Fernandes ne gwarzon marubuta labarin tamaula na 2026

Wannan shafi ne da zai ke kawo muku labaran wasannin BBC Hausa daga 4 zuwa 8 ga watan Mayun 2026.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. , Arsenal 0-0 Atletico Madrid

    Yayin da wasan ke ci gaba, za a ƙara samun saka kaimi da rashin natsuwa.

    Viktor Gyökeres ya yi ƙoƙarin gudu da ƙwallo, amma ya ci karo da abokin wasansa Bukayo Saka, daga ƙarshe kuma ya yi laifi a kan Koke yayin da shi Koke ya ƙwace masa ƙwallon.

    Live

    Asalin hoton, Getty Images

  2. , Arsenal 0-0 Atletico Madrid

    Babbar dama ga Arsenal. Ƙwallo mai ƙyau daga Ben White a gefen dama, an dawo da ita zuwa Bukayo Saka wanda ya buga amma ta yi faɗi.

    Gabriel ya yi yunƙurin buga ƙwallon daga nesa, amma ya ja ta kadan ta wuce gefen sandan raga.

  3. , Arsenal 0-0 Atletico Madrid

    Arsenal ta samu bugun kusurwa, kuma Bukayo Saka yana shi kaɗai sosai a gefen sandan raga na biyu, amma bai san abin da zai yi da ƙwallon ba, sai kawai ya tura ta zuwa gefen ragar ta yi waje.

  4. , Arsenal 0-0 Atletico Madrid

    Bukayo Saka ya rasa ƙwallo, sannan Ben White ya yi laifi a kan Koke, yayin da yake ƙoƙarin gyara kuskuren da ya yi.

  5. , Arsenal 0-0 Atletico Madrid

    Antoine Griezmann ya dawo da ƙwallo daga kusa da layi daf da za ta fita, sai David Raya ya kare ta, amma Giuliano Simeone yana wajen. Buga ƙwallon da ya yi kuma Declan Rice ya tare.

  6. , Arsenal 0-0 Atletico Madrid

    Riccardo Calafiori ya yi yunƙurin buga tamaula daga nesa fiye da yadi 40, amma ya wuce sama sosai kuma ya fita nesa da raga.

  7. , Arsenal 0-0 Atletico Madrid

    Antoine Griezmann ya saki kwallo zuwa Giuliano Simeone a gefen dama, shi kuma ya daga kwallo zuwa cikin akwatin bugun daga kai sai mai tsaron gida ga Julian Alvarez, amma ɗan wasan Argentina ya kasa kai bugun da ya yi manufa na taɓa ƙwallon.

    Live

    Asalin hoton, Getty Images

  8. , Arsenal 0-0 Atletico Madrid

    Har yanzu wasan bai ɗauki zafi ba, babu wani babban hari da aka kai

    An busa usur Antoine Griezmann ya yi wa Eberechi Eze keta.

    Live

    Asalin hoton, Getty Images

  9. , Arsenal 0-0 Atletico Madrid

    An samu kyakkyawan yanayi mai cike da annashuwa a cikin filin Emirates, yayin da Arsenal ta fara da rike ƙwallo a farkon wasan.

  10. An take wasa Arsenal 0-0 Atletico Madrid

  11. Ƴan Arsenal 11 da za su kara da Atletico

    Live

    Asalin hoton, Getty Images

  12. Ƴan wasan Atletico da za su fuskanci Arsenal

    Live

    Asalin hoton, BBC Sport

  13. Live

    Asalin hoton, Getty Images

  14. Idan Arsenal ba ta yi rashin nasara ba a wasan farko a karawar waje a zagayen farko, tana yawan tsallakewa zagayen gaba—ta yi haka sau takwas cikin 10, ciki har da biyar a jere a baya-bayan nan. Sai dai ba ta kai bante ba a lokuta biyu: da Benfica (1991-92) da Chelsea (2003-04).

    Arsenal na neman kaiwa wasan ƙarshe na Champions League karo na farko tun 2006. Idan ta yi haka, zai zama mafi tsawon lokaci tsakanin shiga final ga kowace ƙungiya tun Atlético Madrid a 2014 (shekaru 40), kuma mafi tsawo ga ƙungiyar Ingila tun Liverpool a 2005 (shekaru 20).

    Atlético Madrid na iya kaiwa wasan ƙarshe karo na uku a ƙarƙashin Diego Simeone (2014 da 2016). Koci biyu kacal suka taɓa kaiwa final fiye da haka da ƙungiya ɗaya: Alex Ferguson (Manchester United) da Marcello Lippi (Juventus) – sau huɗu kowanne.

    Arsenal ta sha kashi karo biyu a wasa 23 a Champions League (nasara 17, canjaras huɗu), kuma duka biyun a hannun Paris Saint-Germain (semi-final na kakar da ta gabata). Har yanzu ba ta sha kashi ba a wannan kakar (wasanni 13: nasara 10 da canjaras uku), kuma za ta iya kaiwa wasa 14 ba tare da shan kashi ba a karon farko.

    A ƙarƙashin Mikel Arteta, Arsenal na cin ƙwallaye 0.65 a kowanne wasa a Champions League (24 a wasa 37) — mafi ƙarancin matsakaici ga koci da ya jagoranci wasa 20 ko fiyeda haka, fiye da Frank Rijkaard (0.68).

    Live

    Asalin hoton, Getty Images

  15. Kyaftin din Arsenal, Martin Odegaard, da dan wasan gaba Kai Havertz ba su halarci atisayen ba kafin wasan kusa da karshe a Champions League da za su fafata da Atletico Madrid a ranar Talata a filin wasa na Emirates, amma kociya, Mikel Arteta ya ce duka ƴan wasan suna nan a shirye, inda sakamakon wasan farko suka tashi 1-1.

