Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Fernandes ne gwarzon marubuta labarin tamaula na 2026

Wannan shafi ne da zai ke kawo muku labaran wasannin BBC Hausa daga 4 zuwa 8 ga watan Mayun 2026.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. , Everton 0-1 Manchester City

    Erling Haaland ya ruga da ƙarfi ta tsakiyar fili, amma ya zame yayin da zai bayar da ƙwallo zuwa Jeremy Doku.

    Harin bai yi zafi ba, kuma Everton ta samu damar komawa cikin tsarin tsaron bayansu.

  2. , Everton 0-1 Manchester City

    Akwai kyakƙyawan fata ga Everton, saboda Manchester City ta ɗan rage kai hari da aka dwo zagaye na biyu a wasan na Premier League.

    A wannan kakar, an zura mata ƙwallaye 29, kuma 20 daga cikinsu a zagaye na biyu a gasar ta Ingila.

  3. , Everton 0-1 Manchester City

    Da alama Antoine Semenyo ya bugu sosai a kai daga ketar da Vitalii Mykolenko ya yi masa, amma hatsari ne kawai ba wani komai.

    An duba shi, kuma ya koma fili yana cikin koshin lafiya kuma zai ci gaba da fafatawar.

  4. , Everton 0-1 Manchester City

    Antoine Semenyo ya fadi a cikin gidan Everton a da'ira ta 18 yana riƙe da kansa, don haka alkalkin wasan, Michael Oliver ba shi da zaɓi sai ya dakatar da wasan… abin da ya harzuka magoya bayan masu masaukin baƙi sosai.

  5. Katin gargaɗi, Everton 0-1 Manchester City

    An bai wa Beto katin gargaɗi, sakamakon ketar da ya yi wa Marc Guehi.

  6. An koma zagaye na biyu, Everton 0-1 Manchester City

    Za a koma zagaye na biyu a filin wasa na Hill Dickinson.

  7. , Everton 0-1 Manchester City

  8. , Everton 0-1 Manchester City

    Jeremy Doku ya na da hannu a cin ƙwallo biyar daga wasa biyar bayan nan ya ci uku ya bayar da biyu aka zura a raga.

    Dan Belgium ɗin ya kuma ci gaba da taka rawa wajen cin ƙwallaye a wasa uku a waje a bayan nan a Premier League - Ya ci ƙwallo biyu ya bara da ɗaya a raga.

  9. An je hutu, Everton 0-1 Manchester City

    Manchester City ta ci ƙwallo ta hannun Jeremy Doku, kenan tana da maki uku a minti na 45, saura zagaye na biyu.

  10. GOAL Everton 0-1 Manchester City, Jeremy Doku

    Everton suna sa Manchester City cikin wahala sosai zuwa yanzu, amma tana jajircewa, yayin da suka ci gaba da riƙe ƙwallon a gefen akwatin bugun fenarrti, kuma dama mai kyau ga Jeremy Doku.

    Magoya bayan City suna ta kiran “bug ka buga!” kuma ɗan Belgium ɗin ya yi hakan ya buga ƙwallon da karfi, wadda ta shiga saman kusurwar raga.

  11. Manchester City ta yaga layukan tsaro, amma Rayan Cherki bai samu wanda zai ba ƙwallo ba bayan kyakkyawan hari da ya kai shi cikin akwatin bugun fenariti.

    Harin ba karfi, kuma City ta koma baya da wasa.

  12. , Everton 0-0 Manchester City

    An ture juna tsakanin James Tarkowski da Abdukodir Khusanov, amma babu wani tashin hankali a tsakaninsu.

  13. , Everton 0-0 Manchester City

    Manchester City ta samu bugun kusurwa, kuma ƙwallon da Bernardo Silva ya kawo ta yi kyau, amma Jordan Pickford ya buge ta ya kawar a cikin akwatin bugun fenariti cikin taron ƴan wasa.

  14. Kaɗan ya rage Everton ta ci Man City, Everton 0-0 Manchester City

    Wata babbar dama ga Everton!

    Everton ta wuce masu tsaron bayan Manchester City, kuma Merlin Röhl ya zura ƙwallo ƙasa zuwa kusurwa daga kasa, amma mai tsaron ragar City, Gianluigi Donnarumma ya kai hannu mai muhimmanci ya tare ta. Beto ya iso don karɓar ƙwallon da ta dawo, amma Abdukodir Khusanov ya tare ta a gaban layin raga.

  15. , Everton 0-0 Manchester City

    Wani ƙarfi da gudu daga Bernardo Silva ta tsakiyar fili, kuma ɗan ƙasar Portugal ya samu Nico O'Reilly, amma an katse ƙwallon kafin ta isa ga mai haɗari Jeremy Doku.

  16. , Everton 0-0 Manchester City

  17. , Everton 0-0 Manchester City

    Jeremy Doku ya ɗaga ƙwallon cikin salo mai laushi zuwa ga Antoine Semenyo, amma ɗan Ghana bai samu yadda yake so ba, domin ya buga ƙwallon ta bi ta saman raga.

  18. , Everton 0-0 Manchester City

    Manchester City ta fara samun damarmaki, amma ya kamata ta amfana tun da wuri.

    Yanzu ne wasan ya fara ɗaukar zafi, kuma City tana bukatar maki uku a daren Litinin.

  19. Sai ayi mana gafara mun ɗan samu matala, amma zamu ɗora, Everton 0-0 Manchester City

  20. , Everton 0-0 Manchester City

    Fitaccen mawaki kuma babban masoyin Manchester City, Noel Gallagher, yana cikin bangaren magoya bayan a daren yau — kamar yadda aka saba ganinsa a wasannin City.