Fernandes ne gwarzon marubuta labarin tamaula na 2026

Wannan shafi ne da zai ke kawo muku labaran wasannin BBC Hausa daga 4 zuwa 8 ga watan Mayun 2026.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. Champions League: Wane jan aiki ne a gaban Arsenal?

    Ƙwarewar Luis Enrique wajen gina ƙungiya na nufin cewa Arsenal na da jan aiki a gaba a wasanta na ƙarshe a gasar zakarun Turai wato Champions League da ƙungiyar Paris Saint-Germain.

    PSG ce ta samu nasara a wasan da aka yi a daren ranar Laraba, duk da cewa canjaras aka yi, amma PSG ce ta yi nasara da jimillar ƙwallo 6-4.

    Tun a minti na uku ne ɗan asalin Georgia, Khvicha Kvaratskhelia ya kwaso ƙwallo ta gefe sannan ya jefa wa dodon raga Ousmane Dembele, wanda shi kuma ya ƙarasa ta zuwa cikin raga.

    Duk da ƙoƙarin da Harry Kane ya yi na rama ƙwallo daga baya, hakan bai sauya wani abu ba. Latsa nan domin ci gaba da karanta labarin.

    Liv

    Asalin hoton, Getty Images

  2. PSG za ta yi ƙoƙarin hana Arsenal mamaye wasan da riƙe ƙwallo

    Paris St-Germain na iya ƙoƙarin yin koyi da dabarar Atletico Madrid ta hanyar hana Arsenal mamaye wasan ta hanyar riƙe ƙwallo, mai yiwuwa da tsarin mutum-da-mutum.

    Ƙwazon ƴan wasa irin su Ousmane Dembele, Khvicha Kvaratskhelia da Desire Doue a gaba zai kasance domin tilasta wa Arsenal yin kuskuren rasa ƙwallo da wuri, wanda zai iya haifar da manyan damar cin ƙwallo ga PSG, ko kuma su tilasta musu da buga dogayen ƙwallaye, suna dogaro da Marquinhos da Willian Pacho wajen samun tamaula daga sama.

    Da yake Mikel Merino, wanda yake da ƙwarewa a wasan sama, ba zai buga ba, yayin da Kai Havertz zai dawo bayan jinya, idan Viktor Gyokeres ne fuskanci masu tsaron bayan PSG, to zai yi wa Arsenal wahala wajen riƙe ƙwallo a gaba.

    A wasan da suka yi da Bayern Munich, PSG ta yawaita tsare gida da da tsarin mutum-da-mutum. Idan suka yi hakan ga Arsenal, Gunners na iya ƙoƙarin amfani da gudun ta wajen kai hare-hare.

    A wani bangaren kuma, PSG na iya komawa tsare baya, idan Arsenal ta samu damar mamaye wasan da riƙe ƙwallo kamar yadda ta yi a kakar bara.

    A waɗancan wasannin, Gianluigi Donnarumma ne ke tsaron raga, kuma bajintarsa ta taimaka wa PSG sau da dama. Amma da yake Matvey Safonov ne ke tsaron ragar PSG a wannan kakar, komawa baya domin kare gida na iya zama dabara mai haɗari sosai.

    Liv

    Asalin hoton, Getty Images

  3. , Daga jaridu

    Manchester United ba ta da shirin mayar da ɗan wasan gaban Ingila Marcus Rashford, mai shekara 28, cikin tawagar ƴan wasanta na farko a kakar wasa mai zuwa idan ya dawo daga zaman aro da ya ke yi a Barcelona. (Sun)

    A halin yanzu, Rashford ya kuduri aniyar ci gaba da taka leda a kulob ɗin na Sifaniya inda zai ci gaba da wasa a ƙarƙashin horaswar Hansi Flick, duk da rashin tabbas kan makomarsa na dogon zango a United. (TeamTalk)

    Real Madrid na tunanin dawo da tsohon kociyan ƙungiyar Jose Mourinho, amma ƙungiyarsa ta Benfica ta na son ya ci gaba da zama na aƙalla kaka ɗaya. (AS)

    Arsenal da Barcelona na zawarcin ɗan wasan tsakiya na Chelsea Enzo Fernandez, mai shekara 25, duk da cewa suna fuskantar hamayya daga Manchester City kan ɗan wasan na Argentina. (Teamtalk)

    Live

    Asalin hoton, Getty Images

  4. Matsalar rauni da koken magoya baya – me ke faruwa da Kylian Mbappé?

    Makomar Kylian Mbappé a Real Madrid zuwa yanzu na tangal-tangal, saboda abubuwa ba sa tafiya yadda aka yi tsammani tun a farko.

    Duk da cewa ɗan wasan mai shekara 27 ya ci ƙwallo 85 a wasa 100 tun bayan komawarsa filin Santiago Bernabéu, ƙungiyar na daf da ƙare kaka ta biyu a jere ba tare da lashe kofi ba.

