Mu kwana lafiya
Mun zo ƙarshen rahotonni a wannan shafin, wanda ya kawo labarai daga sassan duniya a ranar Talata.
Mu haɗu gobe da safe domin samun wasu sababbi.
Wannan shafi ne da zai kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 24/09/2024
Usman Minjibir, Isiyaku Muhammed, da Umar Mikail
Mun zo ƙarshen rahotonni a wannan shafin, wanda ya kawo labarai daga sassan duniya a ranar Talata.
Mu haɗu gobe da safe domin samun wasu sababbi.
Rundunar sojin Isra'ila ta ce hare-haren da take kai wa Hezbollah a kudancin Lebanon na taƙaitaccen lokaci ne, amma kuma a shirye take idan hakan zai ɗauki lokaci.
Maimagana da yawun rundunar, Daniel Hagari, ya ce: "Muna ƙoƙarin mu ga mun kammala cikin ƙanƙanin lokaci, dalilin da ya sa kenan muke kai hari da ƙarfi sosai, amma kuma dole ne mu shirya ko da hakan zai ɗauke mu tsawon lokaci."
"Babbar manufarmu ita ce cim ma burinmu na mayar da mazauna arewacin Isra'ila gidajensu, kuma dole ne mu dage kan hakan."

Asalin hoton, Reuters
Shugabannin ƙasashen duniya da ke jawabi a babban taron Majalisar Dinkin Duniya (MDD) sun yi kira da a dakatar da rikicin da ke ƙara tsanani tsakanin Isra'ila da kungiyar Hezbollah ta Lebanon.
Shugaba Biden ya shaida wa shugabannin duniya cewa babu wanda yake sha'awar yaƙi a Gabas ta Tsakiya, "kuma za a iya amfani da diflomasiyya wajen samar da mafita".
Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres ya shaida wa taron cewa "duniya ba za ta zuba ido wata ƙasa ta koma kamar Gaza ba".
Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, Shugaban Iran Masoud Pezeshkian wanda ya halarci taron a New York ya zargi MDD da rashin ɗaukar mataki kan Isra'ila.

Asalin hoton, State Government
Kwamitin da gwamnatin Kano ta kafa don duba halin da madatsun ruwan jihar ke ciki ya tabbatar da cewa wasu daga cikin madatsun ba su fuskantar barazanar ɓallewa.
Gwamnati ta ce ta ɗauki matakin tura jami’ai su gudanar da bincike ne sakamakon ambaliyar ruwan da aka samu a jihar Borno sakamakon madatsar ruwan Alau da ta ɓalle
Jihar Kano na da ɗumbin madatsun ruwa da ake amfani da su wajen noman rani da kuma samar da ruwan sha ga al’ummar jihar.
Kwamashinan Ruwa Ali Haruna Makoɗa ne ya jagoranci tawagar zuwa manyan madatsun ruwan.
"Jiya [Litinin] mun je Tiga, yau kuma mun zo Watari. Mun ga wurin da idan ya cika ake fitar da ruwan kuma lafiya yake...Amma mun ga wurin da zaizayar ƙasa ta ɗan shafi wurin," in ji shi.
Bayanai sun nuna cewa Kano na da manyan madatsun ruwa 19 mallakar gwamnatin jihar da ta tarayya, da kuma 46 ƙanana.
Injiniya Marwan Ahmad Aminu, shi ne kwamashin ma'aikatar ayyuka, kuma ya ce sun lura akwai 'yar matsala a jingar da aka yi wa madatsar ruwa ta Tiga.
"Mun ga akwai 'yar matsala amma dai ba wata gagarumar matsala ba ce, kuma muna da bayanin cewa gwamnatin tarayya ta turo tawagar da za ta yi wannan gyaran," a cewarsa.

Asalin hoton, EPA
Jakadan Isra'ila a Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) ya ce ƙasarsa a shirye take ta tattauna hanyoyin da za a kawo ƙarshen rikici a Lebanon.
Kamfanin labarai na Reuters ya ruwaito Danny Danon na cewa: "Ba mu zumuɗin kai samame ta ƙasa kan kowace ƙasa," kamar yadda ya faɗ wa manema labarai.
"Mun fi son hanyoyin difilomasiyya," a cewarsa.

