Za a buga wasan karshe a Champions League a Budapest

Asalin hoton, Getty Images
Wannan shafi ne da zai ke kawo muku labaran wasannin BBC Hausa daga 4 zuwa 8 ga watan Mayun 2026.
Mohammed Abdu

Asalin hoton, Getty Images
David Raya na Arsenal ya hana ƙwallaye su shiga ragarsa fiye da kowane mai tsaron raga tun kakar da ta gabata, sannan ya buga wasa 14 ba tare da wallo ya shiga ragarsa ba.
Antoine Griezmann na Atlético Madrid na iya buga wasa na 128 kuma na ƙarshe a manyan gasannin zakarun Turai.
Yana na huɗu cikin ƴan Faransa mafi yawan buga wasanni, bayan Karim Benzema da Thierry Henry da Claude Makélélé. Haka kuma yana cikin ƴan Faransa huɗu da suka ci ƙwallaye 50 ko fiye da haka a gasar zakarun Turai.
Viktor Gyökeres na Arsenal na iya zama ɗan wasa na uku da ya ci ƙwallo a dukkan wasa biyu na daf da karshe ga ƙungiyar Premier League, bayan Sadio Mané (Liverpool) da Riyad Mahrez (Manchester City).

Asalin hoton, Getty Images
Dangane da raunin ƴan wasa, Alvarez — wanda ya ci kwallo 20 ya bayar da tara aka zura a raga a wasa 48 a dukkan fafatawa a wannan kakar — yana cikin waɗanda suka je Ingila, bayan da aka sauya shi a karshen wasan farko kuma an yi fargabar ba zai buga wasana biyu ba a Emirates
Ɗan wasan dan asalin Argentina mai shekaru 26, wanda ya taɓa lashe Kofin Duniya, ya taba taka leda a Manchester City.
“Julian a irin wannan wasa yana da muhimmanci,” in ji Simeone. “Ya san gasar sosai. Wasan makon da ya gabata ya yi kokari sosai. Ina fatan zai bada gudummawa kamar yadda wasan ke bukata.”

Asalin hoton, Getty Images
Arsenal tana karɓar bakuncin Atletico Madrid a wasan zagaye na biyu a Champions League da za su kara a Emirates.
A wasan farko a makon jina sun tashi 1-1 a Sifaniya, inda za a fayyace wadda za ta je zagayen karshe a kakar bana.
Arsenal da Atletico Madrid ba su taɓa lashe kofin zakarun Turai ba, bayan da Gunners da ta zagayen karshe sau ɗaya ta Spain ta je sau uku.
Duk wadda ta yi nasara za ta fuskanci ko dai Bayern Munich ko kuma Paris St Germain.
Za mu kawo muku wasan da Arsenal za ta karɓi bakuncin Atletico Madrid ranar Talata a Champions League, duk wadda ta yi nasara za ta kai karawar karshe.
Da faran za ku tara a shirin tare da ni Mohammed Abdu, Mammman Skipper Tudun Wada Kano, Najeriya.
Tun farko Manchester City ta sa ran samun maki uku, amma ta raba da Everton a wasan da ya kayatar a Premier League a ranar Litinin.
Wataƙila maki ɗaya bai isa ba, amma wannan ƙyaƙƙyawar ƙwallo ce daga Jeremy Doku da kuma jajircewa mai ban mamaki daga Manchester City don dawowa cikin wasa.
Jeremy Doku ya lanƙwasa ƙwallo daga gefen akwatin bugun fenariti zuwa saman kusurwar raga, kuma City ta raba maki da Everton.

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, Getty Images
Kasa da mintuna biyar tare da ƙarin lokacin suka rage wa Manchester City don ta samu wani abu daga wannan wasa ko raba maki ne daga neman uku tun kan fara wasan.
Abin mamaki, bayan ƙwallon Thierno Barry da ya Everton a gaba da cin 3-1, wasu magoya baya sun fara barin filin wasa. Amma sun sake dawowa da sauri bayan Erling Haaland ya zare ɗaya.
Wannan wasa ya kara rikicewa, amma idan akwai wanda Manchester City za ta dogara da shi, to shi ne Erling Haaland.
Ɗan Norway ɗin ya karya layin masu tsaron bayan Everton, ya ruga da ƙarfi, sannan ya ɗaga ƙwallon sama ta wuce Jordan Pickford.
Manchester City ta ruɗe gabaki daya ta yadda aka ci ƙwallo na uku.
Kuma kuskure aka yi daga Manchester City, inda Thierno Barry ya yi amfani da damar.

Asalin hoton, Getty Images
Phil Foden da Mateo Kovacic sun shiga fili sun kuma canji Antoine Semenyo da Nico Gonzalez.
Wani sauyi mai ban mamaki ga Everton!
Ta samu bugun kusurwa, kuma ƙwallon da aka kawo ta yi ƙyau, inda Jake O'Brien ya yi amfani da kai ya zura ta cikin raga.
A cikin mintuna kaɗan, gasar neman kofin ta juya gaba ɗaya.

Asalin hoton, Getty Images
Tun farko an soke ƙwallon da cewar da satar gida, yayin da Guehi ya mayar da ƙwallo ga mai tsaron gida, amma ba ta je gurin Dunnarumma ba, nan da nan Barry ya jefa a raga.

Asalin hoton, Getty Images
Beto an maye gurbinsa da Thierno Barry.
Everton na korafin fenariti a cikin da'ira ta 18, amma alkalin wasa ya ce ba komai.