    A tarihin ƙungiyar mai kofin La Liga 36 da na Champions League 15, wannan gagarumar koma baya ne ga Real Madrid.

    Tuni magoya bayan Real Madrid ke nuna fushinsu a fili, bayan jita-jitar rashin jituwa a ɗakin hutun ƴanwasa. BBC Sport ta duba yadda kakar wasa ta biyu mai ƙalubale ga Mbappé a birnin Sifaniya ta ci karo da cikas.

    Liv

    Asalin hoton, Getty Images

  5. Salon wasa zai iya taka rawar gani a karawar karshe

    Wasan ƙarshe zai zama maimaicin daf da karshe a kakar bara, wanda PSG ta yi nasara da jimillar ƙwallaye 3-1 a kan Arsenal.

    A wasan farko na kakar da ta gabata, Mikel Arteta ya nuna kai tsaye cewa ya yi kuskure wajen tsarin matsa lambar da ƙungiyarsa ta yi amfani da shi. A cikin mintuna 20 na farko, tsarin 4-4-2 na Arsenal ya gamu da matsala saboda yadda PSG ke sauya matsayi cikin sauri.

    Ousmane Dembele yana saukowa zuwa tsakiya, kuma tare da ƴan wasan tsakiya uku na PSG, hakan ya sa suka fi rinjayar Arsenal a tsakiyar fili. A wannan lokacin ne PSG ta ci ƙwallon farko a Emirates Stadium.

    Arteta zai shiga wasan ƙarshe yana sane da irin yadda Luis Enrique ke bai wa Dembele damar motsawa koiya a cikin fili, kuma mai yiwuwa ya koma amfani da gyaran gurbin tsaro kamar yadda ta yi a bara — wato tsarin 4-2-3-1 inda Martin Odegaard zai rika taka rawa, domin taimaka wa ƴan tsakiyarsa.

    Duk da cewa Arsenal ta fi karkata ga kai hare-hare cikin sauri a wannan kakar, ƙungiyar ta fi samun nasara idan tana riƙe ƙwallo tare da mamaye wasa a saman fili.

    Liv

    Asalin hoton, Getty Images

  6. Wannan karon Arsenal ta daban ce

    Babu shakka Arsenal tana da dama — musamman irin tsaron bayan da take da shi da kuma maitsaron raga.

    Wasan ƙarshe zai kasance mai matuƙar jan hankali. PSG za ta fi kai hare-hare fiye da yadda ta yi da Bayern Munich, amma wannan karon Arsenal ɗin ta bambanta da wadda aka sani a baya.

    Sun ci karo da ɗan koma baya a makonnin baya-bayan nan. Amma yanzu sun fara komawa kan ganiya. Suna da damar yin wani abu a karawar karshe. Abin da kawai suke buƙata shi ne su ci gaba da sa kwazo fiye da abinda suka yi a baya.

    Liv

    Asalin hoton, Getty Images

  7. Daga Jaridu

    Newcastle za ta sanya sayen sabon mai tsaron gida a matsayin ɗaya daga cikin abubuwan da za ta sa a gaba a bana, inda ta ke sanya ido kan golan Manchester City da Ingila James Trafford da kuma Bart Verbruggen na Brighton da Netherlands. (Telegraph)

    Arsenal na shirin sayar da manyan ƴan wasa a kasuwar musayar ƴan wasa ta bana duk da cewa ta samu sama da fam miliyan 120 a kuɗaɗen kyaututtukan Uefa sakamakon nasarar da ta yi na kai wa wasan ƙarshe na gasar zakarun Turai. (Sky Sports)

    Brentford na ƙoƙarin ɗauko ɗan wasan bayan Austria Jannik Schuster, mai shekara 19 daga Red Bull Salzburg a kan kuɗi fam miliyan 17. (Athletic)

    Tottenham na zawarcin ɗan wasan Brighton Jan Paul van Hecke, mai shekara 25, duk da cewa Chelsea da Liverpool su ma suna harin ɗan wasan na Netherlands. (TeamTalk)

    Liv

    Asalin hoton, Getty Images

  8. Me muka sani kan wasan Arsenal da PSG?, Champions League

    Arsenal ta kara da Paris St-Germain sau uku a Gasar Zakarun Turai ta kakar wasan da ta gabata.

    Ta samu gagarumar nasara da ci 2-0 a filin Emirates Stadium a matakin rukuni, inda Kai Havertz da Bukayo Saka suka ci mata ƙwallaye tun kan hutu.

    Sai dai PSG ta ci gaba da inganta wasanninta a hankali a kakar, kuma bayan da ta tsallaka matakin gaba, daga nan ƙungiya ta kara ƙarfi sosai har ta kai ga doke Inter Milan da ci 5-0 a wasan ƙarshe — kafin nan ta fitar da Liverpool da Aston Villa, sai kuma ta yi waje da Gunners a daf da karshe.