Asalin hoton, Reuters
Ministan kula da ayyukan agajin gaggawa na Lebanon, Naser Yasine, ya faɗa wa BBC cewa akwai mutum 28,000 da ke samun mafaka yanzu haka a makarantun gwamnatin ƙasar.
Ya ce mutane da dama da suka guje wa gidajensu a kudancin ƙasar na zaune a gidajen haya, da na abokansu ko kuma 'yan'uwa.
Akwai kuma ayyukan da ƙungiyoyi da yawa ke yi na taimaka wa mutanen da ke gudun hijirar.

Asalin hoton, Reuters
Gwamnatin Lebanon ta sanar da rufe duka makarantun yara da ke faɗin ƙasar har zuwa ƙarshen makon nan.
Sauran makarantu da jami'o'i ma za su rufe a wanna tsakanin.
A 'yan kwanakin nan, an yi ta mayar da makarantu sansanonin fakewa na mutane da ke tsere wa hare-haren Isra'ila kan Hezbollah a ƙasar.

Asalin hoton, CBN
Babban Bankin Najeriya (CBN) ya ce ƙarin kuɗin ruwa da dinga yi akai-akai ya taimaka wajen ƙarfafa gwiwar 'yan ƙasar game da tunaninsu kan takardun kuɗi na naira.
Gwamnan CBN Olayemi Cardoso ya ce kuma bayyana matakin bankin na sake ƙara kuɗin ruwan zuwa kashi 27.25 a yau Talata jim kaɗan bayan kammala taron kwamatin harkokin kuɗi.
Hakan na nufin duk mutumin da ya ci bashin banki yanzu sai ya biya kuɗin ruwan kashi 27.25 na kuɗin da ya karɓa. CBN na cewa yana yin hakan ne da zimmar rage hauhawar farashi.
"Mun kusa faɗawa matsalar zagayawar kuɗi tsakanin jama'a a 2017 zuwa 2023, kuma mun ga yadda aka dinga zuba kuɗi a hannun jama'a," in ji shi yana mai zargin wanda ya gada, Godwin Emefiele.
"A 2015, yawan kuɗin da ke zagayawa a hannun jama'a sun kai naira biliyan 19, a 2023 kuma tiriliyan 54. Wannan babban ƙari ne...Saboda haka buga takardun kuɗin na jawo yawan kuɗi.
"Saboda haka, mun yi imanin cewa yawan ƙara kuɗin ruwan ya taimaka wa mutane wajen sauya tunani game da takardun kuɗin, kuma yanzu akwai alfanu mai girma idan mutum yana riƙe da naira ba kamar a baya ba."
A ƙarƙashin Cardoso - wanda ya fara aiki a watan Satumban 2023 - ana canzar da dala ɗaya kan naira 1,600, saɓanin N700 da ake canzarwa a lokacin da ya kama aikin.

Asalin hoton, Getty Images
Sojojin Isra'ila sun ce za su zafafa hare-haren da suke kai wa Hezbollah a Lebanon, bayan luguden wutar da ta yi a ranar Litinin wanda ya yi sanadiyyar mutuwar ɗaruruwan mutane.
Ministan Lafiya na Lebanon Firass Abiad ya ce an kashe sama da mutane dari biyar da hamsin tun daga lokacin da Isra'ila ta fara ƙaddamar da hare-hare a ranar Litinin.
Ya ƙara da cewar mata da yara ƙanana kusan ɗari da hamsin na daga cikin waɗanda suka rasa rayukan nasu.
Mutane da dama na ci gaba da tserewa daga gidajensu a kudancin Lebanon
Wakiliyar BBC ta ce har yanzu Isra'ila ba ta bayyana wa'adin da za ta ɗauka tana ƙaddamar da hari ko kuma kai farmaki ta ƙasa ba, abin da ake ta hasashe a yanzu.
To sai dai Hezbollah ta bayyana cewar ta kai wa sojin Isra'la hare-hare a Arewacin Isra'ila.
Kasashen duniya sun sake yin kira da a kawo karshen faɗa tsakanin Isra'ila da Hezbollah.
Babban kwamishinan kare haƙƙin bil'adama a Majalisar Ɗinkin Duniya, Volker Turk, ya nemi dukkanin bangarorin da suke fada-a ji a yankin Gabas ta Tsakiya su taimaka a dakile rikicin.
Ma'aikatar harkokin wajen Chaina ta ce Beijing ta yi Allah Wadai da karya ka'idojin tsaron Lebanon.
Shugaban Iran Masoud Pezeshkian ya ce bai kamata duniya ta ƙyale Isra'ila ta mayar da Lebanon wata Gaza ba.
Ya kuma kara da cewa Hezbollah, wadda Tehran ke goyon baya, ba za ta iya yaƙar Isra'ila ita kadai ba.

