ransu, sai 141 da suka samu raunuka da kuma 65 da suka rasa ransu bayan kiraye-kirayen neman dauki da suke samu.

  2. Sudan ta rufe gidajen jaridu da ke da alaka da al-Bashir

    .

    Asalin hoton, Getty Images

    Sudan ta rufe kamfanonin buga jaridu biyu da kuma gidajen talabijin biyu a kasar sakamakon alakarsu da Tsohon Shugaban kasar Omar al-Bashir.

    An dai zargi kafafen da karbar kudade daga tsohon shugaban kasar.

    Kwamitin da aka kafa domin bincike da kuma rufe cibiyoyin da tsohon shugaban yake da alaka da su ne ya rufe Jaridun Al-Sudani da Al-Ray Al-Am da kuma gidajen talabijin na Ashrooq da kuma Teeba.

    Daya daga cikin dan kwamitin da aka kafa na rikon kwarya a Sudan din Mohamed al-Fekki, ya shaida cewa ''an yi amfani da kudaden kasa domin gudanar da wadannan cibiyoyi, muna so mu mayar wa 'yan Sudan kudinsu''.

    Sai dai babban editan jaridar Al-Sudani Diaa al-Din Belal ya musanta karbar kudade daga gwamnatin al-Bashir.

  3. An toshe intanet a gabashin Habasha

    Kafafen sada zumunta

    Asalin hoton, Getty Images

    Yankuna da dama a gabashin Habasha wato Ethiopia na fuskantar katsewar layin intanet tun ranar Litinin.

    A wasu yankunan ma har layin kiran waya aka toshe. Sai dai kamfanin sadarwa daya tilo na gwamnati, Ethiotelecom bai yi karin bayani ba game da toshe layuykan.

    Mai magana da yawun kamfanin ya shaida wa BBC cewa ba zai iya cewa komai ba amma kamfanin zai fitar da sanarwa a hukumance nan gaba kadan.

    Babu tabbaci kan ko toshewar tana da alaka da rikice-rikicen da suka faru a cikin shekaru biyu da suka wuce, wanda ya yi sanadiyyar kashe wasu jami'an gwamnati a yankin.

    A shekarar da ta gabata, Habashar ta rufe layin intanet lokacin da ake gudanar da jarabawar makarantun sakandare ta kasa baki daya da kuma lokacin da aka samu tashin hankali mai alaka da kabilanci a kasar.

  4. Farashin mai ya tashi bayan harin da Iran ta kai

    getty i

    Asalin hoton, Getty Images

    Farashin danyen mai ya tashi bayan da wasu makmai masu linzami suka afkawa wasu sansanonin sojojin Amurka biyu da ke Iraki.

    Farashin danyen mai samfurin Brent ya tashi da kashi 1.4 cikin 100 inda ake sayarwa kan $69.21 kowace gangar mai daya a kasuwar mai ta Asia.

    Su ma ma'adinan kasa kamar gwal da kudin Japan Yen sun tashi bayan da aka kai harin.

    Kazalika hannun jari a duniya ya yi kasa sakamakon rikicin da ake yi a yankin gabas ta tsakiya.

  5. Jam'iyyar SDF a Kamaru ta fara janye 'yan takararta

    s

    Asalin hoton, SDF

    Rahotanni daga Kamaru na cewa Jam'iyyar adawa a kasar, SDF ta fara janye 'yan takaranta na zaben kananan hukumomi daga wasu mazabu, musamman ma ta yankin renon ingila inda jam'iyyar ta fi samun magoya baya.

    Jam'iyyar ta yi haka ne bisa ga barazanar da take ta samu daga masu fafutuka da ke yunkurin kafa kasarsu ta Ambazonia.

    Cikin sanarwar da suka fitar, masu fafutukar sun lashi takobin daukar mataki kan duk wani wanda ya fita kada kuri'a ranar 9 ga watan Fabrairu.

    Dangane da haka ne kuma suka kafa dokar hana fita da za ta fara aiki daga ranar 5 zuwa 12 na watan Fabrairu.

  6. Jihar Akwa Ibom ta sayi sabbin jirage 2

    Ibom Airlines

    Asalin hoton, @ibomairlines

    Bayanan hoto, A watan Yuni jirgin Ibom Airlines ya fara aiki

    Gwamnatin jihar Akwa Ibom a Najeriya ta sayo sababbin jirage guda biyu ga kamfanin Ibom Airlines, inda jiragen kamfanin mallakar jihar suka zama biyar jumulla.

    Shugaban kamfanin, Air Commodore Idongesit Nkanga mai ritaya, ya ce za a kaddamar da sabon jirgin ne a watan nan na Janairu, a cewar rahoton kamfanin dillancin labarai na NAN.

