Real Madrid ta doke Alaves da ci uku da biyu a La Liga

Asalin hoton, Getty Images
Real Madrid ta doke ƙungiyar Alaves da ci uku da biyu a wasan da a wasan mako na bakwai a La Liga da aka fafata a filin wasa na Santiago Bernabéu a ranar Talata.
Vinicius jr da Kylian Mbappe da Rodrigo ne suka tura ƙwallaye a ragar Alaves, kafin daga bisani Alaves ta farke ƙwallo biyu.
Real tana makaki na biyu a kan teburin La Liga da maki 14, bayan cin wasa biyar da canjaras biyu.
Ita kuwa Alaves maki 10 ne da ita a mataki na takwas, bayan nasara a karawa uku da canjaras ɗaya, sannan aka doke ta fafatawa uku.
Sun kara a bara a babbar gasar tamaula ta Sifaniya, inda Real Madrid ta je ta ci Alaves 1-0 ranar Alhamis 21 ga watan Disambar 2023.
A wasa na biyu kuwa a Bernabeu, Real ta yi nasara 5-0 a kan Alaves ranar Talata 14 ga watan Mayun 2024.
Ranar Juma'a 20 ga watan Satumba Alaves ta doke Sevilla 2-1 a wasan mako na shida, ita kuwa Real ta yi nasara a kan Espanyol 4-1 ranar Asabar 21 ga watan Satumba.
Tuni kociya, Carlo Ancelotti ya bayyana ƴan wasan da Real Madrid za ta kara da Alaves a Bernabeu.