Asalin hoton, Getty Images
Hukumomi a arewa maso yammacin Pakistan sun yi kira da a gudanar da taron shugabannin ƙabilu bayan rikicin da ya ɓarke tsakanin wasu ƙabilu biyu wanda ya yi sanadiyar mutuwar aƙalla mutane 13 a lardin Khyber Pakhtunkhwa.
Fadai ya ɓarke a ranar Asabar ɗin da ta gabata sakamakon rikicin filaye a yankin Kurram.
An jikkata gomman mutane lokacin da ɓangarorin biyu ɗauke da manya da ƙananan makamai suka yi arrangama .
Rikicin na baya-bayan nan ya samo asali ne bayan 'yan ƙauye daga wata ƙabila sun yi ƙoƙarin haka ramuka a filin da ake taƙaddama a kai.
Rikicin ya fantsama ɓangarori da dama na yankin. A watan Yulin bana, aƙalla mutane 10 aka kashe a wani rikici kwatankwacin wannan.

Asalin hoton, Getty Images
Masu gabatar da ƙara a Sweden, sun zargi Hukumar Leƙen Asirin Iran da kutsawa manhajar aikawa da saƙonnin Sweden don aika dubban sakonnin kiran ɗaukar fansa kan mutanen da suka ƙona Alƙur'ani.
Wani binciken Hukumar Leken Asirin Sweden ya bayana cewar saƙonnin dubu goma sha biyar aka aike a watan Agustan bara.
Wakilin BBC ya ce sun ce ba wani abu ba ne, illa yunƙurin haifar da rabuwar kai tsakanin al'umar Sweden da kuma son ayyana Sweden a matsayin ƙasa mai ƙyamar addinin Islama.
Gwamnatin Sweden ta yi alawadai da yada aka bayar da damar ƙona Alƙur'ani a shekarar da ta gabata saboda kariyar da doka ta yiwa ƴancin fadin albarkar baki.

Asalin hoton, Getty Images
Shugabannin ƙasashen duniya sun hallara a birnin New York don babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya.
Ƙoƙarin hana ɓarkewar rikicin yankin Gabas ta Tsakiya na sahun gaba cikin batutuwan da za a tattauna ya yin taron.
Joe Biden zai yi taƙaitaccen jawabi a taron, wanda shi ne lokaci na ƙarshe da zai bayyana a zauren MDD a matsayinsa na shugaban Amurka.
Wani babban jami'in ma'aikatar harkokin waje ya ce Washington na da wasu shawarwari da ta ke son tattaunawa da kawayenta, sannan kawayen Amurkan za su haɗa ne da waɗanda suke da alaƙa da Hezbollah.

Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya ce yaƙin da ƙasarsa ke yi da Rasha ya kusa zuwa ƙarshe.
"Ina ganin mun fi kusa da samun zaman lafiya yanzu, kawai dai akwai buƙatar mu ƙara juriya."
Ya bayyana haka ne a zantawarsa da kafar ABC News ta Amurka, inda ya ce tsarin samun nasarar da zai gabatar wa shugaban ƙasar Amurka Joe Biden a wannan makon zai buƙaci "ƙarin taimakon soji" daga ƙawayen ƙasar.
Zelensky ya ce tsarin ba wai neman sulhu da Rasha ba ne,"tsari ne na gyara diflomasiyya da kuma kawo ƙarshen yaƙin."
Ya ƙara da cewa da tsarin ne Ukraine za ta yi amfani wajen matsa wa shugaban ƙasar Rasha Vladimir Putin lamba domin ya kawo ƙarshen yaƙin.
A ranar Talata, kakakin Fadar Gwamnatin Rasha, Dmitry Peskov ya ce Rasha na bi a hankali ne wajen jawabi a kan tsarin da Ukraine ke magana a kai, amma ya ƙara da cewa yaƙin zai zo ƙarshe ne kawai idan Rasha ta cimma burinta.
Zelensky ya daɗe yana kira ga ƙasashen Yamma su ba Ukraine damar amfani da makamai masu linzami masu dogon zango domin kai wa Rasha hare-hare, sannan ana tunanin zai sake miƙa wannan buƙatun a wannan makon idan ya je Amurka.
A ranar Lahadi, Biden ya ce har yanzu bai yanke shawarar sahale wa Ukraine wannan damar ba, shi kuma Zelensky ya ce Amurka ce yake so ta shige gaba wajen ɗaukar wannan matsaya. "Kowa na jiran Biden ne, sannan kuma muna buƙatar wannan domin kare kanmu," kamar yadda ya bayyana wa ABC.
A ranar Laraba ce Zelensky zai gabatar da jawabi a gaban zauren majalisar MDD, sannan zai gana da ƴan takarar shugabannin Amurka Donald Trump da Kamala Haris.