    Dukkan ƙwallayen da aka ci a wasan farko a Madrid a makon jiya daga bugun fenariti ne, inda ɗan wasan gaba Viktor Gyokeres ya ci wa Arsenal, yayin da Julian Alvarez ya zura wa Atletico kwallo.

    Live

    Asalin hoton, Getty Images

  16. Julián Álvarez na Atlético Madrid yana bayar da ƙwallo ana ci a matsakaici duk bayan minti 80 a Champions League (Guda 34 a minti 2,710 — Ya ci ƙwallo 25 ya bayar da tara aka zura a raga). Daga ƴan gaba masu hannu a cin ƙwallaye 20 ko fiye da haka, Erling Haaland ne kaɗai ya fi shi (minti 74).

    Álvarez ya ci ƙwallo 14 a wasa 14 a wannan kakar (Ya ci 10 ya bayar da huɗu akazura a raga), sannan shi ne na farko a matsa lamba da yawa — mafi girma daga cikin ƴan wasa a gasar.

    Declan Rice na Arsenal ya fi kowa yawan raba ƙwallo mai guda (83), Shi ne ɗaya daga cikin ƴan tsakiya mafi tasiri a matakin knock-out.

    Live

    Asalin hoton, Getty Images

  17. Arsenal ba ta taɓa shan kashi a hannun Atlético Madrid ba a gasar UEFA Champions League, inda ta ci su 4-0 a Emirates kuma suka tashi 1-1 a filin Riyadh Air Metropolitano a wannan kakar. Koci biyu kacal ne suka fara wasa uku ba tare da shan kashi a hannun Diego Simeone ba: Carlo Ancelotti da Maurizio Sarri (duk sun yi haka sau uku).

    Atlético Madrid ba ta samu nasara ba a wasanni biyu da ta buga da Arsenal a wannan kakar (canjaras ɗaya da rashin nasara daya). A karo na ƙarshe da ta buga wasa uku ko fiye da ƙungiya ɗaya ba tare da nasara ba a kakar guda shi ne a 2022-23 da Real Madrid (canjaras daya da rashin nasara biyu).

    Arsenal ba ta sha kashi ba a wasa takwas a bayan nan da ta yi da ƙungiyoyin Spain a Champions League (nasara bakwai da canjaras daya). Ƙungiya guda ɗaya ce kawai ta fi wannan tarihin: Chelsea (wasanni 16 ba tare da shan kashi ba tsakanin 2006 da 2014).

    Atlético Madrid ta yi rashin nasara a wasa shida cikin bakwai a baya da ta yi a waje da ƙungiyoyin Ingila a Champions League (nasara ɗaya), ciki har da huɗu a jere a baya-bayan nan. Rashin nasarar 0-4 da ta yi a Emirates a Oktoba 2025 na daga cikin mafi muni da ta taɓa yi a gasar.

    Live

    Asalin hoton, Getty Images

  18. Arsenal, wacce ke kan gaba a teburin Premier League duk da saura wasa uku suka rage a kammala kakar nan, an fitar da ita daga Champions League a matakin kusa da na karshe a kakar da ta gabata ta hannun zakarun gasar na wancan lokaci, Paris Saint-Germain.

    “Ina matukar fatan yin nasara a wasan nan. Ina jin karfin gwiwa a cikin kungiyar da kuma kewayentaa,” in ji Arteta.

    A gefe guda kuma, kocin Atletico Diego Simeone ya ce ƙungiyarsa ta canza otal kafin wasan zagaye na biyu London bayan sun zauna a wani daban lokacin da Arsenal ta doke su da ci 4-0 a matakin rukuni, yana mai barkwanci cewa sun yi hakan ne saboda farashi, duk da rahotannin kafafen yada labarai na Spain da ke cewa wata al’ada ce ta camfi.

    Arteta

    Asalin hoton, Getty Images

  19. Filin Emirates ya fara ɗauakr ƴan kallo

    Live

    Asalin hoton, Getty Images

  20. Ƴan wasan Arsenal da na Atletico Madrid da za su fafata, Arsenal v Atletico Madrid

    Mikel Arteta bai yi sauyi ba daga ƴan wasan da ya doke Fulham 3-0 a Premier League ranar Asabar da zai fuskanci Atletico ranar Talata a Emirates

    Kawi dai zai yi amfani da Myles Lewis-Skelly daga tsakiya, yayin da Martin Zubimendi ke benci.

    Ƴan wasan Arsenal 11: Raya, White, Saliba, Gabriel, Calafiori, Rice, Lewis-Skelly, Eze, Trossard, Saka, Gyokeres

    Ƴan zaman benci: Arrizabalaga, Setford, Mosquera, Hincapie, Odegaard, Jesus, Martinelli, Norgaard, Madueke, Havertz, Zubimendi, Dowman

    Diego Simeone ya yi canji da dama kuma tun farko ya hu8tar da wasu ƴan wasan a gasar La Liga, zai kuma fara da Julian Alvarez, ya kamata Arsenal su kala da shi sosai.

    Ƴan wasan Atletico Madrid 11: Oblak, Pubil, Le Normand, Hancko, Ruggeri, Simeone, Llorente, Koke, Lookman, Alvarez, Griezmann

    Ƴan zaman benci: Musso, Gimenez, Mendoza, Cardoso, Sorloth, Alex BAena, Almada, Lenglet, Molina, Vargas, Bonar, Julio Diaz