Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Fernandes ne gwarzon marubuta labarin tamaula na 2026

Wannan shafi ne da zai ke kawo muku labaran wasannin BBC Hausa daga 4 zuwa 8 ga watan Mayun 2026.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. , Bayern Munich 0-1 Paris St-Germain

    Abin tausayi ga Willian Pacho. Bayan ɗan lokaci kaɗan da Harry Kane ya gogar masa saman kansa da takalminsa, sai kuma Konrad Laimer ya buge shi a fuska da gwiwar hannu.

  2. , Bayern Munich 0-1 Paris St-Germain

    An tsayar da wasan sakamakon raunin kai da dan wasan da PSG, Willian Pacho ya ji.

  3. , Bayern Munich 0-1 Paris St-Germain

    Bayern ta kai hari da wuri wajen kokarinfarke kwallon, amma babu wani abun da ya faru.

  4. An koma zagaye na biyu, Bayern Munich 0-1 Paris St-Germain

  5. An je hutu, Bayern Munich 0-1 Paris St-Germain

  6. , Bayern Munich 0-1 Paris St-Germain

    Magoya bayan Bayern Munic ba su ji dadi ba da karin minti biyu da aka daga allo.

  7. An shiga karin lokaci, Bayern Munich 0-1 Paris St-Germain

    an yi karin minti biyu

  8. , Bayern Munich 0–1 Paris Saint-Germain

    Jamal Musiala ya isa layin ƙarshe ya zura ƙwallo da ƙarfi a cikin yankin gola, amma mai tsaron ragar Paris Saint-Germain Matvey Safonov ya kai hannu ya dan taɓa ƙwallon.

    Har yanzu, Safonov bai fuskanci wata babbar barazana kai tsaye ba da ta buƙaci tare kwallo a wannan wasan.

  9. , Bayern Munich 0–1 Paris Saint-Germain

    Marquinhos yana da shekara 31, amma yana jin kamar ya daɗe sosai a fagen ƙwallon ƙafa.

  10. , Bayern Munich 0-1 Paris St-Germain

    Ba Jonathan Tah aka bai wa katin gargadiba, Josip Stanisic ne na Bayern Munich.

  11. , Bayern Munich 0–1 Paris Saint-Germain

    PSG ta samu bugun kusurwa.

  12. , Bayern Munich 0–1 Paris Saint-Germain

    Wannan ne dalilin da ya sa ba a bayar da fenariti ba:

    Dokokin ƙwallon ƙafa suna cewa ba a ɗaukar sa hannun, idan ƙwallo ta buga hannun ɗan wasa bayan an buga ta ne daga abokin wasansa — sai dai idan ƙwallon ta shiga raga kai tsaye ko kuma ɗan wasan ya ci ƙwallon nan take.

    Saboda haka, a wannan yanayin, da ƙwallon ta fito daga Vitinha ta buga hannun João Neves, ba a ɗauke a matsayin laifin fenariti.

  13. Korafin fenariti, Bayern Munich 0–1 Paris Saint-Germain

    Wani ƙorafi kan kwallo ya bugi hannu, ya sake tasowa! Vitinha ya buga ƙwallo da ƙarfi, amma ta bugi hannun abokin wasansa João Neves.

    Tambayar ita ce: shin wannan zai iya zama bugun fenariti ga Bayern Munich?

  14. , Bayern Munich 0–1 Paris Saint-Germain

    Vincent Kompany, wanda yake kusa da abin da ke faruwa a fili fiye da masu kallo, yana cikin tsananin fushi. Haka ma ‘yan wasan Bayern suna nuna bacin rai sosai.

    Ba a fahimci dalilin da ya sa alkalin wasa ya ba Bayern bugun tazara ba maimakon PSG, saboda alamar da ta nuna ta yi kama da bugun da ya kamata a yi wa PSG.

  15. , Bayern Munich 0-1 Paris St-Germain

    Wani muhimmin lokaci mai iya canza sakamakon wasa: ƙwallon ya bugi hannun Nuno Mendes a gefen fili kuma ‘yan wasan Bayern suna ta ƙorafi suna neman a nuna masa katin gargadi na biyu.

    Amma abin mamaki, alkalin wasa ya yanke hukunci ya ba Bayern Munich bugun tazara.

  16. , Bayern Munich 0-1 Paris St-Germain

    Kowa ya san Luis Díaz ɗan wasa ne mai kyau a lokacin da yake Liverpool, amma a wannan kakar ya ƙara yin fice sosai a Bayern Munich.

  17. , Bayern Munich 0-1 Paris St-Germain

    A dan lokacin da ya wuce Manuel Neuer ya tare kwallo mai kyau a karon farko a wasan na daf da karshe, bayan da aka buga masa shida.

  18. , Bayern Munich 0-1 Paris St-Germain

    Sai dai kafin lmasu duba lafiyar ɗan wasa su shigo filin, daga gefen fili dan wasan PSG, Khvicha Kvaratskhelia ya ja kwallon daga baya ya samu bugun kusurwa.

  19. , Bayern Munich 0–1 Paris Saint-Germain

    PSG sun tsira daga wani babban kuskure. Dan wasan gefen dama, Warren Zaïre-Emery ya rasa ƙwallo ga Luis Díaz, amma daga baya Michael Olise ya buga kwallon amma an tare ta.

    Sai kuma Jamal Musiala ya faɗi sakamakon rauni, inda masu duba lafiyar ƴan wasa suka shigo filin domin duba shi.

  20. , Bayern Munich 0-1 Paris St-Germain