Asalin hoton, NDLEA
Jami'an hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Najeriya, NDLEA sun ce sun kama wani mutum ɗauke da hodar iblis mai nauyin kilogiram 19.4 da kuɗinta ya kai naira biliyan huɗu da miliyan 606.
NDLEA ta ce mutumin ya taho ne daga ƙasar Ethiopia inda kuma ya sauka a filin jirgin sama na Legas, kuma a nan ne jami'an hukumar suka yi ram da mutumin ranar Talata.
Hukumar ta ce mutumin dai mai shekara 48 ɗan Najeriya ne wanda aka taɓa aikewa da shi kurkuku bisa tuhumar safarar miyagun ƙwaya a bara, amma ya zaɓi ya biya tara domin gujewa zaman gidan kaso.
Shugaban hukumar Mohammed Buba Marwa dai ya sha alwashin sanya ƙafar wando ɗaya da duk masu safarar ƙwayar a Najeriya.

Asalin hoton, Getty Images
Kociyan Manchester United, Erik ten Hag ya ce ya kamata a yadda da dalilin da ya sa Marcus Rashford ya zauna a benci a wasa da Crystal Palace.
Ƙungiyoyin biyu sun tashi 0-0 a wasan mako na biyar a babbar gasar tamaula ta Ingila ranar Asabar.
Tun kafin karawar Ten Hag ya sanar da cewar Rashford ya fara komawa kan ganiya, wanda ya zura ƙwallo uku a raga a wasa biyu.
To sai dai kawai aka ga Rashford a benci, inda Ten Hag ya zaɓi fara amfani da Alejandro Garnacho da Amad Diallo, daga baya ne Rashford ya canji Joshua Zirkzee.
Mai yiwa Sky Sports sharhi da bayanin wasannin, Jamie Redknapp ya ce hakika da akwai wani abun da ya faru da ta kai an ajiye Rashford a benci.
Haka shima Gary Lineker da Alan Shearer ba su gamsu da dalilin da ya sa Ten Hag ya ajiye dan ƙwallon Ingila a benci ba a karawa da Palace.
An tambayi Ten Hag ranar Talata kan makomar Rashford, sai kociyan ya ce kowa yana da damar faɗin albarkacin bakinsa, amma bai kamata ake yaɗa jita-jita ba.
Ranar Laraba United za ta kara da FC Twenty a Europa League a Old Trafford, sannan ta karbi bakunci Tottenhama a Premier League ranar Asabar.

Asalin hoton, Getty Images
Real Madrid za ta karɓi bakuncin Deportivo Alaves a wasan mako na bakwai a La Liga da za su kara a Santiago Bernabéu ranar Talata.
Real tana makaki na biyu a kan teburin La Liga da maki 14, bayan cin wasa hudu da canjaras biyu.
Ita kuwa Alaves maki 10 ne da ita a mataki na bakwai, bayan nasara a karawa uku da canjaras daya aka doke ta fafatawa biyu.
Sun kara a bara a babbar gasar tamaula ta Sifaniya, inda Real Madrid ta je ta ci Alaves 1-0 ranar Alhamis 21 ga watan Disambar 2023.