    Ya kara da cewa kamfanin ya yi jigilar fasinja har kusan sau 3,000 tun daga lokacin da ya fara aiki a watan Yuni, sannan kuma ya ci gaba da fadada harkokinsa.

    Nkanga ya bayyana cewa kafin shekarar 2023 jihar za ta sayi jirgi 10, yana mai cewa gwamnati ta zuba jari mai yawa a harkar sufurin jirgin sama domin bunkasa hanyoyin samar da kudaden shigar jihar.

  7. Cutar kyanda ta kashe sama da mutum 6,000

    AFP/GETTY

    Asalin hoton, AFP/GETTY

    Hukumar lafiya ta duniya WHO ta bayyana cewa yawan mutanen da cutar kyanda ta kashe a Jamhuriyyar Dimokradiyyar Congo sun sun haura 6,000.

    Hukumar ta bayyana cewa cutar ita ce cutar da ta fi bazuwa a duniya.

    Ta kuma bayyana cewa an samu kusan mutum 310,000 da ake zargin sun kamu da cutar tun a farkon 2019.

    A Satumbar da ta gabata ne gwamnatin Congo tare da hadin gwiwar hukumar WHO suka gudanar da rigakafin gaggawa kan cutar kyandar .

    Sama da yara miliyan 18 ne aka yi musu rigakafin cutar a shekarar bara.

  8. Labarai da dumi-dumi, 'Yan Iran 82 sun mutu a hatsarin jirgin sama

    .

    Asalin hoton, Getty Images

    Jirgin saman Ukraine da yayi hatsari a Iran na dauke da 'yan kasar Iran 82.

    Ministan harkokin wajen Iran Vadym Prystaiko ne ya tabbatar da hakan inda ya bayyana cewa akwai 'yan Birtaniya uku da hatsarin ya rutsa da su wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutum sama da 170.

    Sauran 'yan kasashen da hatsarin ya rutsa da su kamar yadda ministan ya shaida sun hada da:

    • 'Yan Canada 63
    • 'Yan Ukraine 11, ciki har da ma'aikatan jirgin
    • 'Yan kasar Sweden 10
    • 'Yan Afghanistan hudu
    • 'Yan kasar Jamus uku

    Ofishin jakadancin Ukraine da ke Tehran ya bayyana cewa matsalar inji ce ta yi sanadiyar hatsarin jirgin ba wai harin ta'addanci ba.

  9. Harin bam ya raunata mutum 11 a Somaliya

    An samu fashewar bam a Mogadishu babban birnin Somaliya.

    Bam din ya fashe ne cikin wata mota a kan wata hanya mai cike da hada-hadar motoci a garin na Mogdishu.

    Rahotanni sun bayyana cewa a kalla mutum 11 sun samu raunuka sakamakon tashin bam din.

    Sai dai babu wata kungiyar da ta dauki nauyin kai harin .

    Kwanaki 10 da suka wuce sai da aka samu irin wannan harin a kasar inda mutane 90 suka mutu inda kuma sama da 100 suka samu raunuka.

    .

    Asalin hoton, Getty Images

  10. Likitoci 78 sun yi nasara a tiyatar raba jarirai a Najeriya

    ,

    Wasu likitoci a Najeriya sun samu nasarar raba wasu jarirai 'yan biyu da ke hade da juna.

    Likitan da ya jagoranci tiyatar raba jariran Emmanuel Ameh ya shaida wa BBC cewa tiyatar da aka gudanar domin raba Goodness da Mercy ta yi nasara kuma a halin yanzu suna da cikakkiyar lafiyar da za a iya sallamar su daga asibiti domin tafiya gida.

    Ya bayyana cewa tiyatar da aka gudanar ta lashe kusan dalar Amurka dubu 55.

    Mista Emmanuel ya ce tiyatar na cike da sarkakiya kuma likitoci 78 ne suka kwashe kusan sa'o'i 12 suna gudanar da ita.

    Sai dai an bayyana cewa likitocin da ke a Babban Asibitin Tarayya na Abuja ba su caji kudin aikin ba sakamakon mahaifan jariran wato Michael Edeh da Maria Onya Martins ba su da halin biyan kudin.

    .
  11. Jirgin Ukraine ya yi hatsari a Iran

    Wani jirgin Ukraine Boeing-737 dauke da mutum sama da 170 ya yi hatsari a Iran.

    Kungiyar agaji ta Red Crescent a Iran ta ce yana da wahala a samu wanda ya rayu.

    Rahotanni sun ce jirgin ya yi hatsari ne jim kadan bayan ya tashi a tashar jirgin sama ta Imam Khomeini a Tehran.

