Yadda luguden wutar Isra'ila ke sa dubban jama'a barin garuruwansu a Lebanon

Jami'ar sibil defens na Lebanon tana rarrashin wata mata da ta iso Beirut bayan ta tsere daga kudanci

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Jami'ar sibil defens na Lebanon tana rarrashin wata mata da ta iso Beirut bayan ta tsere daga kudanci
    • Marubuci, Orla Guerin, Nafiseh Kohnavard and Carine Torbey
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
    • Aiko rahoto daga, Beirut
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 5

A faɗin kudancin Lebanon, iyalai da dama na rububin kwaso kayayyakinsu ne suna shiga mota suna komawa arewacin ƙasar a motoci ƙanana da manya da babura a daidai lokacin da Isra'ila ke cigaba da luguden wuta a yankunan da ta ce tana harin Hezbollah.

Rahotanni na nuna cewa wasu daga cikin mutanen yankin sun samu saƙonnin wayar salula da saƙonnin murya daga sojojin Isra'ila cewa su bar yankunan da ke da ƴan ƙungiyar ta Hezbollah wadda ke samun goyon bayan Iran.

Zahra Sawli, wata ɗaliba ce da ke kudancin garin Nabatieh ta bayyana wa shirin Newshour na BBC cewa luguden wutar ya tsananta.

"Na farka da misalin ƙarfe shida na safiya kawai na fara jin ƙarar bama-bamai. Da rana sai hare-haren suka ƙara tsananta."

"Na ji ƙararrakin fashewar gilasai."

Amma ba kamar wasu ba, ita Zahra da waɗanda suke gida ɗaya ba za su iya barin gidan cikin sauƙi ba.

"Ina za mu je? mutane da dama sun maƙale a titunan garin. Yanzu haka akwai wasu ƙawayena da suka maƙale a hanya saboda motoci sun yi yawa a hanya kasancewar mutane da dama suna ta ƙoƙarin tserewa," in ji ta.

Ko da yamma ta yi, hanyoyin zuwa Beirut sun cika maƙil da motoci da sauran ababen hawa, inda mutane suka cika hanyoyin tafiya da dawowa baki ɗaya saboda sauri.

Wasu hotunan kuma sun nuna mutane suna wucewa ta kusa da wani wajen shaƙatawa a kudancin ƙasar, a can baya kuma hayaƙi ya turnuƙe ta sama.

BBC ta zanta da wasu iyalai su biyar da suka iso Beirut a kan babur ɗaya da suka taso daga wani ƙauye a kudanci, suna hanyar zuwa Tripoli da ke arewaci a gajiye.

"Me kake so mu ce maka? ai dole ne mu tsere," in ji mai gidan.

Iyalan mutum biyar a babur ɗaya.

Asalin hoton, Hassan Harfoush

Bayanan hoto, "Me kake so mu ce maka? ai dole ne mu tsere," in ji mai gidan a zantawarsa da BBC.
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Da yammacin ranar Litinin, Ma'aikatar Lafiyar Lebanon ta ce mutum 492 sun mutu, sannan sama da 1,600 sun jikkata a hare-haren. Ta ce aƙalla ƙananan yara 35 ne suka mutu, a daidai lokacin da Rundunar Tsaron Isra'ila wato IDF ta ce ta kai hare-hare guda 1,100 a cikin awa 24.

Daga cikin hare-haren akwai wanda ta kai kudancin Beirut, wanda IDF ta ce tana harin wani babban kwamandan Hezbollah ne.

A Beirut ma ana cikin zullumi da fargaba. A daidai lokacin da mutane suke rububi daga kudancin ƙasar zuwa babban birnin ƙasar a motoci da kayayyakinsu, wasu daga cikin mazauna birnin ma suna tserewa.

Isra'ila ta gargaɗi mutane su bar yankunan da suka ce ƴan Hezbollah suna ajiye makamai - amma kuma sun tura saƙonni ga mutanen gundumar Beirut da ba sa cikin yankunan da Hezbollah ke da ƙarfi irin su Hamra, yankin da ke cike da ofisoshin gwamnati da bankuna da jami'o'i.

Iyayen sun yi rububin zuwa makaranta domin kwashe ƴaƴansu bayan sun samu saƙonnin barin yankunan.

Wani mahaifi, Issa ya je ya ɗauko yaronsa a makaranta, inda ya bayyana wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa, "mun zo ɗaukar yaranmu ne saboda kiranmu da aka yi ta waya.

"Suna ta kiran mutane suna musu barazana ta wayar salula. Wannan ya sa na zo domin in ɗauki ɗana dagaa. Yanayin ƙasar babu kwanciyar hankali," in ji shi.

Wasu mutane ɗauke da kayayyakinsu suna wucewa ta wani wajen shaƙatawa a Tyre a kudancin Lebanon a ranar Litinin.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Wasu mutane ɗauke da kayayyakinsu suna wucewa ta wani wajen shaƙatawa a Tyre a kudancin Lebanon.

Mohammed, wani ɗan Falasɗinu ne da BBC ta tarar a hanya tare da matarsa yana hanyar barin Beirut.

Da aka tambaye shi ko zai cigaba da zama a babban birnin, sai ya ce, "yanzu a Lebanon babu inda ake da kwanciyar hankali. Isra'ila na cewa za ta yi luguden wuta a ko'ina ne. Yanzu ta fara yin barazana ga babban birnin ma, ina za mu je ke nan?"

"Lamarin akwai tayar da hankali, ban ma san yaya zan yi ba - aiki zan cigaba da ya yi ko gida zan koma, na ruɗe baki ɗaya."

An mayar da wasu makarantu zuwa sansanonin wucin gadi ga mutanen suka gudu daga kudancin ƙasar kamar yadda gwamnati ta bayar da umarni.

BBC ta samu shiga wani aji a makarantar Bir Hassa da ke yammacin Beirut a ranar Litinin, inda mutanen da suka zo daga Bekaa Valley suka samu mafaka - yankin da Hezbollah ke da matuƙar ƙarfi - wanda Isra'ila ta ce tana shirin kai wa hari.

Gidajen man fetur ma sun cika a Beirut.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Gidajen man fetur ma sun cika a Beirut.

Bayan haka, an umarci asibitoci su dakatar da dukkan tiyatar da ba dole ba ne domin likitoci su kasance cikin shirin jinyar waɗanda suka ji rauni.

Amma duk da tashin hankali da fargabar da ake fama da su a Beirut, wasu ko gezau.

"Idan ma an fara yaƙin dole mu tsaya mu haɗa kai domin goya wa ƙasarmu baya ba tare da la'akari da bambancin siyasa ba, domin ko ba komai, ƙasarmu ce ake jefa wa bama-baman," kamar yadda wani mutum ya bayyana wa BBC.

"Idan yaƙi suke so a yi, mu yaya za mu yi? babu yadda za mu yi," kamar yadda wani mai shago Mohammed Sibai ya bayyana wa Reuters.

Mohammed mai shekara 57 da ke zaune Dahieyh a kudancin Beirut - asalin yankin Hezbollah - ya shaida wa BBC cewa ya "tsira daga dukkan yaƙoƙin da ake yi tun daga 1975," don haka "na riga na saba."

"Babu inda zan je. Zan cigaba da zama a gidana," in ji shi.