    Ƙungiyar Luis Enrique ta doke Arsenal da jimillar ƙwallaye 3-1, inda ta yi nasara a wasan farko a Ingila, bayan Ousmane Dembele ya ci ƙwallo daga nan ta yi nasara 2-1 a wasa na biyu a Faransa.

    Gianluigi Donnarumma, wanda yanzu yake Manchester City, ya taka rawar gani da ta kai PSG ta lashe kofin.

    Wannan shi ne karo na biyu da Arsenal ta kai wasan karshe a Champions League kofin da ba ta taɓa ɗauka ba.

    lIV

    Asalin hoton, Getty Images

  9. Live

    Asalin hoton, Getty Images

    Liv

    Asalin hoton, Getty Images

    Liv

    Asalin hoton, Getty Images

  10. Paris St-Germain za ta kara da Arsenal, bayan fitar da Bayern, Champions League

    Paris St-Germain ta kai wasan ƙarshe a Gasar Zakarun Turai da za ta kara da Arsenal, bayan da ta doke Bayern Munich, mai fatan kara lashe kofin karo na biyu a jere.

    Wasan daf da ƙarshe na biyu da aka buga a Jamus bai kai armashin na farko da aka buga a Paris ba, wanda ya bai wa masu riƙe da kofin karkashin Luis Enrique nasarar cin 5-4 kafin su je filin Allianz Arena a Munich ranar Laraba.

    Harry Kane ya ci ƙwallonsa na 55 a kakar wasa ta bana, amma a karin lokaci. Yana da 14 a bana yayin da Kylian Mbappe ke kan gaba a yawan ƙwallaye a gasar mai 15 a raga.

    PSG, mai rike da kofin bara na fatan lashe shi karo na biyu a jere, idan ta zo wasa da Arsenal ranar 30 ga watan Mayu a Budapest.

    Live

    Asalin hoton, Getty Images

  11. Murnar kai wa wasan karshe ga PSG

    Live

    Asalin hoton, Getty Images

    Live

    Asalin hoton, Getty Images

    Live

    Asalin hoton, Getty Images

  12. , Bayern Munich 1–1 Paris Saint-Germain

    Paris Saint-Germain ta zama ƙungiya ta farko da ta kai wasan ƙarshe (a UEFA Champions League sau biyu a jere tun Liverpool a 2019.

    Haka kuma, su ne masu rike da kofin da suka fara kaiwa final tun bayan Real Madrid a 2018.

  13. Mbappe ne zai lashe takalmin zinare, Bayern Munich 1-1 Paris St-Germain

    Kylian Mbappe ne zai karbi takalmin zinare a bana a Champions League mai 15 a raga, Harry Kane mai 14 an cire su daga karawar.

    Wanda ya rage sai dan wasan Paris Saint-Germain, Khvicha Kvaratskhelia, wanda ya ci ƙwallaye 10.

  14. An tashi wasan Bayern 1-1 PSG, Bayern Munich 1-1 Paris St-Germain

    Paris St Geramin ta kai wasan karshe a Champions League, bayan nasara 6-5 gida da waje a kan Bayern Munich.

    Kenan PSG za ta kara da Arsenal a wasan karshe a Champions League.

  15. , Bayern Munich 1-1 Paris St-Germain

    An bai wa dan wasan Bayern, Joshua Kimmich katin gargadi duk da an tashi wasan.

  16. , Bayern Munich 1–1 Paris Saint-Germain

    Yanzu Bayern tana da damar ƙarshe — ko ma a ce dama ta ƙarshe gaba ɗaya. Dole ne su ƙirƙiri wata dama nan take, ba tare da jinkiri ba.

    Lokaci ya ƙare, wannan ne ko yanzu ko babu lokaci.

  17. GOAL Bayern Munich 1-1 Paris St German, Harry Kane

    Wani abu mai ban mamaki Harry Kane a cikin akwatin bugun fanareti, ya juya, sannan ya buga kwallon da karfi a kusurwar saman raga.

    Yanzu tambayar ita ce: shin akwai isasshen lokaci kuwa?

    Liv

    Asalin hoton, Getty Images

  18. , Bayern Munich 0–1 Paris Saint-Germain

    Bayern Munich na da mintuna huɗu kawai da ake sa ran za ta ci biu nan gaba ko sa komo karawar.

    Har ila yau, ba a sa ran za a samu tsawon ƙarin lokaci mai yawa sosai ba.

    Liv

    Asalin hoton, Getty Images

  19. , Bayern Munich 0-1 Paris St-Germain

    An bai wa dan wasan PSG, mai tsaron baya Marquinhos katin gargadi.