    Jirgin ya tashi ne da nufin zuwa Kyiv babbar birnin Ukraine. Gwamnatin Ukraine ta ce za ta kaddamar da bincike kan hatsarin.

    .

    Asalin hoton, Getty Images

  12. Farawa

    Masu bibiyarmu da fatan kun tashi lafiya. A yau Laraba za mu ci gaba da kawo muku irin wainar da ake toyawa a Najeriya da Niger da Kamaru da Chadi da Ghana da ma sauran kasashen Afirka da duniya baki daya. Da fatan za ku biyo mu.

  13. Cardi B na son masoya su zaba mata sabon suna

    Cardi B

    Asalin hoton, Getty Images

    Mawakiyar nan Cardi B ta ce tana neman takardar shaidar zama 'yar Najeriya bayan da Amurka ta kashe Kwamandan Iran.

    Mawakiyar 'yar Amurka mai salon wakar "rap" ta nemi shawarar masoyanta da su zabar mata suna irin na 'yan Najeriya.

    Ta bayar da zabi guda biyu kan sunan da take so wato tsakanin Chioma B da kuma Cadijat.

    An sake wallafa rubutun da tayi a tuwita fiye da sau 10,0000.

    Jaridar Premium Times ta Najeriya ta ruwaito cewa an rada mata sunan Chioma B irin na 'yan Najeriya, a ziyararta ta farko da ta kai wa Najeriya a Disambar 2019, yayin da kuma jaridar ta ce masoyanta musulmai 'yan arewacin kasar, sun zabar mata sunan Cadijat.

    A ranar uku ga watan Janairun shekarar nan ne Cardi B ta wallafa a shafinta na tuwita cewar, tana neman takardar shaidar zama 'yar kasar Najeriya bayan da Shugaba Trump na Amurka ya ba da umurnin kashe Kwamandan Iran Qasem Soleimani.

    Shugaba Trump ya ce suna da tabbacin cewa, Soleimani na shirya kai hare-hare wa Amurka kuma sun kashe shi ne a harin jirgi da Amurkan ta kai wa Bagadaza ranar Juma'a.

    Mawakiyar ta ce wannan shi ne mafi munin mataki da Shugaba Trump ya taba dauka.

    Kisan ya janyo tashin hankali a yankuna da dama, yayin da Iran ke barazanar 'ramuwar gayya'.

  14. Tinubu ya kai wa Buhari ziyara

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya tattauna da jagoran jam'iyyar APC mai mulki a kasar wato Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

    Mai mai ba da shawara ga shugaba Buhari kan shafukan sada zumunta, Bashir Ahmed ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa mutanen biyu sun tattauna a yau Talata a fadar shugaban kasar da ke Abuja.

    Tinubu dai ya taka muhimmiyar rawa a zaben Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a zaben 2015 da kuma 2019.

    @BashirAhmaad

    Asalin hoton, @BashirAhmaad

  15. An bayar da belin uwar gidan mataimakin shugaban Zimbabwe

    Getty Images

    Asalin hoton, Getty Images

    Kotu ta bayar da belin Uwar Gidan Mataimakin Shugaban kasar Zimbabwe Constantino Chiwenga kan dala 50,000 bayan an kama ta a watan da ya gabata bisa zargin yunkurin kashe mijinta da kuma zargin ta da almundahana da kuma halarta kudin haram.

    Kotun dai ta bai wa Mary Munaiwa umarnin bayar da fasfonta da kuma takardun wata kadara da ta mallaka da aka yi rajisata da sunan mahaifinta duk a cikin sharuddan beli.

    Sai dai ta musanta duka zarge-zargen da ake yi mata. Kotun bata bayyana ranar da za a ci gaba da sauraren karar ba.

    Masu gabatar da kara sun zarge ta da yunkurin kashe Janar Chiwenga yayin da yake jinya a wani asibiti a Afirka ta Kudu.

    Janar Chiwenga dai ya jagoranci rundunar sojin kasar da ta sa baki wajen tilastawa tsohon shugaban kasar Zimbabwe marigayi Robert Mugabe ya yi murabus a 2017.

  16. Gwamnan Borno ya zargi sojoji da 'karbar na goro'

    Hakkin mallakar hotoFACEBOOK/@GOVBORNO

    Asalin hoton, FACEBOOK/@GOVBORNO

    Tun bayan da gwamnan jihar Borno farfesa Umar Babagana Zulum, ya yi kakkausar suka dangane da abin da ya kira 'karbar na goro' da sojojin Najeriya ke yi a shingayen da suke kafawa a manyan titunan fadin jihar, jama'a ke ta fadin albarkacin bakinsu a kafafen sada zumunta.