Asalin hoton, EPA
A faɗin kudancin Lebanon, iyalai da dama na rububin kwaso kayayyakinsu ne suna shiga mota suna komawa arewacin ƙasar a motoci ƙanana da manya da babura a daidai lokacin da Isra'ila ke cigaba da luguden wuta a yankunan da ta ce tana harin Hezbollah.
Rahotanni na nuna cewa wasu daga cikin mutanen yankin sun samu saƙonnin wayar salula da saƙonnin murya daga sojojin Isra'ila cewa su bar yankunan da ke da ƴan ƙungiyar ta Hezbollah wadda ke samun goyon bayan Iran.
Zahra Sawli, wata ɗaliba ce da ke kudancin garin Nabatieh ta bayyana wa shirin Newshour na BBC cewa luguden wutar ya tsananta.
"Na farka da misalin ƙarfe shida na safiya kawai na fara jin ƙarar bama-bamai. Da rana sai hare-haren suka ƙara tsananta."
Ku shiga nan domin karanta Cikakken labarin

Asalin hoton, Getty Images
Wani sabon bincike ya nuna cewa gandun daji mafi girma a duniya na Amazon, ya rasa wani yanki na dazuka da girmansa ya kai a haɗa ƙasar Jamus da Faransa sakamakon sare dajin da ake yi a cikin shekaru 40.
Rahoton da gamayyar ƙungiyoyi da masu bincike na RAISG suka gabatar, ya ce wannan ya taka muhimmin rawa wajen ƙaruwar matsalolin fari da gobarar daji a yankunan Kudancin Amurka, da kuma fitar da iskar da ke gurbata muhalli.
Dajin Amazon da ya kewaye ƙasashen 9 na da matukar muhimmanci a yaƙin da ake yi da matsalolin sauyin yanayi a duniya.

Asalin hoton, Getty Images
Ministan lafiya na ƙasar Lebanon, Firass Abiad ya ce mutum 558 ne hare-haren Isra'ila suka kashe sannan 1,800 suka jikkata daga ranar Litinin zuwa yanzu.
Da yake magana a wani taron manema labarai, ministan ya shaida wa ƴanjarida cewa mutum 1,835 ne suka jikkata a tashin bama-baman inda ya ce ma'aikatan lafiya na iya ƙoƙarinsu wajen kula da marasa lafiyar.
Abiad ya ƙara d acewa ma'aikatan lafiya huɗu sun mutu a ranar Litinin lokacin da Isra'ila ta antayo hari kan wata motar ɗaukar marasa lafiya.
Dangane kuma da mutum fiye da 500 da aka kashe, ministan ya ce 50 daga ciki ƙananan yara ne.
Bayanai dai sun nuna cewa ranar Litinin ta fuskanci hare-hare mafi muni a Lebanon tun shekarar 1990 lokacin yaƙin basasa.

Asalin hoton, BSG
Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya ƙaddamar da aikin raba tallafi ga mutane fiye da miliyan biyu da ambaliyar Maiduguri ta shafa.
Magidanta 5,235 ne a yankin Gwange 1 suka fara amfana da tallafin da gwamnan ya ƙaddamar ranar Talata.
Gwamnan ya ce gidajen mutum 587 da suka amfana daga tallafin sun rushe baki ɗaya inda magidanta 2,365 kuma gidajensu suka samu ƴar matsala sannan mutum 2,283 kuma nasu gidajen sun ɗan taɓu.
Gwamnan ya ce tallafin zai kasance hawa-hawa, inda waɗanda suka samu ƴar matsala a gidajen nasu za su samu naira dubu 100 da ƙaramin buhun shinkafa da wake da tabarmi da barguna da gidan sauro.
Sauran kuma waɗanda ambaliyar ko dai ta rushe musu gida baki ɗaya ko kuma ta illata shi za su karɓi abin da ya dace asarar da suka yi.
Farfesa Zulum ya kuma kara sanar da jama'a cewa yawan kuɗin tallafin da suka samu daga gwamnatoci da ɗaidaikuwar al'umma sun kai naira biliyan 7.5 ya zuwa lokacin ƙaddamar da rabon tallafin ranar Talata.
A ranar Litinin ne dai gwamnan ya ƙaddamar da kwamitin mutum 32 da zai ɗauki alhakn yin rabon tallafin ga al'ummar da ambaliyar ta shafa, inda a lokacin ya sanar da cewa an yi wa al'ummar alƙawarin gudunmowa da ta kai yawan naira biliyan 13,195,500,000.

Asalin hoton, BSG

Asalin hoton, BSG

Asalin hoton, BSG

Asalin hoton, BSG

Asalin hoton, BSG