Fernandes ne gwarzon marubuta labarin tamaula na 2026

Wannan shafi ne da zai ke kawo muku labaran wasannin BBC Hausa daga 4 zuwa 8 ga watan Mayun 2026.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. Khvicha Kvaratskhelia yana da hannu a cin ƙwallaye 15 (ya ci 10 ya bayar da biyar aka zura a raga) — tarihi ga PSG. Ya ci bakwai a knockout; an wasa kaɗan ne suka wuce shi kamar Cristiano Ronaldo da Lionel Messi, da Karim Benzema.

    Tun bayan zagaye na 16, Kvaratskhelia ya zama ɗan wasa na huɗu da ya shiga cikin masu cin ƙwallaye a wasanni shida a jere a knockout, bayan Kaká, Edin Džeko, da Ousmane Dembélé.

  2. Paris Saint-Germain za ta koma filin da ta lashe kofin UEFA Champions League a bara, lokacin da za ta kara da Bayern Munich a wasa na biyu a daf da karshe ranar Laraba.

    Kocin PSG, Luis Enrique, yana tuna filin Bayern Munich kenan yana bukatar ƙarin ƙwarin gwiwa. PSG ta ci wasan farko da ci 5-4 a Faransa, kuma yanzu za ta je filin Bayern, Allianz Arena, da ɗan ƙaramin rinjayen ƙwallo ɗaya.

    A wannan filin ne PSG ta lashe kofinta na farko a Champions League a bara, bayan da ta doke Inter Milan da ci 5-0 a wasan ƙarshe.

    Haka kuma, Luis Enrique ya taba lashe wannan gasar ta zakarun Turai a shekara goma da suka gabata lokacin yana horar da Barcelona, inda ƙungiyarsa ta yi nasara a kan Bayern Munich a matakin kusa da na ƙarshe.

    Luis Enrique

    Asalin hoton, Getty Images

  3. Bayern Munich ta ci ƙwallaye 20 a wasanni biyar a zagayen knockout — matsakaicin huɗu a wasa, mafi girma a tarihi. PSG kuma ta ci 22 a wasanni bakwai.

    Ƴan wasan Bayern Munich sun yi gudu 40 ba tare da ƙwallo ba a wasan farko; mafi yawa a kakar nan. Aleksandar Pavlović ya yi 11 daga ciki.

  4. , Bayern Munich v Paris St-Germain

    Nasarar da Paris Saint-Germain ta yi 5-4 kan Bayern Munich a wasan farko, ita ce mafi yawan ƙwallaye da aka zazzaga a wasan daf da karshe a European Cup tun bayan da Eintracht Frankfurt ta doke Rangers 6-3 a kakar 1959-60.

    A jimillar wasanni biyu, tarihin yawan cin ƙwallaye mafi yawa a daf da karshe a wannan karon (16), inda Frankfurt ta yi nasara 12-4.

    lIVE

    Asalin hoton, Getty Images

  5. , Bayern Munich v Paris St-Germain

    Bayern Munich za ta kara da Paris St Germain a wasa na biyu a daf da karshe a Champions League da za su fafata a Jamus.

    A makon jiya Paris St Germain ta ci 5-4 a karawar daf da karshe daaka ci ƙwallo tara.

  6. Za mu kawo muku wasan Bayern Munich da PSG kai tsaye anjima

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

  7. Wannan shi ne karo na biyu da Arsenal ta kai wasan karshe a Champions League.

    Za ta zira wadda za ta fuskanta tsakanin Bayern Munich da Paris St Geramin.

    Ranar Laraba Bayern Munich za ta karbi bakuncin PSG a wasa na biyu na daf da karshe a gasar ta zakarun Turai.

    A wasan farko a makon jiya PSG ce ta yi nasara da cin 5-4.

    Shin wa zai hadu da Arsenal a wasan karshe a Budapest a Champions League?

  8. , Arsenal 1-0 Atletico Madrid

    Babbar murna daga ‘yan wasan Arsenal da ma’aikatan ƙungiyar.

    Sun kai wasan ƙarshe a Champions League karo na farko tun 2006, kuma karo na biyu kacal a tarihin su.

    Wasan ya bugu kuma kowa ya samu dama, Arsenal ce da nasara.

  9. An tashi wasan, Arsenal 1-0 Atletico Madrid

    ARSENAL TA KAI WASAN KARSHE A CHAMPIONS LEAGUE'

    Liv

    Asalin hoton, Getty Images

  10. , Arsenal 1-0 Atlético Madrid

    Arsenal na ƙara kusantar zuwa wasan karshe sosai.

    Yanzu kuma Mikel Arteta ya samu katin gargadi.

    liv

    Asalin hoton, Getty Images

  11. , Arsenal 1-0 Atlético Madrid

    Arsenal na ta kokari a waɗannan mintuna na ƙarshe sosai da kyau.

    Amma Atlético ba ta matsa musu da yawa ba.

  12. Karin lokaci, Arsenal 1-0 Atletico Madrid

    An yi karin minti biyar, lokacin da ya rage Arsenal ta kai wasan karshe a Champions League.

  13. , Arsenal 1-0 Atlético Madrid

    Alex Baena ya yi wani yunƙurin buga kwallo da ƙarfi, wanda ya sa magoya bayan Arsenal suka yi ta kuwa, amma ƙwallon ta wuce sama da raga.

    Minti ɗaya kawai ya rage tare da ƙarin lokaci a tashi daga wasan nan kowa ya kama gabansa.

  14. , Arsenal 1-0 Atlético Madrid

    Kash! Abin tausayi sai kuka ake ana ta zubar da hawaye a ɓangaren magoya bayan Atlético Madrid. Ba su da lokaci mai yawa don su farke ƙwallon, kuma gaskiya a wannan lokaci ba ya nuna kamar za su iya dawowa cikin wasannan.

  15. , Arsenal 1-0 Atletico Madrid

    Gabriel Martinelli ya shiga fili ya kuma canji Leandro Trossard - kuma lokaci yana ta kurewa.

  16. , Arsenal 1-0 Atletico Madrid

    An bugo ƙwallo mai kyau daga Marcos Llorente zuwa cikin akwatin bugun daga kai sai mai tsaron raga, amma David Raya ya karkatar da ita, kuma babu wanda ya jo daga baki ko zai yi wani abun..

    Lokaci yana ƙurewa Atlético.

  17. , Arsenal 1-0 Atletico Madrid

    Ko yaya kociyan Atletico ke ji kuwa?

    Liv

    Asalin hoton, Getty Images

  18. , Arsenal 1-0 Atletico Madrid

    Maritn Zubimendi ya maye gurbin Myles Lewis-Skelly. Saura minti 15 Arsenal ta kai wasan karshe a Champions League.

    Liv

    Asalin hoton, Getty Images

  19. Me Arteta ke cewa ga Arsenal, Arsenal 1-0 Atletico Madrid

    Liv

    Asalin hoton, Getty Images

  20. , Arsenal 1-0 Atletico Madrid

    Lallai Viktor Gyökeres ya kamata ya tabbatar da tikitin Arsenal zuwa wasan ƙarshe a nan!

    An kai wata ƙwallo da sauri mai kyau cikin akwatin bugun daga kai sai mai tsaron raga, sai ya buga ta kai tsaye ta kuma yi kyau, amma ta wuce saman raga. Wata dama ce mai kyau, amma dai ana sa ran ƙwallon za ta shiga raga, amma hakn bai samu ba.

    Liv

    Asalin hoton, Getty Images