Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Fernandes ne gwarzon marubuta labarin tamaula na 2026

Wannan shafi ne da zai ke kawo muku labaran wasannin BBC Hausa daga 4 zuwa 8 ga watan Mayun 2026.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. , Arsenal 1-0 Atlético Madrid

    Atlético ta samu bugun kai tsaye, amma kwallon da Antoine Griezmann ya kawo an fitar da ita kai tsaye daga ɗan wasan Arsenal.

    Julian Alvarez ya yi ƙoƙarin ɗaga ƙwallo sama, amma ta yi kusa sosai da David Raya, wanda ya kama ta cikin sauƙi.

  2. , Arsenal 1-0 Atletico Madrid

    Na manta na sanar da ku Arsenal ta yi canji

    Riccardo Calafiori da Eberechi Eze da kuma Bukayo Saka, an maye gurbinsu da Noni Madueke da Martin Odegaard da kuma Piero Hincapie - to anya canjin nan ya yi kyau kuwa.

    Suma baki sun yi canji inda, Ademola Lookman da Giuliano Simeone da kuma Robin Le Normand, inda Johnny Cardoso da Alexander Sorloth da kuma Nahuel Molina suka shiga fili.

  3. , Arsenal 1-0 Atletico Madrid

    Akwai wasu hukunci guda biyu da ka iya jawo cece-kuce a nan.

    Ƙalubalen Gabriel a kan Antoine Griezmann da kuma na Riccardo Calafiori, shima a kan Griezmann.

  4. , Arsenal 1-0 Atletico Madrid

    Gudu mai kyau daga Declan Rice nan da nan ya bai wa Viktor Gyokeres kwallo daga bangaren hagu, amma kuma Marcos Llorente ya hana shi yin wani abu.

    .

  5. , Arsenal 1-0 Atletico Madrid

    Wannan shi ne lokaci mai kyau daga Atletico Madrid. Sun fito gabaki ɗaya ko za su farke ƙwallon sun fara fahimtar lokaci ya fara ja.

  6. , Arsenal 1-0 Atletico Madrid

    An yi saurin duba VAR ko akwai bugun fenariti, amma an yanke hukunci cewa ƙalubalen Gabriel ya halatta ba wani laifi domin ya fara samun ƙwallon.

  7. , Arsenal 1-0 Atletico Madrid

    Wane martani daga Gabriel! Giuliano Simeone ya yi gudu mai kyau sosai har ya wuce David Raya wanda ya rikice dan kadan, amma dan wasan Brazil ɗin ya yi wani muhimmin kokarin hana kwallon shiga raga..

    Sun kusa ƙwarai da samun kwallon a raga.

  8. , Arsenal 1-0 Atletico Madrid

    Declan Rice ya yi saurin lura da wani mummunar pas daga Atletico Madrid, sannan Marcos Llorente ya yi laifi a kan Leandro Trossard, domin hana masu masaukin baƙi samun wata dama.

  9. , Arsenal 1-0 Atletico Madrid

    Ƙwallo mai haɗari cikin da'ira ta 18 ta Arsenal, sai dai Ademola Lookman ya kasa amfana da wannan damar.

  10. An koma zagaye na biyu, Arsenal 1-0 Atletico Madrid

    An koma zagaye na biyu. Saura minti 45 ko Arsenal za ta kai wasan karshe a Champions League a bana a karon farko tun bayan 2006?

  11. An je hutu, Arsenal 1-0 Atletico Madrid

  12. , Arsenal 1-0 Atletico Madrid

    Atlético za ta yi nadamar yadda ta zubar da damar cin kwallo a wannan lokacin da daf aje hutu, kuma a irin wannan lokacin.

    An yi tambaya kan ko akwai sata gida a kwallon da Saka ya ci?, amma Bukayo Saka yana ya ci ƙwallo mai ƙyau ba wata matsala..

  13. GOAL Arsenal 1-0 Atletico Madrid, Bukayo Saka

    Arsenal ta fara jin kanshin wasan karshe a Champions League.

    Viktor Gyökeres ya riƙe ƙwallo a gefen dama sannan ya ɗaga ta zuwa Leandro Trossard, wanda ya ɗan yi jinkiri da ƙwallon kuma da alama damar ta kusa kuɓucewa.

    Sai ya buga zuwa ƙasan kusurwa, Jan Oblak ya tare ta amma Bukayo Saka ya kasance yana wajen, nan da nan ya zura ta a raga.

    Wannan babbar dama ce mai muhimmiaci a irin wannan lokaci!

  14. , Arsenal 0-0 Atletico Madrid

    Wasan Arsenal ya kasance mai kyau sosai a kusa da akwatin bugun daga kai sai mai tsaron raga, amma Matteo Ruggeri ya yi saurin kai ƙafar sa ya taɓa ƙwallon, ya hana harin ya ci gaba, ko ya zama haɗari.

  15. , Arsenal 0-0 Atletico Madrid

    Ba a ba da bugun fenariti ba. Ina ganin VAR ma ba ta yi nazarin abinda ya faru ba sosai. Wannan na iya zama abin gardama.

    Arsenal ta samu bugun kusurwa, kuma sun sake dauka a takaice, amma bai haifar da komai ba, sannan ba wani haɗari.

  16. , Arsenal 0-0 Atletico Madrid

    Magoya bayan Arsenal suna ta ihu suna neman a ba su bugun fenariti, yayin da Antoine Griezmann ya yi kama da ya turea Leandro Trossard a cikin akwatin fenariti.

    VAR za ta duba wannan lamari.

  17. , Arsenal 0-0 Atletico Madrid

    Ohh, wannan dama ce mai kyau ga Atlético, amma daga ƙarshe an ɗaga tutar satar gida.

    An yi wasa mai kyau a gefen dama, inda Antoine Griezmann ya sami Giuliano Simeone a damansa, shi kuma ya mayar da ƙwallo ga Marcos Llorente, amma an ɗaga masa tuta da cewa yana satar gida.

  18. , Arsenal 0-0 Atletico Madrid

    An dauki bugun kusurwa a takaice, daga bisani kuma ƙwallon ta kai ga Myles Lewis-Skelly, wanda ya riƙe ƙwallon da kyau sannan ya aika ta ciki da gaggawa a gaban raga, amma babu kowa da zai tura ta cikin raga.

  19. , Arsenal 0-0 Atletico Madrid

    Arsenal ba ta ci ƙwallo daga bugun kusurwa ko ɗaya ba a cikin kusurwoyi 42 da ta yi a gasar Champions League, tun bayan da ta ci daga ɗaya a wasan da ta yi da Inter a watan Janairu.

    Ta sake samun wani bugun kusurwa a nan yayin da Declan Rice ya yi ƙoƙarin mayar da ƙwallo cikin gidan Atletico, amma an tare ta ta fita waje.