    Gwamnan dai ya kai wata ziyarar bazata ne ga wani shingen da sojoji suka kafa da ke kan babbar hanya a garin Jimtilo.

    An dai ce gwamna Zulum da kansa ya ba da hannu ga cincirindon motocin da suka yi cirko-cirko a kan titin na Jimtilo, inda mutane suka yi ta yada wa a kafafen sada zumunta.

    To sai dai jim kadan bayan kalaman na gwamna Zulum, mai magana da yawun ayyukan rundunar, Kanar Aminu Ilyasu ya mayar da martani, inda ya nuna rashin jin dadin rundunar dangane da kalaman gwamnan.

  17. Soja ya daba wa soja wuka

    getty images

    Asalin hoton, Getty Images

    An samu fargaba a jihar Osun da ke Kudancin Najeriya bayan wani soja ya caka wa 'yar uwarsa soja wuka da kuma wani farar hula.

    Jaridar Daily Trust a Najeriya ta ruwaito cewa sojan mai suna Blessed Olodi ya kashe abokiyar aikinsa mai suna Iyabo.

    An bayyana cewa tuni aka kai gawar Misis Iyabo asibitin koyarwa na Obafemi Awolowo da ke jihar Osun.

    Mazauna garin Ede da ke jihar Osun sun shaida cewa tun a ranar 2 ga watan Janairu sojan ya fara afkawa jama'a inda har ya raunata matarsa da yaransa hudu.

    Sai dai runduna ta biyu ta sojin Najeriya ta shaida cewa ana gudanar da bincike dangane da lamarin kuma za a sanar da sakamakon binciken idan an kammala.

  18. Kwamandan Sojin Najeriya ya tsallake rijiya da baya

    Getty Images

    Asalin hoton, Getty Images

    Kwamandan Operation Lafiya Dole, Janar Olusegun Adeniyi ya tsallake rijiya da baya bayan 'yan kungiyar Boko Haram sun yi kwantar bauna ga ayarin motocinsa a ranar Litinin a hanyar Jakana da ke jihar Borno.

    Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa wani daga cikin sojojin kasar ya shaida musu cewa kwamandan yana hanyarsa ne ta komawa Maiduguri bayan wata ziyara da ya kai wa wasu dakarun da aka tura garin Jakana ba da dadewa ba.

    An tura jami'an sojin ne zuwa Jakana domin kare rayuka da dukiyoyin al'ummar yankin daga Boko Haram.

    An ruwaito cewa motar da kwamandan yake ciki ta sha ruwan harsasai wanda hakan ya sa motar ta yi kaca-kaca.

  19. Ana zanga-zanga a Guinea Conakry

    Dubban masu zanga-zangar kin gwamnati ne suka hau tituna a birnin Conakry na Guinea da ma sauran birane domin nuna adawa da gwamnatin kasar.

    Rahotanni sun ce akalla mutum 12 sun samu raunuka a garin Kankan da ke gabashin kasar bayan da masu zanga-zangar suka yi arangama da magoya bayan shugaba Alpha Conde.

    Masu zanga-zangar sun yi shigar jajayen kaya domin nuna goyon bayansu ga masu hamayya.

    Tun dai watan Oktoba ne dai ake ta faman gudanar da zanga-zangar nuna kin jinin Alpha Conde mai shekara 81 wanda ake zargin yana shirin yi wa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima domin yin tazarce, a karo na uku.

    Guinea Conakry

    Asalin hoton, Get

  20. Mutum '35' sun mutu a turmutsutsun jana'izar Soleimani

    Getty Images

    Asalin hoton, Getty Images

    A kalla mutum 35 ne suka mutu a wani turmutsutsu a Iran yayin da 'yan kasar ke tururuwa zuwa wajen jana'izar babban kwamandan kasar da aka kashe yayin wani hari da Amurka ta kai.

    Hukumomin kasar ba su da takamaimai adadin mutanen da aka kashe, sai dai jami'an ko ta kwana sun tabbatar da mace-mace da dama.

    Rahotanni sun bayyana cewa sama da mutane 40 sun raunata.

    Za rufe Qasem Soleimani a birnin Kerman, inda aka yi kiyasin miliyoyin mutane sun taru a wurin jana'izarsa.

    Kashe shi da aka yi ya janyo fargabar yaki tsakanin Amurka da Iran, har ma wasu na tunanin kashe shi kan iya jawo yakin duniya na uku.

    Kafin rasuwarsa, ana ganin cewa shi ne na biyu a wurin karfin iko a kasar ta Iran bayan jagoran addinin kasar Khamenei.

    Amurka dai na kallon Soleimani a matsayin ''dan ta'adda'' kuma barazana ga sojojin Amurka.